✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan fashi da ’yan garkuwa suka addabi Jihar Katsina

Ahmed Kabir S/kuka, Katsina Matsalar satar shanu da garkuwa da mutane sun fara yawaita ne a Jihar Katsina a 2016, bayan matakin sulhu da Gwamnatin…

Ahmed Kabir S/kuka, Katsina

Matsalar satar shanu da garkuwa da mutane sun fara yawaita ne a Jihar Katsina a 2016, bayan matakin sulhu da Gwamnatin Masari ta ɓullo da shi a tsakanin manoma da makiyaya, sulhun da ya fara haifar da ɗa mai ido kafin ɓallewar su Baharin Daji waɗanda suka yi wa tsarin karan tsaye.

An riƙa samun ’yan matsaloli nan da can amma mafi yawa a yankunan Jihar Zamfara. Kamar yadda wani wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya: “Muna iya aza taɓarɓarewar wannan sha’anin tsaro a nan Jihar Katsina musamman a kan abin da ya shafi sata da kuma garkuwa da mutane tun bayan shigowar ’yan gudun hijirar Jihar Zamfara a yankunan da suke maƙwabtaka da mu. Dalilin faɗin haka shi ne, kamar yadda muke samun labari, su waɗannan miyagun mutane sun riƙa yin basaja suna shigowa cikin ’yan gudun hijirar domin yin leƙen asiri.

“Ta hakan ne kuma har suka riƙa samun waɗanda suka riƙa ba su labari. A haka suka mamaye waɗannan wurare domin dukkan inda abin ya shafa babu inda babu waɗannan masu gudun hijira. Hakika, an san abu ne mai wuyar gaske a iya tantance waɗannan mutane daga cikin sauran amma dai wannan na daga cikin abin da ya haifar da bazuwarsu cikin ƙaramin lokaci.”

Majiyarmu ta ci gaba da cewa, “Bata garin da muke da su a cikin birane marassa aikin yi, musamman matasa da kuma wasu daga cikin manya marasa sanin ciwon kai sun shiga cikin wannan harkar domin suna ganin hanya ce ta samun kuɗi cikin sauri ba tare da tunanin abin da ka iya biyowa baya ba.”

Da Aminiya ta so jin ta bakinsa a kan zargin da wasu ke yi na cewa akwai batun siyasa a cikin al’amarin, ya ce, “ko tantama babu a kan wannan. Domin ka san ita siyasa abu ce wadda take tattara abubuwa da yawa, musamman daga ɓangaren masu adawa da kuma masu son yi wa gwamnatin da ke ci zagon ƙasa. Saboda haka, a iya yin amfani da wannan dama domin kawo naƙasu ga masu mulki. Kuma ka san babu abin da ya fi ɗaukar wa jama’a hankali irin a ce akwai asarar dukiya da rayuka. Sannan kuma akwai wani ɓangaren da su ma za su iya amfani da wannan dama, wato irin mutanan nan masu son su yi kuɗi ko ta halin yaya, to balle uwa uba ga matasanmu nan zaune babu aikin yi. Ka ga a cikinsu ake samun ƙauraye da ’yan daba da manyan mashaya da kuma masu dillacin miyagun ƙwayoyi, waɗanda su ne ke kan gaba wajen sanyawa ana aikata duk waɗannan manyan laifuffuka saboda mutum ya sha ya gusar da hankalinsa.”

Yadda hare-haren suka canza salo

Shi dai wannan lamari na sata tare da yin garkuwa da mutane a Jihar Katsina, wanda ya fara ɗaukar hankalin jama’a shi ne na sace tare da yin garkuwa da sarakuwar Gwamna Masari, wadda kuma aka sace ta kwanaki uku kafin zaɓen gwamnoni da aka gudanar a kasar nan, wanda shi kansa Gwamna Masarin na cikin ’yan takara.

Kamar yadda Abubakar Sani matashin da ya kitsa tare kuma da jagorantar sauran mutane huɗun da suka sace ta ya ce, an biya kuɗin fansa Naira milyan talatin amma su biyar ɗin sun tashi da Naira miliyan sha ɗaya yayin da sauran Naira miliyan sha tara ta tsaya a hannun dillalai.

Shi ma wani matashin da aka taɓa kamawa daga Rugar Kacallah ya ce abin da ake ba shi bai wuce Naira dubu ashirin ba, duk da cewa aikinsa na tsare waɗanda aka kawo ne.

Sacewa tare da garkuwa da Magajin Garin Daura. wanda aka ɗauke shi a ƙofar gidansa da ke cikin garin na Daura, shi ma ya ja hankalin jama’a matuƙa. Har dai ya zuwa rubuta wannan rahoto babu wani labari a hukumance ko daga iyalinsa da ya bayyana irin halin da Magajin yake ciki, domin an ce har yanzu su masu garkuwar da shi ba su yi magana da kowa ba.

