Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda Wadume ya mallaki miliyoyin Naira cikin shekara uku ba da wata sana’a ba

Hamisu Bala Wadume
Hamisu Bala Wadume

Alhaji Hamisu Bala Wadume wanda a ’yan kwanakin nan labarinsa ya mamaye kakafen watsa labarai na gida da waje. Kafin kashe ’yan sanda uku da farin hula daya da ake zargin sojoji da yi a ranar 6 ga Agusta, jama’ar garin Ibbi ne kawai suka san labarinsa.

Shi dai Hamisu Wadume wanda shekarunsa ba su wuce 31 ba, kafin shekarar 2015 ba ya da dukiyar komai kamar yadda wata majiya ta shaida wa Aminiya. Majiyar ta ce a aji biyu na  Babbar Sakandaren Je-ka-Ka-Dawo da ke garin Ibbi, ya bar makaranta ya shiga bangar siyasa a Jam’iyyar PDP.

ADVERTISEMENT

Daga nan ne kwatsam sai ga shi ya bayyana a wani tsari wanda ya bullo a garin Ibbi, da ake zargin ya yi kama da na kungiyar asiri, wannan lamari da ya bayyana ya kasance matasa a garin Ibbi sun shige shi sosai. A daidai wannan lokaci an kashe mutane musamman yara kanana masu yawa a garin Ibbi ta hanyar yanke sassan jikin, inda ake zargin ’yan kungiyar asiri ne ke aikatawa.

Amma gab da zaben bana, sai Hamisu Wadume ya bar Jam’iyyar PDP, ya koma Jam’iyyar APC, inda ya taka muhimmiyyar rawa ta hanyar bayar da gudunmawar kudi ga wadansu ’yan takara a jam’iyyar, inji majiyar.

ADVERTISEMENT

Maiyarmu ta ce a shekarar 2016, Hasimu Bala Wadume ya  fara bayyana da kudi kafin ka ce haka ya zama miloniya.

Sunan Wadume, kalmar Ingilishi ce, ta “What Do You Mean?” Wadda sannu a hankali aka canja ta  ta koma Wadume saboda yana yawan ambatar haka a lokacin da yake makarantar sankandare.

Kamar yadda wakilinmu ya jiyo a garin Ibbi, kudin da Wadume ya samu daga shekarar 2016 zuwa yanzu ya wuce hankalin kowa a garin, koda kuwa ta hanyar sace mutane yake samunsu kamar yadda ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya yi zargi.

An ce Hamisu Wadume daga samun kudinsa zuwa yanzu, ya raba kyautar motoci da babura sama da 200. Bayan haka ya bayar da kyautar kudi sama da Naira miliyan 100 ga mutane a ciki da wajen garin Ibbi.

Majiyarmu ta ce ya kuma mallaki gidaje sama da 30 a ciki da wajen garin Ibbi, inda ta ce Wadume yana da gidaje na kasaita guda uku, wadanda suke garin Gombe da Kano da Lafiya a Jihar Nasarawa.

Wata majiya a garin Ibbi ta shaida wa wakilinmu cewa Wadume ya mallaki motocin haya kanana da manya tare da babura sun fi 30. Kuma majiyar ta ce gidajensa uku da suke a garuruwan Gombe da Kano da Lafiya kowanne daya kudinsa ya kai Naira miliyan 70.

Majiyar ta ce ana zargin yana da jirgin ruwa mai daukar mutane da motoci, wanda ke jigila a Kogin Binuwai da ke garin Ibbi, wanda ake zargin cewa da jirgin aka tsere da shi bayan sojoji sun kashe ’yan sandan da suka kama shi.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ta hanyar Sarkin Kudu ne Wadume ya bi, bayan an yi masa fito daga Kogin Ibbi, ya bi hanyar Filato, inda har yanzu ’yan sanda ke farautarsa.

Saboda yadda yake bayar da kyauta kusan kowa nasa ne a garin Ibbi, ma’aikata da jami’an tsoro kowa na cin garabasar kyautarsa, wanda ya zama ba wanda ya isa ya taba shi.

Wani mazaunin garin Ibbi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa Aminiya  cewa Wadume yakan sayi manyan kifaye ya sa a mota ya kai wa manyan ’yan siyasa da jami’an tsaro a wurare daban-daban a kasar nan.

Majiyar ta ce a lokacin da aka sace wani hafsan soja a tsakanin hanyar Wukari zuwa Ibbi, Wadume ya bayar da Naira miliyan daya, wanda da su ne aka cika aka biya kudin fansa, aka fid da sojan a hannun masu garkuwa da mutane.

