Da Dumi Dumi

Yadda ’yan fashi suka sassari dan sanda a Abuja

Sufeto Janar Adamu Abubakar Muhammad
Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu

Wasu mutane da ake kyautata zaton ’yan fashi ne sun kashe wani bawan Allah sannan suka raunata wani sajan dan sanda a garin Gofidna da ke kan hanyar Zuba zuwa dei-Dei a Yankin Babban Birnin Tarayya.

Wani mazaunin yankin mai suna Kabiru Adamu ya ce lamarin ya faru ne da kusan karfe 2.30 na daren Laraba, lokacin da ’yan fashin, wadanda ke dauke da bindigogi da adduna, suka yi dirar mikiya a kan al’ummar garin.

Ya kara da cewa marigayin mai suna Hussaini Ibrahim ya yi yunkurin kalubalantar ’yan fashin ne bayan wani daga mazauna garin ya yi ihun neman agaji, inda daya daga cikin bata-garin ya harbe shi a ciki – nan take kuwa ya ce ga garinku nan.

Daga nan ne ’yan fashin, a cewar Kabiru Adamu, suka nufi gidan wani sajan dan sandan kwantar da tarzoma da ke zaune a yankin suka sassare shi da adda.

Ya kara da cewa ’yan fashin, wadanda suka kwashe fiye da sa’a guda suna cin karensu ba babbaka a yankin, sun kuma kai hare-hare gidajen wasu mutanen inda suka kwace kudi da sauran abubuwa masu daraja.

ADVERTISEMENT

Dagacin Gofidna Sumaila Tukura ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ’yan fashin sun yi garkuwa da mutanen yankin har tsawon sa’a daya.

Ya kuma ce saboda harbe-harben da ’yan fashin suka yi ne ya sa aka tashi janareton babban masallacin yankin.

“Hasken ne ya sa ’yan fashin suka tsorata suka suka tsere”, inji shi.

Dagacin ya kara da cewa an kama biyar daga cikin wadanda ake zargi a maboyarsu da ke wani sunkurun daji da ke kusa da garin, bayan da ’yan sintirin yankin suka bi sawun su.

Babban jami’in rundunar ’yan sanda na Zuba, CSP Alkali Lamido, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma tabbatar da kama mutum biyar da ake zargi da hannu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya