✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Tsunami ta kashe mutum 1,500 a Indonusiya

Har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da jimami da kokarin ceto wadanda suka tsira da rayukansu a girgizar kasa ambaliya da ake kira Tsunami…

Har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da jimami da kokarin ceto wadanda suka tsira da rayukansu a girgizar kasa ambaliya da ake kira Tsunami inda kimanin mutum 1,500 suka rasu a Indonusiya.

Kakakin Hukumar Kula da Annoba ta Kasar, Sutopo Purwo Nugrodo ya ce wadanda suka rasu sun haura mutum 1,400, kuma dubban mutane sun samu rauni, sannan mutane sama da dubu 70 sun rasa muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna takaicinta bisa yadda ake jinkirin kai kayan jinkai da suka hada da abinci da ruwan sha da magani a wasu bangarorin kasar.

Kuma akwai rahoton cewa aikin ceto yana samun tsaiko saboda rashin kayan aiki da  yadda girgizar kasar ta yi barna.

A cewar Ofishin Aikin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutum dubu 200, ne suke bukatar tallafin gaggawa, kuma daga cikinsu akwai dubbai da kananan yara, kuma akalla gidaje dubu 66 ne suka lalace a girgizar kasar ta kai karfin digo 7.5.

Aikin ceto da agaji na tafiya yadda ya kamata- Shugaban Kasar

A jawabin, Shugaban Indonusiya, Joko Widodo ya ce aikin ceto wadanda suka makale da kuma taimakon wadanda suke bukatar taimakon gaggawa yana tafiya cikin tsari.

Shugaba Widodo ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ta biyu wurin da aka yi girgizar kasar, inda ya ce gwamnatinsa na yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta tabbatar da dawo da zirga-ziga a yankin tare da habbaka tattalin arzikin yankin ta hanyar sake gina ababen more rayuwa da suka lalace.

“Abin da ya kamata mu fara yi shi ne mu ceto tare da kwashe mutanen da suka fada cikin wannan bala’i tare da ba su tallafin gaggawa. Daga nan kuma sai mu fara gyara da sake gina yankin,” inji shi lokacin da yake zantawa da wakilin Al Jazeera, Andrew Thomas a garin Palu.

Muna bukatar taimako- Wadanda suka tsira

Wadanda suka tsira a yankin Donggala, yankin da ke da mutum kusan dubu 300, a Arewacin Palu sun ce suna bukatar tallafin abinci.

Wani mai shagon sayar da abinci a Donggala mai suna Johnny Lim ya shaida wa Reuters cewa yana rayuwa ne da kwakwa domin rashin abinci.

“Garin ya zama kufai. Komai ya lalace. Muna cikin matsananciyar wahala. Babu ruwa ba abinci,” inji Lim.

A wani yankin na Donggala, wani wanda ya tsira daga bala’in mai suna Ahmad Derajat ya ce suna tsintar abinci ne a duk inda suke tunanin za su ga abin da za su iya sakawa a bakin salati. Ya ce, “Yanzu haka muna rayuwa da duk abin da muka samu daga gonaki, kuma idan mun samu ne sai mu raba a tsakaninmu daga dankali da ayaba da sauransu.Gaskiya akwai sakaci. Me ya sa ba za su kawo mana tallafi ta jirgin sama ba?”

Wata mai aikin ceto, Lian Gogali ya ce ya kamata a kara kaimi wajen taimakon mutanen, “Duk mutanen yankin suna cikin matsananciyar wahala da yunwa. Kowa na bukatar taimakon abinci. Babu ruwa babu abinci da sauransu. Gwamnati ba ta yi kokari ba yadda ya kamata,” inji ta kamar yadda ta sanar da Reuters inda ta kara da cewa tallafin ya yi kadan, domin a babur kawai take zagayawa.