✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tirka-tirkar siyasa ta turnuke a Jihar Legas a makon jiya

Wani abu da ke daukar hankalin al’umma a Jihar Legas da kuma kasar nan shi ne halin tsaka mai wuya da Gwamnan Jihar, Akinwumi Ambode…

Wani abu da ke daukar hankalin al’umma a Jihar Legas da kuma kasar nan shi ne halin tsaka mai wuya da Gwamnan Jihar, Akinwumi Ambode ya samu kansa a ciki bayan sa-in-sar da ta barke a tsakaninsa da ubangidansa kuma Uban Jam’iyyar APC, Ahmad Bola Tinubu, lamarin da ya sa kashi 98 cikin 100 na shugabannin kananan hukumomi da ’yan majalisar jihar suka juya wa Gwamnan baya. Wadannan jami’ai sun nuna goyon bayansu ga dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC, Jide Sanwo-Olu.

Haka Mataimakiyar Gwamnan,  ta nuna goyon bayanta ne ga Jide Sanwo-Olu.

A nasa bangaren Gwamna Ambode ya ki janyewa daga  takarar duk da bukatar haka daga Bola Tinubu. Lamarin da wadansu masu fashin baki suke ganin ya yi daidai kuma hakan ne mulkin dimokuradiyya kamar yadda Malam Musa Yahaya Muhammad ya shaida wa Aminiya. Ya ce dagewar da Gwamna Ambode ya yi na fitowa a kara da shi a zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC, shi ne cikar tsarin mulkin dimokuradiyya.

Ya ce siyasar ubangida a jihohin Kudu maso Yamma ta mayar da tsarin jam’iyyun sun zamo tamkar mallakar mutum guda. “Wannan tsarin siyasar ba a yin irinta a Arewa. Wannan shi zai nuna maka cewa a siyasance a Arewa an fi samun ’yanci domin ba a bar jam’iyyun a hannun wadansu daidaikun mutane ba, kodayake jama’ar Legas ba sa farin ciki da salon mulkin Gwamnan Legas Akinwumi Ambode. Hakan ne ya sa rashin goyon bayan da Bola Tinubu ya nuna mana ya yi tasiri a zukatan al’ummar jihar,” inji shi.

Sai dai a wata hira da Gwamna Ambode ya yi kai-tsaye a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce shi ne dan takarar da zai iya kawo wa Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osibanjo yawan kuri’un da suka kamata.

Kuma ya ce shi ke da gogewa da kwarewa kuma muddin aka samu akasi, jam’iyyar adawa za ta iya karbe madafun iko a Jihar Legas. Gwamnan ya mai da hankali wajen sukar abokin karawarsa Jide Sanwo-Olu, inda ya ce an taba  tsare shi a gidan yarin Amurka sakamakon amfani da jabun Dala.

Haka ya ce abokin karawar tasa ya taba samun tabin hankali har aka kwantar da shi a babban asibitin Bagada da ke jihar. Wannan suka da Ambode ya yi wa Sanwo-Olu bai yi wa da dama daga jama’ar jihar dadi ba, domin hakan ba ya cikin al’adun Yarbawa na kushe mutum da wata nakasa.

Sai dai a zantawar da Ahmad Bola Tinubu ya yi da ’yan jarida, ya  ce kayar da Gwamna Ambode a zaben fid da gwani na jam’iyyar ba zai shafi kuri’un da Shugaba Buhari zai samu a Jihar Legas a zaben 2019 ba. Ya ce al’ummar jihar ne ke da damar zabar wanda suke so, kuma suka ga ya dace ya mulke su. Sai dai masu fashin baki na ganin wannan tirka-tirkar siyasar cikin gida ta Jam’iyyar APC ka iya bai wa jam’iyyar adawa ta PDP nasara a Legas.

Jam’iyyar APC dai ta riga ta gudanar da zaben fid da gwani na dan takarar Gwamna ta hanyar ’yar tinke, bayan dage zaben a karo uku, inda al’ummar jihar suka fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Talatar da ta gabata suka kada kuri’unsu. Tuni dai Mista Jide Sanwo-Olu ya lashe zaben da gagarumar rinjaye, zaben da wakilan uwar jam’iyyar suka ce ba za su lamunta ba. Sai dai labaran da suka shigo wa Aminiya sun ce tuni Gwamna Ambode ya mika wa kai bori ya hau inda ya amince da shan kaye a zaben fid da gwanin.