✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wani ya damfari Gwamna Nyako kusan Naira miliyan takwas

Wani dan damfara mai suna Tope Fagun ya gurfana a gaban Kotun Majistare da ke Unguwar Igbosere da ke Legas bisa zargin ya damfari Gwamnan…

Tope Fagun wanda ya damfari Gwamna NyakoWani dan damfara mai suna Tope Fagun ya gurfana a gaban Kotun Majistare da ke Unguwar Igbosere da ke Legas bisa zargin ya damfari Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Hammanyero Nyako Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan bakwai da dubu 800).
Tope Fagun, mai kimanin shekaru 39, ya yi amfani da sunan wani aminin Gwamna Nyako mai suna Manjo-Janar Emmanuel Abisoye ne ya yi masa karyar cewa an kwantar da shi a Asibitin kueen Elizabeth da ke birnin Landan.
’Yan sandan binciken manyan laifuffuka na kasa da kasa (INTERPOL) da suke sashin binciken manyan laifuffuka na Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya (CID) da ke Alagbon Close a Legas ne suka damke wadanda ake tuhumar.
dan damfarar, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotun tare da abokin yin damfarar tasa mai suna Rotimi Akinade, mai shekara 29, ana tuhumarsu ne da aikata laifuffuka shida, ciki har da damfara da sata.
Mai gabatar da kara a kotun DSP Raymond Odion Akhaine, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargi na farko Tope Fagun, a wani lokaci a shekarar 2011 ya buga waya ga GwamnaNyako ya ce shi ne Manjo-Janar Emmanuel Abisoye (mai ritaya), ya shaida masa cewa yana bukatar taimakon kudi domin ya biya kudin jinya a Asibitin kueen Elizabeth da ke Landan inda yake kwance kan wata cuta da bai ambata ba.
DSP Raymond ya ce rana ta baci ne ga wanda ake tuhumar lokacin da ya yi yunkurin damfarar wani babban dan Jam’iyyar PDP wanda shi ma tsohon soja ne, inda ya bayyana masa cewa shi ne Manjo-Janar Emmanuel Abisoye, kuma ya ambaci asibitin da ya ambata ga Gwamna Nyako ya ce yana bukatar ya taimaka masa ya biya kudin jinya.
Wannan jigo na PDP sai ya kira Janar Abisoye da kansa domin ya ji halin da lafiyarsa ke ciki, wanda shi kuma ya shaida masa cewa yana nan garau kuma ba a kwantar da shi a asibiti ba, kuma bai taba neman taimakon kudi daga kowa ba a duk fadin kasar nan.
DSP Raymond ya ce, Manjo-Janar Abisoye da kansa ya kai rahoto ga ’yan sanda wadanda suka kama wadanda ake zargin bayan bincike na tsawon watanni.
Tope ya san Janar Abisoye abokinsa ne sai ya kira shi ya makale murya, ya kwaikwayi maganar Janar din, ya yi kasa-kasa da muryata, kamar wanda ke kan gadon asibiti yana jinya. Ya yi sa’a gwamnan ya saki jiki da shi yana tsammanin abokin nasa ne. Da ya ga haka, sai ya ce masa ya aiko masa da Dala dubu 35 (kimanin Naira miliyan biyar) zai biya kudin jinyar da yake yi a asibitin na birnin Landan. Nan take ya bukaci asusun da zai zuba kudin. Daga baya ya kara kiransa ya nemi ya aiko mi shi da Dala dubu 15 (kimanin Naira miliyan biyu da dubu dari bakwai), shi ma nan take ya zuba. Kuma ya rika kiransa yana yi mi shi jaje akai-akai.
Sai dai ba Tope kadai ya rika cin kudin ba, akwai wani abokinsa da ya rika taimaka masa mai suna Rotimi. Asirinsu ya tonu ne lokacin da su ka samu lambar wani babban dan Jam’iyyar PDP, Tope ya manta sunansa, ya yi masa karyar da ya yi wa Gwamna Nyako, ashe ya gano cutarsa zai yi. Sai ya hada baki da ’yan sanda har aka kama shi. Amma ban da shi, akwai mutane da yawa da ya damfara, amma Gwamna Nyako shi ne babban kamun da ya taba yi a tsawon lokacin da yake damfarar jama’a. Ban san inda Rotimi yake samo lambobin manyan mutanen ba, amma duk lambar mutumin da ake so Rotimi zai samo masa. Tope yi nacin ya gaya masa inda yake samo lambobin, amma ya ki gaya mi sa.
Wandanda ake tuhumar sun ki amincewa da zargin da ake yi musu wanda ya saba wa sashi na 409 da sashi na 312 (3) da sashi na 285 da sashi na 378 na kundin manyan laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2011.
Kotun ta ba da belinsu kan Naira miliyan daya tare da mai tsaya musu wanda ya mallaki wannan kudin tare da takardun shaidar biyan haraji ga gwamnatin Jihar Legas, sannan ya tura su gidan maza na Ikoyi da ke Legas har zuwa lokacin da za su cika ka’idojin belin, ko zuwa lokacin sauraron shari’ar na gaba.