Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda wasu magunguna ke illata jiki

Wai da gaske ne yawan shan magungunan gargajiya barkatai yana iya lalata koda?

Daga Ilyasu Bebe da Saleh Joda

ADVERTISEMENT

Amsa: Watakila ku yi mamaki idan aka ce muku akwai magunguna wadanda ba na gargajiya ba ma, wato magunguna ne na Bature da kan iya yi wa jikinmu illa. Kuma magunguna sahihai ba wai kayan maye ba. Wato ba magungunan gargajiya ne kadai ke iya kawo haka ba, ko na asibitin ma idan ana shan su barkatai za su iya lalata koda. Kai ba koda kadai ba ma har da hanta. A wasu lokuta shi kansa maganin ne yake yin illar, amma a mafi yawan lokuta ba shi maganin ne a karan kansa zai yi illar ba, a’a abubuwan da aka hada magungunan da su, su ne za su yi illar. Shi ya sa ake ganin ana rubuta duk wani kayan hadi da ke cikin magungunan nasara a jikin leda ko kwalin maganin.

To irin wannan ne ba mu da shi a magungunan gargajiya; ba mu san da-me-da-me aka yi hadin ba – wato ya kamata a rika rubutawa baro-baro me da me ne a cikin maganin, kamar a wata ’yar takarda a lika a jikin ledar ko kwalbar maganin. Wato mu ma’aikatan lafiya abin yakan ba mu mamaki yadda mutanenmu suke da saurin yarda. Da wani mai magani ya kulle wani gari a leda ya bayar ya ce wannan maganin basur ne a sha shi a kunu zai kona basur, kawai sai mu yarda magani ne, duk da cewa babu inda aka zayyana a jikin maganin ko mene ne shi takamaimai. Shin garin kuka ne, ko busasshiyar kubewa, ko dakakken zogale ne, ko yadiya ce, ko kuli-kuli, ko kuma mene ne, kuma me aka kara a kai aka yi hadin? Duk ba mu sani ba, kawai muna karba ne muna sha.

ADVERTISEMENT

To, a garin aikin tace gubar irin wadannan magunguna ne wasu sassan jiki masu aikin tacewar sukan illatu. Kun san a wajen aikin tacewa da sarrafawa da fitar da magunguna daga jiki akwai wadanda koda ce kan yi (magungunan da ke fita a fitsari), akwai wadanda hanta ce kan yi (magungunan da ke fita a bayan-gida). To duk wani magani da koda ko hanta take yawan aiki a kai, ko wanda ya ba su wahala wajen tacewa, to zai iya lalata su. Wani maganin Nasara da kusan kowa ya taba sha, shi ne Panadol. Panadol sanannen magani ne a kimiyyance wajen lalata hanta idan ana shan kwayoyinsa fiye da kima, ko idan ana sha jefi-jefi na tsawon lokaci. Haka ma wani magani sha-ka-fashe, wato Steroids, wadanda wadansu ’yan mata suka mayar abinci, su ma sukan lalata koda. Shi ya sa mu a asibiti idan mutum na shan wasu magunguna na tsawon lokaci, ko na mutu-ka-raba, kamar irin na hawan jini ko na ciwon suga, duk bayan ’yan watanni sai an gwada lafiyar kodarsa da hantarsa, ta yadda da an ga alamu na wata matsala za a rage maganin ko ma a tsayar da maganin gaba daya a canja wani.

 

Na dade ban ci abinci ba, sai na zo na sha wani abu, sai in ji kirjina yana zafi. Shin wannan na cikin alamun ciwon olsa?

Daga Aminu Idris

Amsa: Eh, kwarai wannan zai iya nuni da alamu na ciwon olsa. Amma yana da kyau ka ziyarci likita domin a tabbatar ko hakan ne.

 

Akwai wani bambanci ne tsakanin kwan kaza da kwan salwa? Wanne ne ya fi amfani ga lafiya?

Daga Fatima B.

Amsa: Eh, bincike ya nuna kwan salwa ya fi yawan sinadarin protein da karancin maikon cholesterol, kuma ya fi na kaza yawan bitaman musamman na ajin B. Wadannan dalilai ne suka sa watakila ake ganin kwan salwa ya fi na kaza amfani ga lafiya.

 

Ina da cutar zamani kuma ina shan magani. To idan na je asibiti gwaji sai a ce mini babu cutar. Shi ne nake tambaya ko zan iya auren mai lafiya wanda ba shi da cutar?

Daga Maidamuwa, Sakkwato

Amsa: A’a, zai yi wahala wanda aka ce yana da ciwon zamani, wanda har aka fara ba shi magani, a kuma dawo a yi masa awo a ce babu ciwon kuma a kyale shi ya ci gaba da shan magani. Idan har babu ciwon me ya sa ake karbar magani? Ka dai kara tambayar sahihancin bayanan da suka ba ka a nan cibiyar taku ta karbar magani. Watakila suna ce maka ne ciwon na kara sauki, domin akwai wani gwaji da akan yawan yi wa masu ciwon domin a tabbatar kaifin ciwon na raguwa (wato gwajin CD4). Idan CD4 na karuwa kuma yana kyau, alama ce ta cewa magani ya karbi mutum, kuma ana cin galaba a kan ciwon, amma fa ba wai an warkar da shi baki dayansa ba. Maganar aure ma duk a nan cibiyar, inda kake karbar magani za ku zauna ku yi ta ido-da-ido da ma’aikatan lafiyar ko kuma jami’an da aka ware domin shawara wato ma’aikata masu ba da shawara.

 

Na je asibitoci da dama game da matsalar mura mai sa toshewar hancina. Yanzu na zo Abuja shi ne nake tambaya ko wane irin asibiti zan je a nan Abuja don a duba matsalar?

Daga Albada Ado

Amsa: To a Abujan sai ka nemi asibiti wanda suke da kwararren likitan hanci da makoshi da kunne, wato likitan ENT, wanda zai ji matsalar taka, ya kuma duba hancin naka ya gani ko wace irin mura ce wannan. Akwai su da dama a Abuja irin wadannan asibitoci, tun daga na gwamnati har na kudi.

 

Wai shin yawan taunar cingam yana da wata illa ne ko alfanu ga lafiya?

Daga Muhammad Gambo, Kaduna

Amsa: A’a ba wata illa in dai ba mai sukari ba ne. Wato yawan cin cingam mai sukari ne kan iya lalata hakora, saboda sukarin wani makamashi ne na kwayoyin cuta masu zama kan hakori, wadanda garin cin sukari a kan hakora suke rarake mana su. Sai dai ka san yanzu akwai cingam mai zaki amma wanda ba mai sukari ba, to wannan ba shi da matsala, za a iya tauna shi domin tsabtace baki da motsa muka-muki.