Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Yadda wani tsoho ya mutu a cikin jirgin sama

Jami’an tsaro zagaye da wani jirgi bayan ya sauka

Yadda wani tsoho ya mutu a cikin jirgin sama

Wani dattijo dan shekara 72 ya rasu a cikin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa Abuja daga garin Kalaba na Jihar Kuros Riba.

Mutumin mai fama da ciwon shanyewar barin jiki na cikin jirgin kamfanin Air Peace ne a kan hanyarsa ta zuwa asibiti, rashin lafiyarsa ta yi tsanani a sararin samaniya.

Mai magana da yawun kamfanin Air Peace, Stanley Olisa ya ce da saukar jirgin Abuja, “mun yi gaggawar sanar da jami’an lafiya a filin, wadanda suka tabbatar da rasuwarsa, sannan suka tafi da gawar mamacin zuwa asibiti domin yin sauran abubuwan da suka dace.

Stanley Olisa ya ce sai da aka tabbatar cewa mara lafiyan na iya yin tafiya a jirgi kafin a dauko shi.

“Ma’aikatan lafiya a filin jirgi na Kalaba sun tanance sannan suka bayar da izinin daukarsa a jirgi; ammma kuma jikin nasa ya yi tsanani bayan tasowar jirgin.

“Air Peace riga ta yi feshin magani yadda ya kamata a jirgin kuma yanzu lamarin na hannun jami’an lafiya”, inji shi.