✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wutar daji mafi muni ta daidaita California a Amurka

Akalla masu kashe gobara 8,700 ne suke kokarin shawo kan wutar da ta hanyar amfani da injin kashe gobara guda 1,246 da jirgin kashe gobara…

Akalla masu kashe gobara 8,700 ne suke kokarin shawo kan wutar da ta hanyar amfani da injin kashe gobara guda 1,246 da jirgin kashe gobara 43 da motocin kashe gobara da yawa da sauran kayan aiki, inda suke ta aiki ba kama hannun yaro domin shawo kan wutar daji guda uku da suke neman daidaita Jihar California a tare.

Wannan wutar dajin ta fara ne tun a makon jiya, kuma har lokacin da muke hada wannan rahoton, wutar na ci gaba da ci duk da cewa hukomomi suna ta kokarin tsayar da wutar da masu kididdiga suka ce ita ce mafi muni bayan ta kona sama da fadin eka 225,845 na kasa da dubban gidaje.

A zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton, akalla mutum 48 aka tabbatar da mutuwarsu, sannan kuma akalla muhalli 8,800 suka daidaice a Arewacin California.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta California wato Cal Fire Operations Joshua Bischof ya bayyana wa CNN cewa suna samun nasara a kokarinsu na shawo kan wutar.

A wani bangaren kuma, jami’an tsaro sun kama akalla mutum 6 da laifin sata da wasu laifuka.

Da mutane suka tambayi Komandan Hukumar Kashe Gobarar Cal Fire Todd Durham a kan ko zuwa yaushe za su shawo kan lamarin domin su samu komawa su ga yadda wutar ta musu barna, sai ya ce, “gaskiya babu takamaiman lokaci. Amma ina tunanin zuwa wasu ’yan kwanaki masu zuwa.” Sannan ya tabbatar da cewa sun samu karin ma’aikata da za su taimaka musu.

A Kudancin California kuwa, wutar ta barnata kasa mai kusan fadin mil 150, wanda aka kiyasta ya fi Birnin Denber wanda shi ne Babban Birnin Jihar Colorado fadi da girma. Haka kuma akalla gida 434 ne suka lalace, kuma har yanzu lokacin da ake hada wannan rahoton masu kashe gobara suna ta fama da hayaki mai zafi.

..Mutane suna cikin rashin tabbas

A daidai lokacin da hukomomi suke kokarin shawo kan matsalar, su kuma mutanen yankin da abin ya shafa suna cikin rudu ne da rashin tabbas kasancewa babu ranar komawarsu gida.

Justin Bartek wanda gidansu ya kone kurmus ya bayyana wa CNN cewa wutar ta musu ba-zata, sannan kuma yana matukar tausayin mahaifinsa da ya yi ritaya da kuma jimamin rashin mahaifiyarsa.

“Mahaifina yana cikin damuwa sosai. Tokar mahaifiyata na cikin gidan. Gidan ’yar uwata ya kone kurmus. Zai yi wuya in manta da wannan bala’in cikin sauri.”

Ita ma Nichole Jolly ta shaida wa CNN cewa har ta riga ta cire tsammani da rayuwa a lokacin da wutar ta rutsa da ita tana cikin motarta, inda hayaki ya lullube ta ya hanata ganin abin gabanta, kafin daga bisani bayan ta kira mijinta ya ce mata ta fita daga motar ta arce, “na kira mijina na shaida masa halin da nake ciki, sai ya umarceni da in fito in gudu in bar motar. Shi ne ya fada min cewa ko zan mutu gara in mutu in kokarin ceton kaina,” inji Nichole inda take magana cikin hawaye.

“Na yi kokarin guduwa, amma hayakin ya yi zafi da karfi da ko gabana ban gani. Sai na fadi a kasa, hakanan dai na rarrafa zuwa kusa da wata motar masu kashe gobara. Masu kashe gobarar ne suka taimakeni suka yi kokarin daukoni, amma kuma suma suka makale. Sai daga baya ne wata babbar mota ta kawo mana dauki.”

…yadda wutar ta yi barna a takaice

  1. Wutar Camp: A Arewacin California ne aka samu wutar dajin wanda aka sa wa suna Camp Fire. An samo sunan ne daga inda wutar ta taso wato Camp Creek Road. Kuma ta fi yin barna. Ita kadai ta daidaita akalla eka 130,000 a Arewacin California din, wanda kuma ya fi Atlanta baki daya girma sannan kuma kimanin gina-gine 15,500 suna cikin tsoron abin da zai iya faruwa. A lokacin da muke hada wannan rahoto, masu kashe wuta sun shawo kan kashi 35 na wutar.
  2. Wutar Woolsey: A Kudanci kuma, an saka wa wutar suna Woolsey. Ita kuma ta barnata akalla eka 97,114 kuma muhallai kimanin 57,000 suna cikin tsoro da rashin tabbas. Zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, an shawo kan kimanin kashi 40 na wutar.
  3. Wutar Hill: Nan ma Kudancin California ne, inda nan ma wutar ta barnata akalla eka 4,531, sannan kuma an shawo kimanin kashi 90 na wutar a lokacin da muke hada rahoto.

…An ji alamar wutar kafin ta fara

Duk da cewa har yanzu ba a gano asalin abin da jawo wutar ta Camp da Woolsey ba, hukomomi a jihar suna binciken yadda wasu kamfanoni guda biyu suka kawo rahoton a kan yiwuwar afkuwar lamarin jim kadan kafin wutar ta fara.

Kimanin minti 15 kafin wutar Camp ta fara a kusa da garin Pulga, Kamfanin PG&E ya kawo bayani a kan cewa sun gano matsala a wayar wuta daga kusan nisan mill 1 daga Arewa maso Gabashin garin.

Haka ma a gundumar Bentura, inda wutar Woolsey ta fara. Kamfanin SoCal ya kawo rahoton cewa akwai matsala a na’urar rage wuta ’yan mintuna kadan kafin wutar ta fara.

…akwai sakacin malaman daji a wutar- Shugaba Trump

A jawabinsa a game da wutar dajin, Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa akwai sakacin malama dajin a wutar dajin, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Tiwita.

“Babu wani dalilin da za a rika samun irin wannan mummunar wutar dajin a Jihar California sai dai kawai saboda sakacin malaman daji.

“Muna kasafta biliyoyin daloli duk shekara. Duba da yadda ake rasa rayuka a irin wannan wutar saboda sakaci malaman dajin, dole su yi gyara ko kuma gwamnati ta dakatar da tura musu kudi.

“Idan muka cire sakaci muka lura da dajukan da kyau, za mu iya magance afkuwar irin wannan matsalar da ke faruwa a California,” inji shi.

Sai dai wasu da yawa daga cikin ’yan siyasa da fitattun mutane a Amurka sun nuna rashin jin dadinsu na yadda Shugaba Trump ya kalli lamarin.