✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yaki da ’yan bindiga ke jawo cece-kuce a Zamfara

Jim kadan da kaddamar da shirin kakkabe ’yan bindiga da suke satar shanu da garkuwa da mutane a Jihar Zamfara da makwabtanta jihohin Katsina da…

Jim kadan da kaddamar da shirin kakkabe ’yan bindiga da suke satar shanu da garkuwa da mutane a Jihar Zamfara da makwabtanta jihohin Katsina da Kaduna a makon jiya, sai aka fara samun korafin da ya jawo cece-kuce game da ya yadda yaki da ’yan bindigar yake gudana.

A makon jiyan ne Ministan Tsaro wanda dan asalin Jihar Zamfara ne Birgediya Janar Mansur Dan Ali (mai ritaya) ya yi zargin cewa akwai wadansu sarakuna da suke goya baya ga ’yan bindigar zargin da Majalisar Sarakuna ta Jihar ta musanta tare da kalubalantar Ministan ya bayyana sunayen sarakunan da yake zargi.

Kwatsam a cikin makon sai ga Majalisar Sarakuna ta Jihar ta fito tana zargin Rundunar Sojin Sama da kai hari a kan fararen hula, zargin da rundunar ta musanta tare da kalubalantar masu zargin su kawo shaidar suna kai harin ne a kan fararen hula inda ta ce harin da dakarunta suke kaiwa suna auna shi ne a kan maboyar ’yan bindiga.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa da’awar da dukkan bangarorin biyu suke yi kowannensu yana da alamar gaskiya, inda ta gano akwai kauyukan da sojan saman suka kai wa hari, wadanda a yanzu haka suke ci gaba da alhinin abin da ya faru. Suna masu cewa ba su san laifin da suka yi har da za a yi masu kisan gilla ba.

To amma a gefe guda Aminiya ta gano cewa a wasu lokuta ’yan bindigar ne suke fadawa cikin kauyuka domin su saje da jama’a a duk lokacin da sojin saman suka kai musu farmaki.

Wani mazaunin kauyen Dumburum, a Karamar Hukumar Zurmi, kauyen da sojin sama suka kai w hari, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya “A ranar Talatar 9 ga Afrilu da misalin karfe 4: na yamma, jim kadan da idar da Sallar La’asar sai muka ga jirgin saman na soja ya zo ya yi shawagi na wasu mintoci ya tafi. Daga nan kuma sai ya sake dawowa, da yake mutanen garin sun saba ganin jiragen yaki suna shawagi a yankin don haka babu wanda ya damu. Kwatsam sai muka ga jirgin ya fara harba rokoki a kan gidaje, sai kowa a garin ya gigice muka fara gudu zuwa maboya. Wadansu suka shige gidaje wadansu suka fita wajen gari,” inji shi

Ya kara da cewa: “Bayan minti biyu da tafiyar wannan jigin yaki sai wani jirgin yaki helwafta ya zo ya ci gaba da kai hare-hare a kan gidajen jama’a kuma ya kashe mutum 11 ya jikkata wadansu da dama kuma ya lalata gidaje fiye da 20.”

Sai dai wani mazaunin yankin Kawaye da ke Karamar Hukumar Anka a Jihar Zamfarar mai suna Murtala ya ce wani lokaci barayi sun je da nufin kai hari a kan kauyen Jarkuka, sai aka sanar da sojoji, zuwa can sai ga wani jirgin yaki helkwafta ya zo. “Ko da su ’yan bindigar suka hango jirgin sai suka gudu suka buya. Daga nan jirgin ya tafi, sai su barayin suka fito daga inda suke boye, can sai jirgin ya sake dawowa sai ya fara jefa musu bama-bamai.”

Ya kara cawa: “Koda aka fara yi musu ruwan wuta sai suka fara gudu suka tunkari gari don su saje da sauran mazauna garin, to a nan ne jirgin ya yi harbi ya kashe wadansu yara uku da ke wanka a wani kududdufi da ke bayan garin.”

