✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura

Yan bindiga sun sace daya daga cikin manyan ’yan Majalisar Masarautar Daura da ke Jihar Katsina, Alhaji Musa Umar Uba Magajin Garin Daura. ’Yan bindigar…

Yan bindiga sun sace daya daga cikin manyan ’yan Majalisar Masarautar Daura da ke Jihar Katsina, Alhaji Musa Umar Uba Magajin Garin Daura. ’Yan bindigar da aka su hudu ne sun dirar masa a gidansa da ke tsakiyar birnin Daura suka yi gaba da shi a shekaranjiya Larab.

Basaraken tsohon jami’in a Hukumar Kwastam kuma dan uwa ne ga Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar.

Wani ganau da abin ya faru a kan idonsa, Malam Abdullahi, ya fada wa Aminiya lokacin da ’yan bindigar suka je gidan Basaraken sun zo ne a cikin motoci kirar fijo shudiya da a kori-kura kirar Toyota Hilud.

“Sun same shi a kofar gidansa a Unguwar Kwanar Agam a birnin Daura suka sace shi da misalin karfe 7 bayan Sallar Magariba,” inji shi.

Wani Malam Muhammad wanda ganau ne ya ce ganin abin suke yi kamar wasan kwaikwayo. “Mun yi Sallar Magariba tare da shi a makwabta sannan ya koma kofar gidansa. Kamar yadda ya saba idan ya yi Magariba yakan zauna a kofar gidansa har sai ya yi Sallar Isha’i kafin ya shige gida. Lokacin da yake zaune a kofar gida sai aka kira shi a wayar salula. Bisa ga dukkan alamu wadanda suka kira shi sun ce za su zo su gan shi ne. Mintuna kadan sai ga su sun karaso suka ajiye motocin, sannan suka gabato ga Magajin Gari. Cikin gaggawa suka kama shi suka saka shi cikin wata mota da take tsaye a gabansu,” inji shi.

Ya ce, “A lokacin da mutane suka kawo dauki sai ’yan bindigar suka fara harbi a sama ba kakkautawa wannan ya sa mutane suka gudu domin tsira da rai.”

Da aka tambaye shi ina masu tsaron Basaraken sai ya ce kawai wadansu dogarai ne kalilan suke tare da shi. “Wannan ya faru ne saboda garin Daura da kewaye suna zaune lafiya,” inji shi.

Wata majiya wacce ba ta so a bayyana sunanta ba, ta ce mai yiwuwa dalilin da ya sa aka sace Magajin Garin Daura shi ne dangantakarsa.

“Ka san Magajin Gari yana auren Hajiya Bilkisu, ’yar uwa ga Shugaba Kasa Muhammadu Buhari, wacce ’yar babbar yayarsa ce Hajiya Rakiya. Kuma Magajin Garin mahaifin Fatima ce wadda matar babban dogarin Shugaban Kasa ne Kanar Muhammadu Abubakar. Mudai ba mu taba fuskantar irin wannan mummunan yanayin a Daura ba, duk da cewa muna kan iyaka. Kodayake babu wanda aka kashe kuma ba wanda ya ji wani rauni, amma mutane sun gigice.”

Har yanzu masu garkuwar ba su tun tubi iyalan Basaraken ba

Wata majiya mai karfi ta shaida wa Aminiya cewa bayan ’yan bindigar sun yi harbi a sama sai suka nufi garin Zango cikin hanzari, garin da ke kilomita 16 daga Daura kuma ya yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.

’Yan bindigar sun kashe wayar Magajin Garin saboda haka ba za a ji duriyarsa ba. Kuma ba su tuntubi iyalansa ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin Mai magana da yawun Masarautar Daura Usman Ibrahim, ya ce mutane sun yi yunkurin kubutar da Magajin Garin amma ’yan bindigar suka yi harbi sama suka razana mutane suka tarwatse.

Shugaban Karamar Hukumar Daura, Injiniya Abba Mato ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin ta tarho, inda ya ce sun sanar da jami’an tsaro faruwar lamarin kuma an yi yunkurin kawo dauki abin ya faskara.

Injiniya Mato, ya ce bayan kokarin da jami’an tsaro suka yi na kubutar da Basaraken, malamai da jama’ar gari sun yi kira a dukufa ga addu’a Allah Ya tona asirin masu hannu cikin lamarin.

Wata majiya ta ce jami’an tsaro da suka hada da sojojin sama da na kasa da ’yan sanda da jami’an shigi-da-fice sun dukufa don gano inda Basaraken yake a dukkan iyakokin Daura da Nijar da suka hada da hanyar Daura zuwa Zango da Daura zuwa Kongolam zuwa Mai’adua da Daura zuwa Sandamu da sauransu.

“Jami’an tsaron kasar Nijar suna sa ido sosai a kan lamarin, muna da tabbacin nan ba da jimawa ba za a kama masu garkuwar,” inji majiyar.