✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ya kamata mu kasance a rayuwarmu ta yau da kullum

Assalamu alaikum; ya ku masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. A yau za mu taya juna tambihi, inda za mu duba wasu hikimomi domin…

Assalamu alaikum; ya ku masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. A yau za mu taya juna tambihi, inda za mu duba wasu hikimomi domin su yi mana jagorar yadda za mu tafiyar da rayuwarmu, irin yadda za mu kasance masu amfani ga kawunanmu kuma masu amfani ga sauran al’umma.

A wannan karon, zan ja hankalinmu ne zuwa ga wani mashahurin gwarzo, mai hikima; wanda ya kasance jagora ga al’umma. Wannan gwarzo kuma sadauki, shi ne Aliyu dan Abi Dalibi (Allah Ya kara masa yarda). Shi ne ya sassaita al’umma da tarin hikima da falsafar rayuwa. An ruwaito shi yana cewa, a rayuwarmu ta yau da kullum, mu kasance kamar kudan zuma.

Da yake kara bayani game da wannan batu, fasihin sai ya ce, a rayuwar kudan zuma, duk wani abu da zai ci mai kyau ne kuma mai tsarki. Ba ya cin wani abu mai datti ko wanda ya kasance najasa. Haka kuma duk wani abu da kudan na zuma ya aje ko ya jefar, abu ne mai dadi kuma mai dadadawa. Wani abu na uku game da shi kuma shi ne, duk inda zai zauna, wuri ne mai kyau kuma mai karfi, wanda ba ya karyewa.

Ko ina ma’ana da tasirin haka? Na farko dai, idan mutum ya kasance kamar zuma, babu shakka zai zama mai amfani ga kansa, kuma ya amfanar da sauran al’imma. Mutum zai kasance mai tsantsani ga abin da zai ci, domin kuwa duk abin da zai ci, zai kasance mai kyau ne kuma mai tsarki. Idan haka ta faru, ka ga mutum ba zai yi kokarin cin abincin haram ba, ba zai ci abin da shari’a ta hana shi ba, madamar ya yi koyi da halin zuma. Madallah kuwa da mutumin da ya kaurace wa cikinsa daga haram, ya kaurace wa cikinsa daga datti, domin kuwa zai kasance mutum mai lafiya a karan kansa, sannan kuma ya kasance mai amfanar da sauran al’umma da yake zaune a cikinsu.

Kamar kuma yadda bayani ya gabata, cewa duk abin da kudan zuma zai aje ko zai jefar, abu ne mai dadi kuma mai dadadawa. Idan mutum ya ce zai yi koyi da kudan ta wannan fanni, babu shakka zai kasance mutum marar rowa, mai rarraba alheri ga sauran al’umma. Mu duba, duk abin da zuma ta zubar ko ta kasayar, abu ne da zai amfani al’umma. Zai kasance magani, zai kasance abinci, da sauransu.

Madalla da mutumin da zai zama kamar zuma ta fuskar rarraba alheri. Domin kuwa a duk lokacin da zai aiwatar da wani abu, zai aiwatar da shi da inganci, idan ma ya kasance dan kasuwa, to ba zai sayar da gurbatattun kaya ga mai saye ba, sai dai ya mika kyakkyawa kuma mai inganci, kamar dai yadda kudan zuma yake yi. Idan aka samu haka cikin al’umma kuwa, da shi ke nan, babu cuta kuma babu cutarwa.

Abu na gaba da ke bukatar bayani shi ne, yadda aka ce kudan zuma ba ya zama wuri sai mai karfi, wanda ba ya karyewa. Idan mutum ya so ya yi koyi da kudan ta wannan fanni, ke nan zai kasance mai gaskiya, wanda ya kama hanyar gaskiya, wacce ba ta tsinkewa ko alama. A duk lokacin da mutum ya durfafi hanyar gaskiya, babu inda za ta kai shi sai ingantaccen wuri, inda zai samu tsira. Madamar mutane sun kasance kamar kudan zuma, suka rika zama a wuri mai karfi, suka rika kama reshe, suna sakin ganye, babu shakka al’umma za su kasance cikin ni’ima a kowane lokaci. Babu cuta babu cutarwa, sai gaskiya da gaskiya da zaman gaskiya.

Wasu darussa da za mu kara dorawa bisa wannan hikima ta fasihin gwarzo su ne: Mu kasance masu yawan yin afuwa ga juna, musamman ma a lokacin da muka fusata, muka harzuka. Mu kasance masu dauriyar yin kyauta a lokacin da muke cikin matsatsi. Mu kasance masu kamewa daga aikata barna a lokacin da muka samu kanmu cikin kadaici da damar yin haka. Haka kuma, mu lizimci fadin gaskiya koda a gaban wane ne, koda a gaban wadanda muke tsoro ne.

Fa’idojin da ke tattare da aikata haka suna da dimbin yawa. Misali, a lokacin da muka lizimci yin amfuwa a lokacin da muke cikin fushi, babu shakka za mu kunyata Shaidan. Daga nan sai al’umma su kasance cikin aminci da juna. Idan kuwa muka saba da kamewa daga aikata barna a lokacin da muke da aikon aikatawa. Nan ma sai tasirin haka ya amfani jama’a. A lokacin da muke yin kokarin kyauta a lokacin da muke cikin matsatsi, to idan muka samu budi, ya kake zaton al’umma za ta kasance? A lokacinn da muka saba da fadin gaskiya koda ga wadanda muke tsoro ne, shi ke nan, duniya ta yi kyau kuma ta gyaru.

Muna addu’ar Allah Ya yi mana jagora, Ya kuma ba mu karfin gwiwar dabbaka wadannan kyawawan dabi’u a rayuwarmu, amin.