✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan kwana-kwana suka ceto mutum 132 a Kano

Mutum takwas sun mutu a jihar, inda rashin iya amfani da tukunyar gas ke haddasa gobara

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta ceto rayukan mutum 132 da dukiyoyin da darajar miliyan 16.5 a lokuta daban-daban da hadarin gobara ta ritsa da su a watan Oktoban 2020.

Wannan yana dauke ne cikin wani jawabi da kakakin hukumar, Saidu Muhammad ya sanyawa hannu a ranar Laraba.

Sai dai yace mutane takwas sun rasa rayukansu tare da asarar dukiya ta kimanin miliyan N8.6 a Jihar.

Ya kara da cewa hukumar ta kai dauki a wurare 86 da suka samu rahoto.

A cewarsa bincike ya nuna cewa ana samun yawaitar gobarar ne sakamakon rashin iya amfanin da tukunyar gas, da kuma kayan wutar lantarki.

Muhammad ya ja hankalin mutane dasu ke kokarin kiran hukumar tasu akan lokaci a duk lokacin da aka samu gobara a wani yanki na jihar.