✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shugabancin majalisa ya sake jefa APC a tsaka-mai-wuya

Ga dukan alamu batun shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa (da kunshi ta Dattawa da ta Wakilai) ya sake jefa Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan…

Ga dukan alamu batun shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa (da kunshi ta Dattawa da ta Wakilai) ya sake jefa Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan a tsaka-ma-wuya bayan da jam’iyyar ta bayyana Sanata Ahmed Lawan na APC daga Jihar Yobe a matsayin wanda take so ya shugabanci Majalisar Dattawa da kuma dan Mista Femi Abdulhamid Gbajabimila na APC daga Legas a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai.

Wannan zubi ne jam’iyyar ta yi a shekarar 2015, kafin wadansu ’ya’yan jam’iyyar su yi mata tutsu su hada kai da ’ya’yan Jam’iyyar PDP inda suka zabi shugabannin da ba su jam’iyyar take so ba.

A wancan lokaci akwai zargin Jam’iyyar APC ta yi rabon mukaman ne ba tare da tsoma ’ya’yan Sabuwar PDP ba, inda masu wannan ra’ayi suka yi misali da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ne daga tsohuwar CPC, sai Mataimakinsa Yemi Osinbajo daga ACN, yayin da Sanata Ahmed Lawan ya fito daga tsohuwar ANPP, shi kuma Gbajabimila ya fito daga ACN.

Ana zargin wannan ne ya sanya ’ya’yan sabuwar PDP a wancan lokaci suka hada kai da tsofaffin abokansu a PDP suka yi musu tayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, inda suka wargaza shirin jam’iyyarsu ta APC.

A makon jiya sai ga shi Jam’iyyar APC ta sake bayyana Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawan, Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda take so ya zama Shugaban Majalisar, sannan a tsakiyar wannan mako ta sake fito da dalla-dallar jerin wadanda take so su kasance a kan muhimman kujerun shugabancin majalisar.

Tura shugabancin Majalisar Dattawa ga yankin Arewa maso Gabas tare da bayyana Sanata Lawan a matsayin dan takarar da uwar Jam’iyyar APC ta fi so ne ya sake jawo cece-kuce inda hakan yake barazana ga jam’iyyar bayan da wadansu fitattun ’ya’yanta suka fara botsare mata kan wannan mataki.

Daya daga cikin masu adawa da matsayar ta APC shi ne Sanata Muhammed Ali Ndume tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, wanda tuni har ya kaddamar da kudirori tara da yake son cimmawa idan ya samu nasarar hayewa kujerar. Sannan akwai wadanda ake zargin suna kamfe ta karkashin kasa don neman wannan kujera ciki har da Sanata Danjuma Goje daga Jihar Gombe da Sanata Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa.

Ana zargin wadansu daga cikin sanatoci masu fada-a-ji da aka zaba a karkashin Jam’iyyar APC musamman tsofaffin gwamnoni, suna daga cikin masu yakar wannan matsayi na APC, inda suka zargin cewa wani yunkuri ne na mayar da majalisar ’yar amshin Shata don haka sun tashi haikan don ganin hakan ba ta auku ba.

A jerin rabon mukaman Majalisar Dattawa da Jam’iyyar APC ta yi tamika wa yankin Kudu maso Kudu kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar, inda ake sa ran za a fafata a tsakanin Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar a yanzu Sanata Francis Alimikhena daga Edo ta Kudu da kuma Sanata Obie Omo-Agege daga Jihar Delta, wanda yake fama da shari’a a gaban kotu. Dukan sanatocin biyu tsofaffin hannu ne kuma tuni suka fara kamun kafa musamman a Kudu zuwa Kudu.

Baya ga Sanata Alimikhena da Sanata Omo-Agege, akwai wadansu da ake zargin suna neman kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan da suka hada da Sanata Ajayi Boroffice daga Jihar Ondo da zababben Sanata Orji Uzor Kalu daga Jihar Abiya da kuma Sanata Remi Tinubu daga Jihar Legas.

Mika kujerar Shugaban Majalisar Wakilai ga Kudu maso Yamma ma na jawo cece-kuce tare da barazana ga jam’iyyar, inda wadansu ke ganin tunda Mataimakin Shugaban Kasa ya fito ne daga Kudu maso Yamma ya kamata kujerar ta gusa ne zuwa wata shiyyar ta daban. Masu adawa da wannan mataki suna ganin tunda akwai shiyyoyi shida a kasar nan kamata ya yi a zakuda da kujerar zuwa wata shiyyar maimakon Shiyyar Kudu maso Yamma.Tuni dai Gbajamiabila ya kaddamar da takararsa a farkon wannan mako inda ake sa ran zai fuskanci mutum bakwai masu son tsayawa takarar wannan kujera da suka hada da Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa) da Mukhtar Aliyu Betara (APC, Borno) da Idris Wase (APC, Filato) da Umar Bago (APC, Neja) da Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abiya) da John Okafor (APC, Imo) da Babangida Ibrahim (APC, Katsina) da kuma Mohammed Gudaji Kazaure (APC, Jigawa).

