Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda taron KILAF 2018 ya gudana a Kano

A makon jiya ne aka gudanar da taron baje kolin fina-finai da kuma karrama ’yan fim na Afirka karo na farko.

Taron mai taken Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festibal (KILAF 2018) an gudanar da shi ne a  birnin Kano, inda ya zo da wani sabon salo na sauya fasalin yadda ake gudanar da sana’ar fim tun daga tushe.

ADVERTISEMENT

Tsawon mako guda aka shafe ana gudanar da tarurruka tare da gabatar da jawabai game da yadda sana’ar take da kuma yadda za a gudanar da ita musamman a wannan lokaci da ake samun ci gaban zamani da kuma yadda ci gaban zamani yake neman kashe harkar musamman a masa’antar Kannywood da a yanzu ake ganin ta dauki hanyar durkushewa. Don haka ne ma taron ya mayar da hankali kan lalubo hanyar da za a shawo kan matsalar da harkar take ciki a yanzu.

Manyan malamai daga jami’o’i daban-daban na kasar nan da  wasu daga waje sun gabatar da makaloli a tsawon kwanakin da aka shafe ana gudanar da taron.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabin maraba, shugaban taron Malam Abdulkareem Muhammad, ya bayyana matukar farin cikinsa bisa yadda bakin suka halarci taron, wadanda wadansunsu sun zo ne daga nisan duniya , inda ya yi fatan samun nasara game da abin da aka tattauna.

Babban Bako Mai jawabi Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed, wanda Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Kasa ya wakilta ya jinjina wa Abdulkareem Muhammad dangane da shirya taron, domin a cewarsa wani dandali ne da aka samar na nuna ilimi da kuma kasuwancin kasashen Afirka, don haka ya nuna goyon bayan Gwamnatin Tarayya saboda taron ya yi daidai da kudirinta na samar da aikin yi ga matasa, “Don haka wannan taro abin alfahari ne gare mu saboda manufar ta zo daya da ta bunkasa kasuwancin fina-finai da ake yi da harshenmu na gida.”

Mai masaukin baki Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Kasuwanci Ahmad Rabi’u cewa ya yi, taron kamar ita Gwamnatin Kano aka yi wa kasancewar jihar cibiyar kasuwanci, don haka suna goyon bayan taron domin zai bunkasa jihar da kasuwanci ta hanyar jawo masu zuba jari don gudanar da harkar fina-finai a jihar, “Wannan abin alfahari ne gare mu, kuma za mu ci gaba da ba da goyon baya don ganin an samu nasarar da ake nema,” inji shi.

Bayan ya kammala jawabinsa ne aka bude tambarin taron wanda jakadun KIlAF 2018 karkashin jagorancin Ali Nuhu da sauran manyan baki suka bude.

An ci gaba da taro a rana ta biyu wato Laraba 14 ga  Nuwamba, inda aka fara taron sanin makamar aiki kuma aka kasa taron gida biyu da karamin aji da babba, kuma an gudanar da  taron ne a otel din Babale Suites da ke bayan filin Sukuwar Dawaki a Unguwar Nasarawa, Kano.

Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya, (National Open Unibersity of Nigeria), Farfesa Abdalla Uba Adamu ne ya fara gabatar da jawabi a kan harkar fim da yadda take tun daga tushe.

Malamin ya kawo asalin samuwar harkar fina-finan Hausa da fim din da aka yi na farko har zuwa lokacin da aka rada wa masa’antar sunan Kannywood. Sannan ya yi bayani game da ci gaban da fina-finan Hausa suka samu da bunkasarsu zuwa lokacin da masu harkar suka kashe ta.

Farfesa Abdallah Uba ya nuna mahimmancin mayar da kasuwancin fim ta kafar Intanet inda ya ce, “Da irin wannan taro da ake nazartar juna kuma ana kalubalantar juna a kan hanyoyin da za a bi a farfado da sana’ar. Ba kuma farfadowa kawai a ce kasuwa ta dawo ba, a’a, za a farfado da harkar ce yadda duniya za a san me muke yi, kuma idan ba mu ci gaba da irin wannan taron ba, to haka za mu zauna kullum ana cewa Kasuwar Kofar Wambai, amma yanzu an wuce wannan matsayin abu ne na duniya tunda yake yanzu akwai hanyar da za mu tallata fina-finanmu a duniya, ba wai sai Kofar Wambai ba. Akwai sabuwar hanya ta Intanet da za mu tallata fim dinmu mutane su ga abin da muke yi abin da muke bukata shi ne a hada karfi da karfe a samar da labarai masu inganci da za su nuna rayuwar Bahaushe da yadda yake, ba wai a nuna mutane a wani yanayi da ba haka yake ba. Wannan shi ne babban kalubalen da muke fuskanta a wannan taro.”

