Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda sojoji suka yi wa Kamfanin Daily Trust dirar mikiya

Lokacin da sojoji suka mamayi Kamfanin buga jariidun Daily Trust
Lokacin da sojoji suka mamayi Kamfanin buga jariidun Daily Trust

A ranar Lahadin da ta gabata ce sojoji dauke da bindigogi suka yi wa Kamfanin Media Trsut mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya dirar mikiya, inda suka kama wadasnu ma’aikatansa tare da kassara ayyukansa da kuma kwashe na’urorin kwamfutarsa.

Tun da farko, wadansu sojoji da jami’an tsaro cikin cikin fararen kaya ne suka je ofishin shiyya na kamfanin jaridar da ke Maiduguri da misalin karfe 4:30 na ranar Lahadin, suka gudanar da bincike kafin su yi awon gaba da Shugaban Wakilan jaridar Uthman Abubakar da kuma Ibrahim Sawab.

ADVERTISEMENT

Sannan da misalin karfe 7:30 na yammancin ranar suka kutsa cikin Babban Ofishin Kamfanin da ke Abuja, suka tattara ma’aikatansa a waje guda suka kwace wayoyinsu, suka yi binciken kwakwaf a dakin labaran jaridar, sannan suka yi awon gaba da kwamfutoci da dama da kuma wani ma’aikaci daya, wanda suka sako shi daga baya, bayan ya shafe tsawon lokaci a barikin Mogadishu.

Wannan farmaki ya kawo cikas ga ayyukan kamfanin ta fuskar tsarwa da buga jaridar da za a fitar ranar Litinin. Baya ga dirar mikiyar a ofisoshin na Maduguri da Abuja, wadansu sojoji cikin motoci bakwai sun yi wa ofishin kamfanin na Legas tsinke da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Lahadin.

ADVERTISEMENT

Lokacin da sojojin suka je ofisoshin jaridar na Maiduguri da Abuja, sun rika tambayar inda wadanda suka rubuta babban labarin jaridar ta ranar Lahadi suke don su kama su.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta tare da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun je ofisoshin jaridar ne don gayyatar ma’aikatanta da suka buga wani labari a ranar Lahadi.

Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar ta ce buga labarin ya saba da doka kuma barazana ce ga tsaron kasar nan. A cewarta matakin ya ci karo da sashe na 1 da na 2 na dokar kiyaye sirrin hukuma.

Sannan kuma labarin zai bai wa ’yan ta’adda damar sanin lokacin da sojoji za su kai musu hari, abin da kuma hadari ne ga dakarun da ke yaki da Boko Haram, in ji ta.

Sanarwar ta ce an gayyaci wadanda ke da hannu ne da kyakkyawar manufa da nufin sanar da su game da illar hakan ga tsaron kasa. A cewarta, rundunar sojin ba ta da niyyar cin mutunci ko hana ’yan jarida aikinsu kamar yadda dokar kasa ta tanada, amma ba za ta lamunci duk wata kafar labarai da za ta rika aikata wani abu na nuna goyon baya ga ’yan ta’adda ba ko kuma kokarin kawo cikas ga hukumomin tsaro a kasar nan ba.

Kamfanin Daily Trust ya bayyana farin ciki game da sako editanta na Maiduguri Uthman Abubakar a yammcin ranar Talata, bayan shafe kwana biyu a hannun sojojin.

Shugaba kuma Babban Editan Kamfanin, Malam Mannir Dan-Ali ya tabbatar da sakin Uthman Abubakar, amma ya ce har yanzu da sojojin ba su dawo da kayan aikin kamfanin da suka kwashe ba.