Kazalika ya shaida wa Aminiya cewa ya ga wasu motocin soja guda goma sun wuce ta garin nasu sun shiga wani daji da ke kusa da su. Kuma ayarin motocin sun dawo da misalin karfe tara na dare.

Ya kara da cewa sun ga gungun barayin da garken shanu sun nufin wajen kauyukan Tamuzge da Duza da Tashar Birai da kuma Tungar Daji. Kuma suna kai mutanen da suka sace zuwa can wani daji ne da ake kira dajin Gora.

Shi ma da yake shaida wa Aminiya abin da ya faru lokacin da wani jirgi ya kai hari a kauyen Mutu da ke Karamar Hukumar Tsafe, wani mazaunin garin ya ce harin na Mutu da jirgin yaki ya kai ya ritsa da Na’ibin Limamin garin da matarsa da ’ya’yansa. “Garin Mutu yana kan iyakar kananan hukumomin Tsafe da Gusau ne, kuma garin yana bakin wani daji da ake kira dajin Gwamna wanda ya raba iyakar jihohin Zamfara da Katsina. An dade ana zargin garin na Mutu da zama mai ba da mafaka ga ’yan bindiga da suka addabi Tsafe ta Gabas. An ce su barayin kan yi amfani da garin don zama tudun mun tsira,” inji shi.

Ya ce “Abin da ya faru shine, jirgin saman yakin ya hango gungun barayin a kan babura sai ya biyo su, koda barayin suka fahimci jirgin ya gan su sai suka kwarara cikin garin da nufin boyewa. Daga nan sai jirgin ya fara harbi zuwa cikin garin. Shi Na’ibin Limamin ya fito ne daga gidansa domin ya sake maboya bayan da ya ji wutar ta yi yawa, to daga nan wata roka da jirgin ya harbo ta daki kusa da inda yake kuma ta lalata mashi kafa.”

Duk da haka mutanen da Aminiya ta tuntuba a yankin suna yabawa da yadda rundunar sojen ke kai farmaki a kan ’yan ta’addar inda suka ce kwarin gwiwar jama’a ya karu cewa jami’an tsaron za su iya shawo kan matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a jihar.

A shekaranjiya Laraba ce sarakunan jihar suka fitar da jerin sunayen da suka ce na mutanen da aka kashe ne a harin sama da jirgin yaki ya kai a kauyen Dumburum a Karamar Hukumar Zurmi.

Sarakunan sun ba da sunayen wadanda suka rasu kamar haka:  Maidaji Barau na Dumburumn da Suwaiba Alka da ’Yar Guru na Dumburum da Maryam Shafi’u da Dahe Malan Sule da Buhari Dankurma da Zaliha ta Dumburum da A’isha Akilu da Al’amin Alka da Fati ’Yar Gum.

Wadanda suka samu raunuka kuma su ne: Haruna Kusu da Muhammad M. Sani da Abdurrazak Abubakar da Yakubu Yunusa da Dan Diyya da Sa’a Dayyabu da  ’Yarwargi Mamman da Gwamna na Dumburum da Rashida Alka da Maryam Akilu da Sadik Sukuranu.

Sarakunan sun ja hankalin hukumomi cewa an ga wani bam da bai tashi ba a wani gida a garin na Dumburum, inda suka bukaci a gudanar da bincike a kan lamarin.

Sarkin Fulanin Bungudu wanda ya yi magana a madadin sarakunan ya shaida wa wakilinmu cewa a shirye Majalisar Sarakunan take ta ba da hadin kai wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Kimanin mako uku ke nan da Rundanar Sojin Najeriya ta kaddamar da da wani sabon yaki da ’yan bindiga da masu satar shanu da garkuwa da mutane da ta yi wa lakabi da “Shirin Harbin Kunama.”

A watan Yulin shekarar 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da atisayen “Harbin Kunama” a Gundumar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru mai fama da bala’in ’yan bindiga, amma sai lamarin ya ci gaba da kazancewa har zuwa wannan lokaci.