“Kuma duk lokacin da ya je Abuja, a gidan wani dan Majalisar Tarraya yake kwana. Yana tare da manyan ’yan siyasa wadanda suke a cikin jami’yyun PDP da APC,” inji majiyar.

Bayyanan da wakilinmu ya samu a garin Ibbi sun hada da cewa Wadume kullum a kan tafiye-tafiye yake kuma ba ya ajiye kudi a banki, sa’annan duk abin da ya saya komai tsadarsa a cikin gida zai shiga ya dauko kudi ya biya.

Majiyar ta cewa lamarin Wadume kan irin facakar da yake yi da kudi ya sa wadansu daga cikin jama’ar garin suka nuna rashin yarda da hanyar da ya bi ya samu kudin. Wani mai suna Musa Ibbi ya ce kafin Wadume ya samu kudi, ba wata sana’a da aka san shi da ita kuma bai gaji kudi a wajen iyayensa ba.

Wadume wanda dan kabilar Wurbo ne ta uba da uwa, wadda kabilace da ke da alaka da kabilar Jukun, iyayensa masunta ne kuma gidansu babban gida ne a garin Ibbi amma halinsa ya bambanta da na ’yan uwansa. Ya ce amma saboda halin talauci da ake ciki, jama’a sun kasance suna tururuwa zuwa wajensa don neman taimako. Shi kuma duk wanda ya je wajensa da bukatar kudi zai ba shi.

Wata majiya ta kara da ce bayan kyautar kudi da ababen hawa da bai wa ’yan makaranta taimakon kudin karatu, Wadume ya gina wa abokansa gidaje masu yawan gaske a garin Ibbi.

Wani dan garin na Ibbi mai suna Danmadugu, ya bayyana wa wakilin Aminiya cewa duk inda ake bikin aure ko suna, Wadume ne ake bukatar zuwansa. Ya ce a wurin biki yakan yi kyautar sama da Naira miliyan daya.

Ya kara da cewa akwai lokacin da wadansu ’yan bindiga suka mamaye gidansa da dare suka yi ta harba bindiga amma kafin ka ce haka jama’ar gari da ’yan sanda da sojoji sun kawo masa dauki, wanda hakan ya sa ’yan bindigar suka arce.

Wakilinmu ya fahimci cewa akwai lokacin da Wadume ya samu rashin jituwa da wani matashi mai suna Umar a garin Ibbi, wanda shi ma ake zargin yana neman gasa da Wadume ta ita wannan hanya da ake kira da ‘Ya Bayyana,’ wato ya sami kudi kwatankwacin na shi Wadume.

Rashin jituwar, kamar yadda wani mazaunin garin Ibbi ya shaida wa wakilinmu, ta sa an kai kararsu a hedkwatar Rundumar ’Yan sandan Jihar Taraba da ke Jalingo.

Kuma daya daga cikin wadanda sojoji suka kashe a ranar 6 ga Agusta lokacin da aka kama Wadume mai suna Usman Dan’azumi, wanda ake yi wa lakabi da  Kwalba kuma farin hula da ke aikin beli, dan asalin garin Ibbi, shi ne ya yi belin  Wadume daga hannun ’yan sandan.

Ya ce daga bisani ne aka rubuta takadar kara zuwa ofishin Sufeto Janar, wanda ya yi sanadiyyar yunkurin kama Wadume.

Aminiya ta gano cewa yanzu haka an kama sojoji biyar da ’yan sanda biyu dangane da kisan ’yan sanda uku da farin hula daya.

Kamar yadda wakilinmu ya jiyo, ’yan sandan biyu da suke aiki a ofishin ’yan sandan garin Ibbi, an kama su ne saboda zargin cewa sun tsegunta wa Wadume cewa ana shirin kama shi.

Kuma sama da matasa 60 sun gudu  daga garin Ibbi gudun kada a kama su. Wadanda suka arce, an ce su ne suke cin gajiyar garabasar dukiyar da Wadume ya raba, wadansu kuma su ne suke tuka motoci da baburansa. Bayan haka an kama wadansu daga cikin motocinsa tare da sa wa wasu daga cikin gidajensa kwado a garin  Ibbi, wanda ’yan sanda suka yi a karkashin jagorancin Mataiamkin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari da ke jagorantar yaki da garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka.

Wata majiya ta ce Wadume ya biya wa mutum 10 kujerar Hajji a bana, saannan kuma ya tura matansa biyu zuwa aikin Hajjin.

Majiyar ta ce wadansu mutanen garin Ibbi sun koka game da rashin Wadume a lokacin Babbar Sallah, inda suka ce sun rasa kyautar raguna da kudade kamar yadda ya saba ba su a lokuta irin