Kisan jama’a barkatai kuwa, ya fara ta’azzara musamman a yankin karnanan hukumomin Batsari da Ɗanmusa da Kanƙara, a inda ƙasa da kwana 7 aka yi asarar rayukan jama’a da dama, daga mabambata ƙauyuka da garuruwa. Kisan ba gaira babu dalili na ƙoƙarin rinjayar yin satar shanun tare da yin garkuwa da mutanen don neman kuɗin fansa. Kisa na baya-bayan nan shi ne wanda aka yi a ƙauyen argamji da ke bisa hanyar Batsari zuwa Jibiya a cikin Karamar Hukumar ta Batsari, inda aka kashe mutane 18. An kuma kai wannan harin ne ba tare da an saci komai ba. An ɗauko gawarwakin aka kai wa Gwamna Masari da Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir. An kuma rufe su a maƙabartar Ɗantakun da ke cikin garin.

An kai wannan harin a garin bayan jama’a na gonakinsu suna yin shuka saboda samun ruwan sama. Kamar yadda Saminu Mayetti mazauni a garin Batsari ya shaida wa Aminiya. Ya ce shi da kansa ya ƙirga gawa 15 nan take a cikin gari kuma mafi yawansu matasa ne.

Wannan lamarin ne ya janyo harzuƙa jama’a da har abin ya kai ga yin zanga-zangar lumana, wadda jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin daƙilewa amma abin ya nemi kai ruwa rana. Hakan ne ya sa aka ɗauko gawarwakin zuwa Katsina.

Ganin irin yadda waɗannan hare-hare da kashe-kashen suke faruwa yasa Gwamna Masari ya soke duk wata hidima ko shagalin da za a yi a lokacin da aka rantsar da shi karo na biyu, domin nuna alhininsa ga jama’ar jihar, musamman su al’ummomin da abin ya shafa.

Haka kuma, wannan matsala ta tsaro ce ta sanya masarautun Katsina da Daura suka bayar da sanarwar ɗage bukukuwan Karamar Sallah kamar yadda aka saba har sai zuwa Babbar Sallah.

Ko dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa za ta yi tasiri Jihar Katsina?

A makonni biyu da suka gabata Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan gyaran dokar Kundin Shari’ar “Penal Code” domin samar da hukuncin da ya dace a kan laifukan da kundin bai yi magana ko ya kunsa a cikinsa a baya ba. Sanya hannu a kan wannan dokar ya tabbatar da hukuncin kisa a kan duk wanda kotu ta samu ta kuma tabbatar da laifin yin garkuwa da mutane (kidnapping) da kuma waɗanda aka samu da laifin satar shanu.

Haka kuma an tanadar da hukuncin daurin rai-da-rai hade da biyan tara ga duk wanda kotu ta samu kuma ta tabbatar ya aikata fyaden. Sannan kuma mai laifin zai biya diyya ga wadda aka yi wa laifin. Ita dai wannan doka ta zo daidai da lokacin da jihar take fuskantar matsalar tsaro a yankunan ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari,Safana, Ɗanmusa, Kanƙara,F askari har zuwa Sabuwa.

Ko yaya jama’a ke kallon wannan doka? Alhaji Ashiru Aliyu Ɗanmasanin Jibiya, wanda karamar hukumarsa na daga cikin masu fuskantar wannan matsala ta tsaro, ya ce: “Gaskiya wannan doka ta zo daidai lokacin da ake bukatarta kuma Gwamna Masari ya isa mutumin da za a jinjina wa a kan ɗaukar ire-iren waɗannan matakai na ganin cewa jihar ta riƙe kambinta na jihar da tafi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya. Muna maraba da kuma goyon bayan wannan doka da shi Gwamna Masari da ya yi wannan hangen nesa da kuma ɗaukar matakin daƙile wannan ta’addanci.”

Shi kuwa Alhaji Ala Narto cewa ya yi hatta da su kansu masu kai wa ’yan ta’addan rohoto su ma wannan hukunci ya hau kansu domin ba su da bambanci da masu aikatawar. “Babban abin da ke kawo wa shari’a cikas a kasarmu abubuwa biyu ne, wato bayar da beli da kuma tirka-tirkar lauyoyi wanda hakan kan ja shari’a ta ɗauki dogon lokaci tare da sauya sabon salo.”

Hajiya Hadiza Saulawa matashiya ce mai jagorantar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke kula da marayu da kuma matan da aka yi wa fyaɗe, ta ce, “ai wannan dokar kamar an yi ta ne domin ƙungiyata. Saboda abin ya zamo har ma ka rasa abin da za ka ce saboda takaici. Sai ka tarar da magidanci ko balagaggen mutun ya samu ƙaramar yarinya wadda ba ta ma san ita kanta ba, wato matsayin cewa shin ita mace ce ko namiji amma an ɓata mata rayuwa baki ɗaya. Mun goyi bayan wannan doka kuma za mu ci gaba da goyon bayanta tare da sanya ido mu ga ana aiwatar da ita sau da ƙafa.”

