✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Boko Harama suka kashe mutum 56 a wajen jana’iza

A karshen makon jiya ne wadansu da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai harin ramakon gayya ga mutanen kauyen Badu Kauwa Malam Kyallori,…

A karshen makon jiya ne wadansu da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai harin ramakon gayya ga mutanen kauyen Badu Kauwa Malam Kyallori, mai nisan kilomita 25 daga Karamar Hukumar Nganzai da ke Jihar Borno, inda suka kashe mutum 56.

An kai harin ne a lokacin da mutanenkauyen  suke gudanar da jana’izar wata matar, inda suka kashe mutum 56 tare da jikkata sama da 60.

Malam Bukar Modu daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, ya ce, “Muna tsakiyar gudanar da jana’izar wata makwabciyarmu da ta rasu da yammacin ranar Asabar, sai muka hangi ’yan Boko Haram suna zuwa a kan babura, sai suka bude mana wuta muka watse. Da kyar na tsere amma daga baya mun dawo mun duba wadanda suka kashe da wadanda suka jikkata, wadansu sun shiga cikin daji, wadansu kuma sun fita daga kauyen zuwa wasu kauyukan domin abin ya shafi matanmu da ’ya’yanmu kanana. Sun zo da babura 7 kowane babur akwai mutum uku suna rike da bindigogi. Da yake mun gudu mu buya ne a wani rami, bayan sun tafi sai muka fara tunanin yaya za mu yi? Sai muka tafi wajen jami’an tsaro muka shaida musu halin da ake ciki amma ba mu samu jami’an tsaro ba. Kawai sai muka yi ta kanmu ba mu tsaya ba. A lokacin mutum 24 suka rasu kafin daga baya suka karu.”

Tuni Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara ya kai ziyarar jaje ga al’ummar garin, inda ya nuna bakin ciki da damuwarsa game da faruwar al’amarin, ya ce, “Ban ji dadin faruwar wannan al’amarin ba kuma ina jajanta muku bisa rasa rayukan mutane sakamakon wannan harin kuma ina mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da fatan Allah Ya jikansu. Idan mun koma za mu gudanar da taro da manyan jami’an tsaro don sake lalubo wasu dabarun  tsaron, kuma ina roko ga su ’yan Boko Haram su yi wa Allah su daina abubuwam da suke yi na kashe wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Su zo a yi zaman sulhu da gwamnati, domin idan sun mika wuya akwai tsarin da gwamnati da ta bullo da shi na gyaran halaye inda za a karbe su hannu bibiyu kuma a gyara halayensu tare da taimaka musu a rayuwa. Don haka ina kira gare su da su ajiye makamansu.’’

Yankin Karamar Hukumar Nganzai mai nisan kilomita 85 yana Arewacin Borno ne, kuma ya sha fama da hare-haren Boko Haram a baya. Kuma ana zaton wannan hari da Boko Haram din ta kai na ramuwar gayya ce, saboda ba da dadewa ba aka kashe wadansu ’yan Boko Haram din a kauyen.