✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al’ummar Hausawa

A da can Hausawa sukan koya wa ’ya’yansu wakokin fasaha da suka kunshi tarbiyya da jarumta da dogaro da kai da kyautata zumunci da girmama na…

A da can Hausawa sukan koya wa ’ya’yansu wakokin fasaha da suka kunshi tarbiyya da jarumta da dogaro da kai da kyautata zumunci da girmama na gaba bin miji da zaman lafiya da sauransu. Malam Yahaya, shahararren marubucin adabi wanda ya rubuta mukala da ta shafi maudu’in da za mu yi bayani a kai ya yi gamsashen bayanai a kai.

Bahaushe na da falsafar rayuwa wadda yake son ya ga rayuwar al’ummarsa na gudana a kanta. Daga cikin muhimman abubuwan da Bahaushe ke son ya ga al’ummarsa ta dore a kai, sun hada da kyakkyawar tarbiyya da yin gargadi ga wanda ba ya da su da tausayi da jinkai da rikon amana da fadakarwa da koyar da darussa na ilimi da gurace-guracen rayuwa (irin su soyayya da aure da haihuwa) da jaruntaka da shugabanci. Wadannan abubuwa Bahaushe na koyar da su daidai bukata ga yara maza da mata. Misali, ba a cika samun koyar da jaruntaka da shugabanci a cikin wakokin yara mata ba, haka ma babu koyar da raino da gudanar da aikin gida a cikin wakokin yara maza. Ana koyar da kowane jinsi ne daidai da rawar da ake son a ga ya taka a lokacin da ya cika mutum. Ga yadda koyar da wadannan abubuwa ke zuwa a cikin wakokin yara:

Ladabi da biyayya

Amshi  “Ayye raye yaraye naye

Ayye lye yaraye

Bayarwa: Kowaz zo Kano bai ga Maikano ba

Karyak Kano ce ya kai.

Ni nit tai Kano nig ga Maikano,

Hay yab ba ni baiwa tara.

Ukku suna Kano ukku na Daura

Wasu ukku na Zariya.

’Yak karamassu an nan tana luguden,

Dutsin uwaw wanda yay yi da ni,

Da maza da mata duka.

Ban da sarakuna ban da malamai,

Bisa hankalina nike.

Ban da uwar cikina da tah haifan

Bisa hankalina nike.

Ban da uban cikina da yah haifan,

Bisa hankalina nike.”

Mai rera wannan waka tana kirari ne da nuna gadara na dangantakar da take da ita da wadansu manyan mutane kamar su Maikano. Sai dai duk wannan dangantaka da daukaka da ta samu bai sa ta raina manyan mutane irin sarakuna da malamai da iyaye ba. Komai suka yi mata za ta yi hakuri ba za su shiga cikin wadanda za ta yi ramuwar gayya gare su ba, amma wadansu ba su ba, za ta yi. Wakar na son ta nuna wa yaran Hausawa cewa, iyaye da shugabanni da malamai hakuri ake ga duk abin da suka aikata, ba za a yi ramuwar gayya gare su ba, saboda jin nauyinsu. Haka ma ga abin da wata wakar ke cewa:

Amshi: lye raye manya,

Ayye iye raye manya, Kakale.

Bayarwa da Kakale nika aure,

In babu Kakale ban aure duniya.

Uwar miji ta batan,

Na durkusa na ce Inna gafara.

Uban miji ya batan,

Na durkusa na ce Baba gafara.

Da kishiya tab batan,

Na sussuke ta na sheke,

Na dunkule ta na aika Lahira.”

Wannan ma na koyar da ladabi da biyayya ga matar aure dangane da surukanta. Su ma haka suke tamkar iyayenta, ba a ramuwar gayya gare su. Amma wanda yake daidai da kai shi ba laifi ba idan ka yi ramuwa a kan abin da ya yi maka.

Gargadi

Gargadi shi ne yin kashedi ga aikata wani abu. Yara domin gargadin su guje wa miyagun dabi’u ga misalin wannan:

Yarinya: “Dantille ho, Dantille,

In ka je gida kai zaune,

Ka ce ma Inna da Baba,

Ga ni lawai-lawai da macizai,

Ga ni lawai-lawai da kunami.

Dantille: Ina ruwan Dantille,

Da anka ce a gama mu,

Kic ce ba ki son Dantilie.

Wannan wata waka ce mai gargadi kan girman kai da raina mutane. Ta fizgo ne a cikin wata tatsuniya a inda wadansu iyaye suka nemi hada ’yarsu da baransu amma ta ki. Daga karshe sai ta fada hannun aljanu. Da yaron ya fita kiwo wata rana, shi ne take ba shi sako zuwa ga iyayenta.

Tausayi da jinkan masu rauni

Tausayi da jinkai ma’ana daya ce, wato nuna damuwa kan abin rashin jin dadi da ya samu wani. Hausawa na shirya wa yaransu waka domin su cusa musu wannan dabi’a ta tausayi da jinkan wanda ya kasa. Al’ummar da ba ta da tausayi da wuya a samu hadin kai da ci gaba mai ma’ana a cikinta, shi ya sa Hausawa ke kokarin cusa wannan dabi’a cikin zukatan yaransu. Ga misali:

Bayarwa: Dan  tsoho da gemu

Amshi: Ya tsufa

Bayarwa: A ba shi na Allah

Amshi: Ya tsufa.

Wannan wata wakar cikin tashe ce mai nuna yadda ake son a rika tausaya wa wadanda suka kasa. Yadda yara ke aiwatar da wakar a cikin tashe na kara fito da sakon sarari. Ga kuma abin da M.B. Umar ke cewa:

Yara cikin waka inai muku gargadi,

Hakkinku ne ku ji tausayin tsuntsaye.

In kun ga dan tsuntsu ku bar wasa da shi,

Ku mayar da shi sheka gidan tsuntsaye.

Wadannan baitoci ma da suka gabata suna koyar da tausayi ne. Bahaushe na son ya ga yaransa sun zamo masu tausayi ba ga mutane kurum ba har da sauran halittu.

Rikon amana

Rikon amana wani ginshiki ne na ginuwar al’umma, kuma shi ya sa Bahaushe yake kokarin tabbatar da muhimmancinsa a cikin zukatan yaransa tun suna kanana. A cikin tatsuniyar ‘Madaci’ an kawo wata waka mai nuna muhimmancin rikon amana ba ga mutum ba kawai ko ma ga itace. Ga wakar:

Yaninya: Madaci, Madaci ubana,

Gare ka anka ban ni,

Gare ka za ni tsira.

Madaci: Ishunki, ishunki diyata,

Gare ni anka bak ki,

Gare ni za ki tsira,

Mutum dari da goma,

Manzo dai kan kai gida.

Wannan wata waka ce da wata yarinya da nakuda ta kama uwarata a daji ta haife ta ta bar amanar ta ga itace/bishiyar madaci. Shi ne take rera wannan waka lokacin da ’yan samarin da sarki ya turo ke son kama ta. Tana tuna wa madaci amanar da aka bar masa, shi kuma yana ba ta tabbacin rike amanar.

Mun dauko wannan rubutu ne daga www.bakandamiya.com