Da Dumi Dumi

Yadda tarzoma ta varke a Tsafe kan kashe-kashen ’yan bindiga

Wasu daga cikin motocin da masu zanga-zanga suka qona

Aqalla mutum biyar ne suka rasu bayan wata mummunar zanga-zanga da ta varke a garin Tsafe da ke Qaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

A ’yan kwanakin nan an samu kashe-kashen da ake jinginawa ga varayin shanu da masu garkuwa da mutane, inda  aka yi rasa rayukan aqalla mutum 40 da kuma raba mutum 1,700 da muhallansu, kamar yadda Shugaban Qaramar Hukumar Tsafe Alhaji Aliyu Abubakar ya tabbatar.

Tuni da mutanen qauyukan Asaula da Kwadawa da Dogon Kawo da Mandaba da  Yanza da Kulutu da Sakkya da na Fegin Dakai, dukansu da ke gabashin Tsafe suka bar gidajensu, suka nemi mafaka a wata makaranta da ke garin Tsafe.

Ruhotanni sun ce wani babban xan ta’adda da ya yi fice wajen satar shanu da ake kira Ado Alero ne ya addabi al’umomin Qaramar Hukumar Tsafen da tu’annati.

An ce jami’an tsaro ne suka yi nasarar qwato shanu aqalla 480 daga hannunsa. Kuma bayanai sun nuna cewa ya sato shanun ne daga wasu yankuna na jihar da kuma maqwabciyar Jihar Kaduna.

ADVERTISEMENT

Majiyarmu ta ce Ado Alero ya fusata da qwace shanun inda kuma ya sha alwashin tayar da duk qauyukan da ke gabashin Qaramar Hukumar Tsafe ta hanyar kai hare-haren kisan gilla da kuma satar jama’a, don karvar kuxin fansa.

Wata mai juna biyu mai suna Ra’aina wadda ta sha da qyar daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa ta yi tafiya ta kilomita fiye da ashirin a qafa tare da mijinta don shigowa garin Tsafe.

“Suna kashe mazanmu kuma suna yi wa mata fyaxe. Rayuwa ta yi mana qunci, ba mu da kwanciyar hankali a garuruwanmu yanzu,” inji ta.

Ana cikin wannan juyayi na rashin rayuka da ya ta’azzara, musamman a qaramar hukumar ce sai waxansu matasa suka shirya zanga-zanga, don sun nuna fushinsu da abin da ke faruwa a jihar.

Zanga-zangar dai an ce ta lumana ce amma daga bisani ta rikixe ta koma tarzoma, inda matasan suka tasar wa Sakatariyar Qaramar Hukumar Tsafe; suka kuma banka mata wuta. Masu zanga-zangar sun kuma qona babura da motoci na gwamnati da kuma na sauran jama’a, waxanda sukan je su ajiye abubawan hawansu a sakatariyar.

Wani mazaunin garin Tsafe mai suna Hamisu Xanladi ya shaida wa Aminiya cewa motoci fiye da goma da babura da dama ne aka qona. Mutum biyar aka tabbatar sun mutu kuma waxansu aqalla shida na karvar magani a asibitocin jihar. Kuma jama’a na ci gaba da alhinin abin da ya faru.

To sai dai Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara ta bakin Kakakinta, SP Muhammad Shehu ta ce babu wanda ya rasa ransa a zanga-zangar kuma sun kama mutum 23 da ake zargin suna da hannu a zanga-zangar. Ya yi gargaxin cewa duk wanda aka kama yana da hannu a al’amarin zai fuskanci hukunci. Yana mai cewa an qara yawan jami’an tsaro a qaramar hukumar don tabbatar da bin doka da oda.

Shugaban Qaramar Hukumar Tsafe, ya musanta raxe-raxin da ake yi na cewa zanga-zangar tana da alaqa da ’yan gudun hijirar da ’yan bindigar suka tarwartsa a yankin. Ya ce ’yan siyasa ne ke son cimma burinsu ta wata hanyar daban. “Yanzu dai hankali ya kwanta kuma shaguna sun buxe, ana kuma ci gaba da gudanar da al’amuran yau da kullum,” inji wani mazaunin garin na Tsafe.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa musabbabin bore da qone-qonen, ya biyo bayan samu rahoton cewa cinna wuta ga qauyen Asaula da ke Qaramar Hukumar Tsafe da ’yan bindiga suka yi ne, inda yi qone, kuma suka kashe sarkin garin a makon jiya.

Majiyar ta ce sama da mutum dubu biyu ne suka shiga garin Tsafe a matsayin ’yan gudun hijira, cikinsu har da mata da yara.

Aminiya ta zanta da wani magidanci da ke zaune a garin Tsafe wanda ya nemi a sakaya sunansa, inda ya ce: “A ranar Lahadin da ta gabata Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara ya yi magana da manema labarai cewa Zamfara tana zaune lafiya ba wani tashin hankali. Matasan Tsafe abin ya vata masu rai, ganin ga ’yan gudun hijira nan tare da su sun bar garnnsu saboda matsalar tsaro kuma wani ya ce ana zaune lafiya. Kan haka suka haxa kansu da ’yan sa-kai da ’yan gudun hijira, cewa su fito su nuna maganar Kwamishina ba gaskiya ba ce. Don sun san an qone garinsu da kashe sarkinsu don gwamnati ta xauki mataki suna cikin halin rashin tabbas.”

Ya ci gaba da cewa “Mutanen gari sun amince a yi zanga-zangar lumana. Aka fito har zuwa qarfe 12 na rana, an datse babbar hanyar da ta ratsa garin mai haxa wasu jihohin Arewa. Qarfe biyu na rana abin ya canja, matasan suka tafi Sakatariyar Qaramar Hukumar Tsafe suka kunna wuta, sun qone motoci da babura na gwamnati. Ofishin  Sibil Difens kuma da ke kusa da sakatariyar sun qone musu buhunan shinkafa da ke wurin. Sun sace kwamfutocin hannu guda 2. Duk abin da suka varnatar kayan gwamnati ne, ba su tava kayan mutanen gari da matafiya ba.”

Ya ce shi bai san waxanda suka canja zanga-zangar zuwa ta tashin hankali ba. “Amma a ganina, mutane sun hasala ne kan riqon sakainar kashin da gwamnati ke yi ga sha’anin tsaro a Jihar Zamfara. Ba maganar siyasa a ciki kamar yadda waxansu ke gani kuma suke faxi, mutum 22 da ’yan sanda suka kama da zargin suna da hannu a lamarin mutanen gari ba su gamsu da kamen ba. Sun qi tafiya karvo su ne don gudun kada a ce da su amma dai mutane suna yi musu addu’ar kuvuta,” inji shi.

“A zanga-zangar, an kashe mutum 3, cikinsu har da mace xaya. Hakan ya faru ne a musayar wuta tsakanin ’yan sanda da ’yan sa-kai. Tsafe ta gabas ba zaman lafiya, yanzu haka qanwata na gida an kashe mijinta a qauyen Hangen-da-Kai, muna buqatar kulawar gwamnati a yankinmu,” inji shi

Sai dai Shugaban Qaramar Hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu Abubakar M.C ya ce zanga-zangar tana da nasaba da siyasa, kuma an yi ta ce don shafa wa gwamnati kashin kaji.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya