Da Dumi Dumi

Yadda tsofaffin gwamnoni ke talauta jihohinsu da sunan fansho

Yadda tsofaffin gwamnoni ke talauta jihohinsu da sunan fansho

Tsofaffin gwamnoni a Najeriya suna karbar biliyoyin Naira a matsayin alawus-alawus da fansho, duk da cewa yawancin jihohin ba su iya biyan tsofaffin ma’aikata nasu hakkokin, inda a jihohi da dama za ka ga tsofaffin ma’aikata suna shiga wani hali, kamar yadda binciken Aminiya ya gano.

A kwanakin baya ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bukaci Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya biya shi bashin alawus da yake bin jihar na Naira miliyan 10 da ya kamata a rika biyansa duk wata, wanda daya ne daga cikin kudaden da ya kamata a rika biyan nasa.

Lamarin ya jawo cece-kuce, wanda hakan ya sa Majalisar Dokokin Jihar ta yi sabuwar doka, inda ta dakatar da biyan tsofaffin gwamnonin jihar makudan kudaden. Binciken da Aminiya ta gudanar a jihohi ya nuna cewa a daidai lokacin da tsofaffin gwamnoni da mataimakansu har da ma shugabannin majalisu a wasu jihohin da mataimakansu suke karbar makudan kudade a matsayin fansho a duk shekara, tsofaffin ma’aikatansu kuwa kuka suke yi na rashin biyansu hakkokinsu, inda a wasu jihohin ma suke bin bashin watanni, wasu ma har na shekaru ma suke bi.

Binciken Aminiya ya gano cewa makudan kudaden nan da ake biyan tsofaffin gwamnoni ya saba wa ka’ida da dokar Hukumar Haraji da Kasafi ta Kasa (RMAFC), wadda ita ce ke da alhakin tsara kudaden albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar nan. Dokar hukumar ta tanadar da biyan wanda zai sauka daga mukamin da ya rike kashi 300 na asalin albashinsa.

Da yake karin haske kan lamarin, Kakakin Hukumar RMAFC, Christian Nwachukwu ya ce duk da cewa su ne suke tsara albashi da alawus-alawsu na gwamnonin, ba su da damar yin hukunci kan fanshonsu. Sannan ya kara da cewa bai da masaniya a kan wata doka da ta tanadar da a rika biyan tsofaffin gwamnonin makudan kudade a matsayin fansho.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa a wasu jihohin babu irin wannan dokar ta biyan makudan kudade a matsayin fansho, wasu jihohin da Aminiya ta bincika ta gano cewa ana wuce gona da iri wajen biyan tsofaffin gwamnonin da mataimakansu.

Sai dai kuma a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda kafar labarai ta Premium Times ta ruwaito, Babbar Kotun Jihar Legas ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kwato kudaden da aka biya tsofaffin gwamnonin suka karba a matsayin fansho, alhali a yanzu suna kan mukaman Minista ko Sanata, sannan ta bukaci Ministan Shari’a Abubakar Malami da ya kalubalanci yadda jihohi ke biyan tsofaffin gwamnonin fansho na makudan kudade.

Mai shara’a Oluremi Oguntoyinbo ya yanke wannan hukuncin ne bayan da kungiyar SERAP ta shigar da kara mai lamba FHC/L/CS/1497/2018.

Jihar Legas:

A Jihar Legas dokar da aka yi ta kudin fansho a shekarar 2007 ta ba da damar ginawa tsoffin gwamnoni gida a ko’ina suke so a jihar da Birnin Tarayya Abuja, kamar yadda sashi na biyu na dokar ya zayyana.

Kana dokar ta ba da damar ba da sabbin motoci guda shida duk bayan shekara uku da kuma kashi dari na albashin gwamna mai ci kwatankwacin Naira miliyan 7 da dubu dari 7 a shekara, wato Naira dubu dari 7 da 58 a wata.

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.

Share