Daily Trust Aminiya - Yadda ’yan bindiga suka sare kan mutanen Jigawa 3 suka tafi
Subscribe

Yadda ’yan bindiga suka sare kan mutanen Jigawa 3 suka tafi da su a Taraba

Wadansu ’yan bindiga sun kashe mutum uku ’yan asalin Jihar Jigawa da suke zaune a kauyen Yalwan Tau a ke Karamar Hukumar Jalingo a Jihar Taraba.

’Yan bindigar, wadanda har zuwa hada rahoton nan ba a kama su ba, sun yanke kawunan wadanda suka kashe, suka yi awon gaba da su.

Aminiya ta gano, cewa wadanda aka kashe suna aiki ne a wata gonar shinkafa tare da wadansu ’yan uwansu biyu, lokacin da ’yan bindigar suka kai musu hari da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata.

Amma Aminiya ta samu labarin cewa, biyu daga cikin wadanda aka kai wa harin sun sha da kyar, sai da kuma sun samu munanan raunuka.

Dukkan wadanda aka kai wa harin ’yan asalin wani kauye ne mai suna Yalwan Damai da ke  Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.

Daya daga cikin wadanda suka tsira, mai suna Salihu Muhammed ya shaida wa Aminiya cewa duk shekara suna zuwa garin Yalwan Tau don yin aikin kwadogo a gonakin shinkafa.

Ya ce wani mai suna Alhaji Musa Umar ne ya ba su aiki a gonarsa. Kuma suna cikin aiki ne wadansu dauke da bindigogi suka kewaye su, suka bude musu wuta.

Salihu Muhammed, wanda yanzu ke kwance a Asibitin Tarayya da ke Jalingo, ya ce su biyu da kyar suka sha amma ’yan bindigar sun harbe su a sassan jikinsu.

Ya ce uku daga cikinsu duk ’yan bindigar sun kashe su kuma suka sare kawunansu, suka tafi da su.

Ya ce wadanda aka kashe su ne Muhammed Adamu Daba da Shehu Shayaro da Adamu Gambo kuma dukkansu sun fito ne daga garin Yalwan Damai da ke Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa an kawo gawarwakin wadanda aka kashe dakin ajiye gawa da ke Asibitin Tarayya na Jalingo.

’Yan sanda kuma sun kama Alhaji Musa Umar, wanda ya ba wadanda aka kai wa harin aiki a gonarsa.

Daruruwan ’yan ci-rani daga jihohin Jigawa da Bauchi da Gombe da sauran jihohin Arewa masu nisa ke zuwa aikin yankan shinkafa a sassan Jihar Taraba  duk shekara amma yawancinsu suna fuskantar matsaloli masu dama, har ma wasu lokuta suna rasa rayukansu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Dabid Misal bai amsa kiran waya da wakilinmu ya yi masa ba dangane da wannan lamari.

texem
More Stories