✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka sace dan kasuwa a gadon jinya

Wasu mutane dauke da manyan bindigogi sun kai samame a kauyen Sankara na yankin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa inda suka sace wani hamshakin…

Wasu mutane dauke da manyan bindigogi sun kai samame a kauyen Sankara na yankin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa inda suka sace wani hamshakin dan kasuwa da ke kwance yana jinya.

Al’amarin ya faru ne ranar Asabar inda mutanen, wadanda ake kyautata zaton ’yan bindiga dadi ne suka yi nasarar sace Alhaji Yusif Maifata aka neme shi aka rasa.

Bayanai dai sun nuna cewa ’yan bindigar sun mamaye kauyen na Sankara ne da misalin karfe 1:47 na dare suna ta harbin iska har suka razana mutane suka hana kowa fitowa.

Kafin hakan ta faru an ce da ma dan kasuwar ya jima yana fama da rashin lafiya kuma  ranar Alhamis aka sallamo shi daga asibiti, ya koma kauyen na Sankara.

“Shi ne barayin suka yi amfani da wannan damar suka sace shi”, inji daya daga cikin ’yan uwan Alhaji Yusuf, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

‘Barayin sun nemi miliyan 40’

Ya kara da cewa, “Wadanda suka sace shi sun bukaci ’yan uwansa da mu kawo masu Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa, kuma sun tambayi irin abincin da ake ba shi da kuma nau’in magungunan da likita ya dora shi a kai”.

Ya kuma ce a lokacin da barayin suka yi ta harbe-harbe da bindiga dan kasuwar ya firgita matuka har ya sa ya fita daga hayyacinsa.

Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya ce wanda aka sace din yana da shekara 75 kuma suna kokarin ceto shi daga wajen barayin mutanen.

Ya ce tuni rundunar ta tura tawagar ’yansanda daga sashen yaki da fashi da makami da aikata miyagun laifuffuka yankin don ganin an ceci rayuwar Maifata.

Ya kara da cewa har zuwa lokacin da yake zantawa da wakilinmu ba su da labarin barayin sun bukaci wani kudi daga wajen iyalan dan kasuwar.