An kashe sama da mutum 100 a wani kazamin hari da ’yan bindigar suka kai a ’Yar Galadima, mai tazarar kilomita 20 Arewa da garin Dansadau a watan Afrilun 2014.

A wannan shekarar da muke ciki, ’yan bindigar sun kashe akalla mutum 179 a hara-haren da suka kai wa kauyuka 17, inda mutane da dama suka jikkata.

Karamar Hukumar Shinkafi ce ta fi dandana kudarta a bana kawo yanzu inda aka kashe kimanin mutum 104, bayan hare-hare a kan kauyukanta biyar a Gundumar Kware a tsakanin watan Fabrairu da Maris din bana, kuma mutane da dama sun arce daga muhallansu.

A watan Janairun da ya gabata an kashe mutum 25 a hare-hare kan kauyuka 9 da ke Karamar Hukumar Gusau. Kuma an harbe mutum 13 a kauyen Kawaye da ke Karamar Hukumar Anka a watan Fabrairun da ya wuce.

A watan Maris kuma an hallaka mutum 20 a kauyen Gando da ke Karamar Hukumar Bukuyyum, kuma mako daya bayan harin ’yan bindigar sun kashe mutum 17 a harin da suka kai a Masallacin Juma’a na kauyen Dumama da ke Karamar Hukumar Zurmi.

An shirya atisayen Harbin Kunama III ne da nufin kakkabe gungun ’yan ta’adda  a dazukan jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina wanda zai gudana daga 1 ga Afrilu zuwa 30 ga Yunin bana.

Hafsan Hafsoshin Sojin Kasa, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai wanda Manjo Janar Lamidi Adeosun ya wakilta ya ce a da an shirya fara atisayen ne daga 2 zuwa 27 ga watan Yuni bana, to amma yadda abubuwa suka ta’azzara suka sa aka canja shawara, kuma aka kara fadada atisayen zuwa dukkan maboyar ’yan taadda a dazukan jihohin Arewa maso Yamma.

“Kamar yadda kuka sani kashe-kashe na ci gaba da ta’azzara a wasu jihohi na Arewa maso Yamma. Wadannan miyagun ayyuka sun shafi harkokin tattalin arziki da zamantakewa. Mutane da dama sun rasa rayuka, kuma dukiya ta salwanta,” inji Buratai.

An kaddamar da ire-iren wadannan atisaye na soja a baya, kamar su atisayen “Sharar Daji” da na “Dirar Mikiya” wadanda rundunar sojin sama ta kaddamar. Rundunar sojan sama ta ce ta kai hari a kan maboyar ’yan bindigar a dazukan Sububu da kuma Ajja. Kuma mazauna yan kunan karkara da dama da suka yi magana da wakilinmu sun ce matakin da ake dauka a ’yan kwanakin nan kwalliya tana biyan kudin sabulu.

A wata sanarwa da Kakakin Sojin Sama Iya Kwamanda Ibekunle Daramola ya fitar a shekaranjiya Laraba ya ce Rundunar Sojin Sama ta samu nasarar tarwatsa wani gungun ’yan bindiga da suka addabi Jihar Zamfara.Sanarwa ta ce, sakamakon rahotannin sirri da ta samu cewa wadansu gaggan mahara na tattaruwa a yankin kauyukan Rafi da Doka a Gundumar Mada a Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamafara, nan take rundunar ta tashi sojinta na musamman a jiragen yaki, domin tarwatsa ’yan bindigar daga garuruwan biyu a ranar Talatar da ta gabata.

Sanarwar ta ce dakarunta sun hadu da tirjiya daga ’yan bindigar, kuma a wannan dauki-ba-dadi sojin saman sun yi nasarar hallaka ’yan bindiga biyu, yayin da saura suka tsere da raunukan bindiga. Sanarwar ta ce sojojin saman da takwarorinsu za su ci gaba da wannan aiki har sai sun kakkabe mahara a yankin Arewa maso Yamma.