✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka dauke mani yara hudu – Hadiza Mai Abinci

A kwanakin baya ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Moriki, a cikin Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara da…

A kwanakin baya ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Moriki, a cikin Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara da misalin karfe goma na dare kuma suka tafi da mutane shida. A cikin wadanda aka dauka har da ’ya’yan wata mata mai aikin dafa wa dalibai abinci a makarantar, mai suna Hadiza Abdulkadir.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da ita a kan abin da ya faru, Hadiza ta bayyana cewa “yadda abin ya faru shi ne, muna cikin gida, kawai sai na ga mutum uku da bindigogi. To, da suka zo akwai wani yarona mai suna Hayatu, sai ya gudu cikin kewaye ya boye. Ashe sun gan shi, sai suka fada kewayen suka fito da shi suka kwace masa wayarsa.

“Suka zo inda nake ni ma, suka ce in ba su waya, sai na fada masu cewa wayata tana daki. Sai wani yarona mai kimanin shekara 16, mai suna Abdurrahaman ya dauko masu wayar. Nan suka kama ni suka ce in kai su dakunan kwanan dalibai, in kai su wurin yara. Sai na ce masu mu ba mu da yara. Suka ce mani idan ban kai su ba za su harbe ni. Haka suka suka zo inda mai gadi yake, shi ma suka kwace masa waya.”

Hadiza ta ci gaba da cewa “to a lokacin da suke magana da maigadi sai na zare jiki a hankali na gudu na buya a cikin wani kewaye da ke kusa. Kuma Allah bai ba su ikon ganin lokacin da na gudu na boye ba

“Na kubuta daga hannunsu, to amma sun tafi da ’ya’yana hudu, Zubairu, Maryam, Fatima da kuma mijinta. Ina cikin damuwa don haka ina rokon jami’an tsaron jihar nan da su taimaka su kubutar da su. Haka ma ina rokon jama’a da su taimaka mani da addu’a,” inji taTo sai dai wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun shiga harabar makarantar ne bayan da suka haura katanga da misalin karfe goma na dare.

“An ga wadannan ’yan bindiga suna shawagi tun misalin karfe hudu na yamma. Kuma kasancewar akwai ’yan bangarmu na zarumai da gora, ba su iya shigo cikin garin a wannan lokacin ba.

“Tun ba yau ba wadannan ’yan bindiga suke kai hari a garin na Moriki suna yin garkuwa da mutane. Ba ma garin Moriki kadai ba, duk wadanda suke bin wannan hanya zuwa Shinkafi suna fuskantar cin zarafi daga wadannan ’yan bindiga,” inji shi.

Ya kara da cewa kusan duk bayan ’yan kwanaki sai ka ji barayi sun tare hanyar zuwa Shinkafi sun kashe jama’a, sun kuma yi garkuwa da wasu mutanen, kuma hanyar tana neman ta zama tarkon mutuwa.

Shi garin na Moriki yana kan hanyar zuwa Shinkafi ne daga garin Kaura Namoda. Haka kuma garuruwan da ke yankin suna cikin taskun ta’asar ’yan bindigar da ke ci gaba da cin karensu ba babbaka a Jihar ta Zamfara.

A yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a kewayen makarantar, kuma mutane na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, duk da cewa jama’a har yanzu suna cikin dardar.

To sai dai wani mazaunin garin Zurmi wanda yake da yarinya ’yar aji hudu a sakandaren ta ’yan mata da ke garin Moriki mai suna Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa tun da ya ji labarin harin ’yan bindigar a kan makarantar, hankalinsa bai kwanta ba.

“Sai da na tafi na ga yarinyata sannan na sami natsuwa. Ba ma ni ba, iyaye da dama sun je makarantar kuma sun ga yaran nasu domin mun gode wa Allah cewa babu dalibar da aka dauka”

To sai dai shi ma wani mazaunin garin Kaura Namoda wanda yake da yara biyu a makarantar mai suna Kabiru Aliyu, ya shaida wa Aminiya cewa duk da ba a dauki yaran ba har yanzu shi hankalinsa ba zai kwanta ba in ba gani ya yi cewa yaran sun dawo gida ba.

“Ni fa har na fara tunanin canza masu makaranta saboda al’amarin yana da ban tsoro. Idan aka dauki yaran nan ta ya zan yi in karbo su? Ni dai ba ni da miliyoyin kudin fansa. Don haka dole in yi taka-tsan-tsan,” inji shi.