ADVERTISEMENT

Yadda ‘yan Boko Haram sanye da kayan soja suka kashe soja 48

Ana ci gaba da samun karin haske a kan harin da ‘yan Boko Haram suka kai wa sojoji a Arewacin Jihar Borno a ranar Alhamid da ta wuce.

ADVERTISEMENT

 

ADVERTISEMENT

Majiyoyi da yankin da kuma bangaren sojojin sun tabbatar da cewa lallai an kai harin, kuma ‘yan Boko Haram din sunya kayan sojoji ne, sannan kuma sun yi amfani ne da bindigu da motocin sojoji wajen kai harin.

 

A harin dai an kashe kusan sojoji 50, “’Yan Boko Haram din sun yi amfani da makaman da suka sace wa sojoji ne daga Jilli na Jihar Yobe domi kawo wannan harin na Zari.

 

“Sojoji sun yi kokari sosai wajen fafatawa da su, amma sun fi karfinsu, wanda hakan ya sa dole su ja baya bayan an kashe sojoji da yawa. Sannan kuma ‘yan ta’addan da suka yi kwantar bauna daga nesa sai suka bi sojojin da suke kokarin ceton ransu, suka kashe su, amma suma an kashe su da yawa.  

Wani mazaunin Mobbar na Jihar Borno, Kime Alhaji Baana ya tabbatar da cewa lallai an gwabza fada tsakanin sojoji da Boko Haram, “amma daga jiragen yaki sun kawo wa sojoin dauki, inda suka taimaka wajen Koran ‘yan ta’addan. Har yanzu akwai gawawwaki a cikin daji,” inji shi.

Rundunar sojoji ta bakin mai magana da yawun rundunar yaki da Boko Haram, Onyema Nwakchukwu dai ta tabbatar da harin a ranar Juma’a, inda ta ce ba kashe mata soja ba.

Amma kuma rahotanni daga Jihar Borno tun a ranar Lahadi suka nuna cewa an samu gawa guda 30, sannan kuma daga aka kara samun wasu guda 16, wanda jimilla ya zama 48.