Ya kara da cewa “A yanzu haka jami’ar da yake shugabanta za ta fara yin kwasa–kwasai a kan sha’anin fim, inda jami’a ta ba mu damar karantar da abin da ya shafi harkar fim, to a wannan hanyar da muka gani za mu gyara sana’ar, don haka a yanzu idan dan fim zai shigo muna maraba da shi kuma wadanda muka fi nema su shigo su ne masu matakin kammala sakandare da suka fara daga Babbar Sakandare 2 za su je su sayi JAMB. To ka ga idan suka kammala za su je su yi sana’arsu. Don haka muna ganin idan muka samu wadannan dalibai nan da shekara goma za a samu wadanda za su fito da sanin hakikanin yadda ake yin fim. Kuma su ne mutanen da za su yi fim da duniya za ta gani ta san mun iya fim. Don haka mutane su farka domin akwai bambancin abin da ilimi ne yake bayar da shi da kuma wanda kwarewarka ta ba ka. Don haka akwai bambancin kwarewa da kuma kasuwanci, kuma da yawa daga cikin ’yan fim dinmu suna kallon fim ne a matsayin kasuwanci, in kasuwa ta ba da dama a yi in ba ta ba da dama ba a bari,” inji shi.

Ya kara da cewa, “To mu ba haka muke so a kalli fim ba, so muke a kalle shi a matsayin sana’ar da take da ka’idoji, don ba ka isa kawai ka ce kai likita ne ba tare da an koya maka ba, to don me za ka ce kai dan fim ne ba tare da an koya maka ba? Don haka muna so a bai wa fim darajarsa a yarda sana’a ce, yanzu ko malanta ma da aka raina an fito an ce sana’a ce, sai mutum yana da takardar shaidar koyarwa. To me ya sa shi fim ake yi masa kallon wulakanci kowa ya ga dama sai ya diro ya ce shi ma ya iya? Don haka a yanzu muna so ne mu mayar da fim ya zama sana’a, ya zamo ba za ka yi ba sai kana da kwarewa.”

A ranar 16 ga wata an gudanar da taron cin abinci tare da gabatar da jerin sunayen fina-finai 8 da suka tsallake matakin tantancewa cikin 25 da aka shigar.

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci taron inda ya samu wakilcin Jarman Kano Farfesa Isa Hashim.

A cikin jawabin da ya gabatar, ya ce Masarautar Kano tana maraba da irin wannan taro da aka shirya domin samar da fim da ake yin amfani da harshen uwa, “Domin idan muka duba yadda al’adunmu suke shiga wani yanayi da kuma barazana ta bacewarsu lallai ana bukatar a samar da hanyar da za a farfado da su saboda yara da suke tasowa da kuma masu zuwa nan gaba, don haka ya zama dole mu tashi mu yaki bakin al’adun da suke zuwa mana musamman ta fina-finan Turai da na Indiya,” inji shi.

A ranar 17 ga Nuwamba aka kammala taron da raba kyautuka ga jarumai da kuma fina-finan da suka ci gasar ta KILAF AWARD.

A jawabin Malam Abdulkareem Muhammad ya kalubalanci ’yan fim a kan rashin halartarsu wajen taron kasancewar taron nasu ne amma sai ga shi ba su ba abin muhimmanci ba, domin in ban da Ali Nuhu da Abba Almustapha da  Baballe Hayatu da Hamisu Lamido Iyantama babu dan fm din da ya halarta.

Ya yi kira gare su da su daina boye kansu ga duk wani abu na ilimi da aka kawo musu su rika fitowa ana yi da su, ta haka ne za su karu da ilimin da harkar take bukata, sai ya yi fatan nan gaba za su zo a yi da su tun da abin nasu ne.

Shi kuwa alkalin da ya jagoranci fitar da fina-finan da suka yi nasara Malam Sule Bello cewa ya yi, fitar da sakamakon wannan gasar ba karamin aiki ba ne saboda an shirya shigar da fina-finan ne ta Intanet don haka wadansu ba su gane ba. Shi ya sa shigar ta yi musu wahala. “Mu kanmu mun samu matsala wajen sauke fina-finan domin akwai wanda ba mu iya sauke shi ba sai barinsa muka yi. Kuma da yake mun samu kurewar lokaci ina ganin hakan ce ya sa ba mu samu fina-finai daga sauran kasashen Afirka ba. Hakan ya sa dukan fina-finan da muka duba na Hausa ne, sai guda daya na harshen Ibo da muka samu. Sannan kuma a tsarin gasar fina-finai kashi 3 ne za a shigar, wato mai dogon zango da mai gajeren zango, sai kuma na tarihi. Amma dai har muka kammala na tarihi guda daya muka samu don haka shi kadai ba zai shiga gasa ba, wannan kuma ina ganin saboda karancin fina-finan da muke da su a kan tarihi ne ya sa hakan ta faru,” inji shi.

Fim din Juyin Sarauta ya fi samun maki domin shi ne ya lashe kyautar Gwarzon Fim, sannan shi ne ya lashe kyautar mafi kyawun labari. Haka nan mai ba da umarninsa ya zamo Gwarzon Darakta, kuma shi ne ya samu wanda ya lashe Gwarzon Mai tsara waje.

Gwarzon jarumi na gasar KILAF Award 2018 shi ne Sadik Sani Sadik, da fim din Ruwan Dare, sai mai tallafa wa Gwarzon Jarumi shi ne Omoh Inaji da fim din Amonye Bu Owye,  (Fim din Ibo) sai fim din Yeelow da ya yi nasara da mafi tsara kwalliya.