✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan gudun hijira suka zama manyan manoman wake a bana

‘Yan gudun hijira sun nuna bajintarsu ga noman wake a kasa   Wasu unguwanni a garin Auta-Balefi da ke Jihar Nasarawa da aka san su…

  • ‘Yan gudun hijira sun nuna bajintarsu ga noman wake a kasa

 

Wasu unguwanni a garin Auta-Balefi da ke Jihar Nasarawa da aka san su da noma bayan wasu shekaru garin ya zama birni inda aka yi watsi da noma a gonakinsu.

A garin Auta-Balefi ne ake da babbar kasuwar wake da ta bunkasa a harkar saya da sayarwar  wake, sai ga shi an yi nasarar samun gudunmawar ’yan gudun hijira wajen yin noma mai yawa sanadiyyar zamansu a yankin.

Unguwar dai tana kan hanyar Abuja zuwa Keffi a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa da nisan kilomita 12 zuwa birnin tarayya Abuja, kuma akwai sansanin ’yan gudun hijira da ke zaune garin daga Jihar Borno.

‘Yan gudun hijira lokacin da suke gyaran gona

Wakilinmu ya ziyarci unguwar kuma ya gana da wadansu ’yan gudun hijira da dama inda mafi yawansu daga Karamar Hukumar Gwoza ne, wadda take da nisan kilomita 84 a Kudu maso Gabas da Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Binciken wakilinmu ya gano cewa, kafin ’yan Boko Haram su tagayyara yankunan ’yan gudun hijirar a shekarar 2014, mazauna garin yawancinsu manoman wake ne da suke da gonakinsu a iyakokin Najeriya da kasar Chadi.

Amma rikicin yankin ya sa suka bar kauyukansu suka koma Abuja da zama, wadansu na zaune a sansanin wucin gadi wadansu kuma a gidajen da ba a kammala ba, wadansu a tashoshin motoci da sauransu.

Wadannan ’yan gudun hijira sun yanke shawarar ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba, don haka suka yanke shawarar neman gonakin da za su noma a wajen Abuja. Sun fara neman a ba su haya ko kuma kuma a ba su jinginar gonakin, duk da yake neman gonaki a Abuja haya yana da wahalar samu.

Wani daga cikin ’yan gudun hijira mai suna Mista Philemon Ayuba, ya dawo sansanin ’yan gudun hijirar ne a shekarar 2015, inda ya samu ’yan uwansa da suka yi hijira daga garin Gwoza da ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira a Jihar Nasarawa da kuma  birnin tarayya Abuja. Ya fahimci mafi yawan ’yan gudun hijirar na yi wa wasu ayyuka ne kawai ba tare da dogaro da kansu ba, wannan ya sa ya fara hada kan jama’ar da ke zaune a sansanin ta fara noman wake saboda tuntuni sana’arsu ke nan a  Gwoza kafin rikici ya addabi yankunansu.

Ayuba ya ce, a shirin da suke yi na inganta harkar noman wake, ya tuntubi sarakunan yankuna kamar: Etsu Karu da mai unguwar garin Auta-Balefi da shugabannin addinai kamar su Akibishop Onaiyekan, wadanda z asu iya taimaka masu su hada su da hukumomin da za su iya taimaka wa ’yan gudun hijirar wajen samar musu gona.

Sakamakon kokarin ’yan gudun hijirar wajen noman wake a kasuwar Auta-Balefi shekara uku da suka gabata, akwai akalla manyan motoci tirela 100 da ke fita da wake duk mako zuwa wasu yankunan kasar nan.

Waken da aka girbe

Ayuba ya ce, a yanzu a ninka adadin noman wake da ake kaiwa kasuwa. Da hadin gwiwar wadansu ’yan gudun hijira da suka kai sama da dubu 8 da suka bayar da gudunnmawar gonaki inda suka bude kasuwa tare da biyan harajin Naira dubu 150 ga Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa duk wata.

Kasuwar waken ta kasance daya daga cikin manyan kasuwannin wake a kasar nan inda take da masu saya daga jihohin Oyo da Enugu, kuma an samu ci gaba sosai ta hanyar janyo ra’ayin ‘yan kasuwa a duk yankunan kasar nan.

Wadansu daga cikin manoma ’yan gudun hijirar sun bayyana wa Aminiya jin dadinsu game da canjin rayuwa a yanzu ta yadda suka shiga cikin kuncin rayuwa a shekarun baya sanadiyyar rikicin da ya addabi Jihar Borno.

Daya daga cikin wadanda suka yi noman wake mai suna Bulus John ya bayyana wa Aminiya cewa, daya daga cikin matsalar da suke fuskanta ita ce, idan sun karbi hayar gona bayan sun girbe sun samu amfani mai yawa da kyau, sai masu gonakin su kara musu kudin hayar gonakin da ba a tsara tun farko ba.

Ya ce, sun yi girbe buhun wake 150 a bana amma bai yi murna karyewar farashin waken, don wannan ya shafi ribar da ake zaton samu a noman.

Bulus ya ce farashin magungunan kwari da takin zamani da kudin hayar gona duk ya lakume kudadensu, a karshen kadan zai rage musu.

Wani dan gudun hijirar mai suna Albert Peter mai shekara 29, ya ce, jama’a da dama daga kamfanoni ko manyan ’yan kasuwa na zuwa wurinsu su saya a farashi mai sauki.

Shekara biyu da suka gabata masu sayen wake na sayen buhu a kan Naira dubu 22 zuwa sama, amma yanzu an karya farashin ana saya a kan Naira dubu 7 na buhu mai nauyin kilo 50, idan aka kwatanta adadin kudaden da aka kashe a noman wake yanzu ba za a iya hadawa da na shekara biyu da suka gabata ba.

Wani daga cikin manoman waken mai suna Zakariya Luka, ya ce, ya girbe buhun wake 20, inda ya ce, idan har ya sayar a kan farashin da bai kai Naira dubu 22  a buhu ba, wannan zai sa jarinsa ya karye ko  kuma ya samu karamar riba yayin da zai sha wahala wajen biyan rancen da ya yi kafin ya girbe waken da ya shuka.

Wani manomi mai suna Andrew James mai shekara 33 ya yi hayar gona a kan Naira dubu 35 da biyan kudin taki da kudin maganin kwari da kuma biyan ’yan kwadago a karshe ya samu buhu 21, amma a yanzu haka abin da yake fargaba shi ne yadda farashin zai kasance a kasuwa, don haka akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin.

A lokacin da Ministan Gona, Cif Audu Ogbeh, ya ziyarci kasuwar inda ya ce, “Wannan ba karamin abin ban mamaki ba ne, maimakon a ce ’yan gudun hijira sun jira a kawo musu tallafin abinci daga wani wuri sai ga shi wani rukunin mutane daga Jihar Borno, sun hadu sun zama ’yan gudun hijirar da suka kirkiri masana’anta mai zaman kanta. Ministan ya ce, “Wannan ita ce babbara kasuwar da na taba gani a Najeriya wanda hakan ke nuna duk da kalubalen da wadansu suke fuskanta na rayuwa za su iya yi wa kansu abubuwa, muna alfahari da irin wadannan mutane.”