Kuma a yayin da APC ke cikin wannan tsaka-mai-wuya, a gefe guda kuma Jam’iyyar PDP tana can ta sake kwanton bauna domin jirar bango ya tsage ta yadda za ta kutsa kai ta yi wa APC barna.

Wata majiya ta ce, tuni Jam’iyyar PDP ta sha alwashin ‘koya’ wa APC hankali a fagen dimokuradiyya wajen zaben shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa karo na tara da zarar an kammala zaben Jihar Ribas inda za ta gana da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilanta.

Majiyarmu ta ce za a yi ganawar ce don sanin alkibla da jam’iyyar za ta nufa kan yadda wakilan jam’iyyar za su gudanar da zaben shugabannin majalisar a ranar 9 ga Yuni mai zuwa.

Wata majiya ta kusa da Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta shaida wa wata kafar labarai cewa za su gana don auna yadda aka gudanar da zaben na bana. “Kuma mun san lokacin da za mu kai farmaki idan lokacin ya zo. Kyale su (APC) su yi ta surutu sai ka ce zauren Majalisar Dokoki ta Kasa Sakatariyar Jam’iyyarsu ce,” inji majiyar ta PDP da ta nemi a sakaye sunanta.

Tuni Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa jam’iyyar a wannan karo ba za ta bar maciya amana su yi mata shigar sauri kwace shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa ba.

Ya sha alwashin cewa tilas ne a fifita batun biyayya ga jam’iyya wajen yanke shawara kan wadanda za su jagoranci Majalisar Dattawa da ta Wakilai a wannan karo.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da manema labarai a wajen addu’o’in da aka shirya don taya shi murnar cika shekara 67 a Legas, inda ya ce, “Biyayya a tsakanin ’ya’yan jam’iyya shi ne ginshiki, wajibi ne mu kasance masu biyayya ga jam’iyya.”

Ya ce, “Mun dan yi sakaci a shekarar 2015. Mun bayar da dama maciya amana sun shiga jam’iyyarmu kuma sun hana Najeriya samun ci gaban da ya kamata. Kun ga sakamakon hakan, don haka ba za mu bari hakan ta sake aukuwa ba. Wajibi ne mu girmama jam’iyyarmu, kuma za mu tabbatar da an bi ka’idoji da dokokin jam’iyyarmu.”

Sanata Tinubu ya kara da cewa: “Ko dai ka kasance tare da mu ko ka biyo mu, ko kuma ka bar mu. Kana da ’yancin zabi, amma ’yancin bai ba ka dama a matsayinka na marar rinjaye ka je ka hada baki don yin kafar ungulu ka sarayar da amanar da muka ba ka ga abokan adawarmu ba, wadanda Sannan Jam’iyyar APC ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa mai barin gado Sanata Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da fara aiki a bayan fage don ganin sun kawo mata cikas game da yadda ta tsara yadda take son shugabannin majalisun biyu su fito.

Wani kalubalen da Jam’iyyar APC za ta fuskanta shi ne tsoma bakin da Kungiuar Kiristoci ta Kasa (CAN) ta yi kan batun zaben shugabannin Majalisar Dokokin ta Kasa, inda ta bukaci lallai a tabbatar daya daga cikin shugabannin majalisun biyu na Dattawa ko na Wakilai ya kasance Kirita ne.

Wannan mataki na Kungiyar CAN yana zuwa ne a daidai lokacin da ta fahimci cewa tsarin da APC ta yin a rarraba mukaman shugabancin majalisun biyu ya zabi Musulmi biyu ne don shugabanta Majalisar Dattawa da ta Wakilai, wato Sanata Ahmed Lawan da Femi Abdulhamid Gbajabiamila.

Masu lura da harkokin siyasa dai suna ganin matakin na Kungiyar CAN na iya kara raba kan ’ya’yan Jam’iyyar APC a fagen addini, duk da cewa an taba samun shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakinsa da Shugabana Kasa duka Kiristoci a baya ba tare da Musulmi sun daga jijiyar wuya ba.

Koma me zai faru akwai wadanda suke ganin Jam’iyyar tana da isasshen lokaci wajen kintsa ’ya’yanta tare da tabbatar da ba a yi mata shigar sauri irin na shekarar 2015 ba, ganin cewa akwai sauran sama da wata biyu kafin a gudanar da zaben shugabannin majalisun biyu.