Akwai yiwuwar matsalar ta shafi noma a bana

Hassan Dogon Faci, ɗaya daga mazauna kuma manoma a yankin na Batsari ya ce: “Ai batun noma a waɗannan yankuna, wato Nahuta, Kasai, Garin Labo, Inwala har zuwa garin Yara sai dai a ce kawai a samu ’yan tsiraru. Domin ga shi garin ’Yargamji jama’a sun ci gaba da harkokin noman amma ina tabbatar maka duk wata gona da ta shafi bakin daji, batun noma dai a bana, to sai wani iko daga Allah. Gonakin bakin gari ne kawai za a iya noma kai tsaye.”

Shin hare-haren sun tsaya?

Mafi akasari idan an ce ga wata doka gwamnati ta sa musamman a kan hana faruwar wani abu, cikin ɗan lokaci za a ga wannan abu ya fara ja ba ya saboda tsoron abin da ka iya biyowa baya. To amma a batun wannan doka ta hukuncin kisa ga waɗannan barayin shanu da mutane, su masu wannan ayyukan ta’addanci ko a jikinsu, domin koda ba da wannan sanarwa sai da suka kai hari a garin Biya-Ki-Kwana da maƙwabtan garin. An kuma ce sun yi ɓarna. Wasu da ke cikin garin sun zargi jami’an tsaron da ke kusa da garin da gaza taɓuka komai har suka shiga daji. Wani harin da aka kai a makon jiya shi ne harin da za a ce an yi bata kashi tsakanin ɓarayin da jami’an tsaro.

Garin Batsarin Alhaji, kimanin kilomita ɗaya tsakaninsa da garin na Batsari an samu rahoton cewa maharan sun shigo garin ne bayan ƙarfe 8 na dare. Kamar yadda shaidu na ido suka ce, maharan sun kashe mutane biyu a cikin garin a yayin musayar wuta da suka yi da jami’an tsaron. Sannan kuma sun kora wasu daga cikin shanun da suka tattara kafin isowar su jami’an. Isowar jami’an tsaron ya kawowa ɓarayin cikas bisa ga abin da suka yi niyyar yi. An kuma bi ɓarayin har wajen garin duk da samun ’yar matsalar da motarsu ta samu na kafewa a cikin wani tafki. Daga baya an gano cewar an yi wa ɓarayin mummunar ɓarna, duk da dai babu wani rahoton kamu ko kisan wani daga kowane ɓangare amma jama’ar da abin ya shafa da maƙwaftansu sun yaba da irin rawar da jami’an tsaron suka taka.

A’isha Buhari ta ziyarci ’yan gudun hijira

Batun masu gudun hijira na daga cikin abubuwan da jama’a ke kallo a kan waɗannan hare-haren ta’addanci. Mafi yawan masu gudun hijrar mata ne da kananan yara, walau waɗanda suka rasa iyaye, mazaje ko dangi.

A makon jiya, Uwargidan Shugaban Kasa A’isha Buhari ta kawo ziyarar gani da ido gami da alhini tare da jajanta wa waɗanda wannan iftila’i na hare-haren Batsari ya shafa. Ta samu tarba tare da rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihaar Katsina kuma shugaban kwamitin tsaro da sasanci a tsakanin ɓarayin shanun da sauran al’ummar da abin ke shafa, Dokta Mustapha Muhammed Inwa, sun je gidan baƙi da ke bayan Babbar Asibitin Katsina. A wajen, uwargidan ta nuna damuwarta ƙwarai tare da tausaya wa ’yan gudun hijra.

Sama da mutane 20, 000 ne wannan bala’in ’yan ta’addan ya shafa, waɗanda ke neman mafaka ko matsugunni a wurare dabam-daban da ke cikin Jihar Katsina. Matan da abin ya shafa suna cikin wani hali tare da bukatar sake haɗuwa da danginsu, waɗanda ɓarayin shanun tare da yin garkuwa da mutane gami da yin kisan ba gaira suka tarwatsa. A ƙalla sama da ƙauyuka 28 abin ya shafa a cikin Karamar Hukumar Batsari kawai, a cikin lokacin da bai wuce wata ɗaya ba.

Uwargida A’isha Buharin ta kai ziyara a waɗannan sansanin ’yan gudun hijra da ke cikin garin Katsina da Batsari. Sai dai tayi kira ga masu gabatar da shirin nan na zuba jari don tallafa wa ci gaban al’umma na Gwamnatin Tarayya da su sanya waɗannan ’yan gudun hijra don samun tallafin da zai amfanar da su.

A ƙarshe ta bayar da gudunmuwar buhunan shinkafa da taliya da sauran kayan masarufi ga ’yan gudun hijira da ta kai wa ziyarar jaje da tausayawa a sansanonin da ke Katsina da Batsari. Ta kuma yi addu’ar Allah Ya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli, tare da ƙara yin kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa waɗannan bayin Allah.