✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘Yan Najeriya 188 suka sauka a Legas daga kasar Afirka ta Kudu

A daren jiya Laraba ne jirgin ‘Air peace’ ya sauka Legas da kashi na farko na ‘yan Najeriyan da suka bukaci su komo gida Najeriya…

A daren jiya Laraba ne jirgin ‘Air peace’ ya sauka Legas da kashi na farko na ‘yan Najeriyan da suka bukaci su komo gida Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu, mutum 188 da suka hadar da maza da mata da yara kanana sun samu kyakkyawan tarba daga mai taimakawa shugaba Buhari akan al’ummaran ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA da jami’an hukumar shige da fice ta kasa.

‘Yan Najeriyan sun isa filin sauka da tashin jirage na kasa na Murtala Muhammad cike da farin ciki da annushuwa inda suka yi ta rera taken kasar Najeriya tare da bayyana takaicin su da irin halin kuncin da suka sami kansu a kasar Afrika ta Kudu.

Codobasi dan asalin jihar Abiya daya ne daga cikin mutanen 188 ya shaidawa Aminiya cewa, ya yi matukar farin ciki ganin sa a gida Najeriya ya ce zuwa yanzu akwai tarin ‘yan Najeriya da sarkafe a kasar Afirka ta Kudu, ya ce akwai wanda basa so su dawo ko a halin kaka, “Ni karatu ya kai ni kasar Afirka ta Kudu inda na shafe sama da shekaru 7, kuma ni malamin coci ne, nayi farin cikin dawo wa ta, Allah ya sakawa wadanda suka yi ruwa da tsaki a dawowar mu.” In ji shi.

Ka zalika Temilabi, wacce ta dawo dauke da ‘yarta ta shaidawa Aminiya cewa, ta tafi kasar Afirka ta Kudu ne bitar aikin yi a lokacin da ta kammala karatun ta a Jami’ar jihar Legas, ta ce idan gwamnati ta samawa matasa ayyukan yi za a samu saukin ‘yan kasar nan da ke fita kasashen ketare neman aiki.

‘Yan Najeriya sun shaidawa ‘yan jaridu cewa da yawan su sun sauka Najeriya babu komai a tare da su, inda su kace akwai da dama daga cikin su da suka bar tarin dukiyoyin su a can suka komo ba ko kwabo, haka zalika akwai ‘yan Najeriyan da baza su dawo ba saboda baza su iya barin abubuwan da suka mallaka ba. A daya bangaren gwamnatin Najeriya gwamnatin Najeriya ta sha alwashin kyautata rayuwar ‘yan Najeriyan da suka bukaci komowa gida daga kasar ta Afirka ta Kudu, Idris Abubakar Muhammad babban jami’i ne na hukumar bada again gaggawa ta NEMA wanda ya jagoranci jami’an hukumar wajen karbar mutanen 188 ya shaidawa Aminiya cewa, hukumar ta shirya tsaf domin basu kulawa, ya ce sun tanadi kayayyakin abinci, magunguna da dai sauran su, “Bayan jami’an shige da fice ta kasa sun tantance su kamar yadda kake gani ana yi a yanzu zamu basu wannan tallafi mu kuma sanya su a motocin da zasu karasa da su jihohin su sannan mu basu dan abin hasafi kafin daga bisani mu mukai su wajen mahukunta a mataki na jihohin suma su daura akan tallafin da gwamnatin tarayya tayi.” In ji shi.

‘Yan Najeriya da aka dawo da su daga kasar Afirka ta Kudu

A nata bangaren mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta bada tabbacin basu kulawa ta musamman ta ce, ko wannan su za a ba shi layin wayar salula na MTN da kudin kira a ciki Naira dubu 40 wanda za suyi amfani da su cikin wata 2 ” mun baku wannan ne domin in kun je gidajen ku kun huta ku sami hasafin kiran ‘yan uwa da abokan arziki ku yi zumunci, kana akwai kamfanunuwa da muka gayyato wadanda za su tallafa maku ku kama sana’a ko kasuwanci.” In ji ta. Ta ce gwamnatin Najeriya zata basu dan abin hasafi domin su ta da komada Haka zalika shugaban kamfanin jiragen sama na ‘Air Peace’ Mista Allen Onyema, ya shaida cewa sun yi jigilar mutanen 188 daga kasar Afirka ta Kudu zuwa Najeriya a jirgin ‘Air Peace’ ba tare da karban ko kwabo ba, ya ce sun ga ya dace su taimaka masu su kuma bada irin tasu gudunmawar a matsayin su na ‘yan kasa masu son ci gaban kasa da al’ummar ta, ya ce abin da ya burge shi shi ne ganin yadda mutanen ke ta rera taken kasar nan a lokacin da suka sauka Najeriya, “Wannan shi zai tabbatar maku cewa mutane ne masu son kasar mu Najeriya ba ‘yan tawatse bane, a shir ya nake mu ci gaba da kwaso su, duk wanda yake bukatar komowa mun shirya dauko su, ko da mutum guda ne ya rage mu a shirye muke mu dau jirgi muje mu dauko shi, jira kawai muke mu sami izini daga gwamnatin tarayya.” In ji shi.  Dubun dubatar ‘yan uwa da abokan arzukan mutanen 188 suka hallara domin karbar su wadanda yawancin su suka yi ta zaman dirshen tun daga safiyar Laraba har zuwa daren a lokacin da ‘yan uwan nasu suka sauka birnin Legas daga kasar Afirka ta Kudu.

‘Yan Najeriya da suka dawo tare da Wakilinmu Abbas Dalibi da ziyarci filin jirgin saman na Legas