✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan sanda suka azabtar da dana har ya mutu – Madobi

Yanzu haka ’yan uwan marigayi Abdulkadir Nasir dan kimanin shekara 26, suna ci gaba da alhini da kokawa game da halin da suka tsinci kansu…

Yanzu haka ’yan uwan marigayi Abdulkadir Nasir dan kimanin shekara 26, suna ci gaba da alhini da kokawa game da halin da suka tsinci kansu na rashin tabbacin samun adalci wajen bin hakkin kashe dansu da suke zargin ’yan sanda da aikatawa a Jihar Kano, lokacin da suke tuhumarsa da sa hannu a wani fadan ’yan daba da aka yi a garin Madobi.

Mahaifin marigayin Malam Nasiru Abdulkadir Madobi, ya shaida wa Aminiya cewa da kansa ya dauki dansa ya kai wa ’yan sanda don bincike amma maimakon su yaba masa sai suka kama azabtar da dan nasa a gabansa.

“Lokacin da wani dan sanda mai suna Haruna ya zo gidana, marigayin ba ya nan. A nan muka yi yarjejeniya cewa da zarar ya dawo zan kawo musu shi. Bayan sun tafi, na kira dana a waya na nemi ya zo gida. Bayan ya dawo zai sha shayi ke nan sai na nemi mu tafi ofishin ’yan sanda, inda na dauke shi na kai shi wurinsu da kaina,” inji shi.

Ya kara da cewa:  “Da muka je sai na ga yaron da ya yi kararsa, dan abokina ne wanda daga baya ma ya yi da-na-sanin faruwar lamarin gaba daya.”

Aminiya ta gano cewa a lokacin da ’yan sandan ke tuhumar marigayin ne ’yar takaddama ta kaure a tsakaninsu, inda suka rika jifar juna da munanan kalamai, lamarin da ya harzuka ’yan sandan suka yi wa marigayin dukan kawo wuka; wanda ya janyo ya ce ga garinku nan.

“Lokacin da suka fara bincika masa jiki sai ya ce shi ba ya da kudi sai Naira 50 kawai don haka ba sai an bincike shi ba. Shi ke nan sai suka fara maganganu a tsakninsu, sai wani dan sanda a cikinsu mai suna Danbichi ya mare shi, shi ma ya rama. Sai sauran ’yan sandan da suka hada da Takalmin Zomo, Haruna da Mustapha suka rika dukansa har sai da ya galabaita, sannan suka fesa masa tiyagas,” inji mahaifin.

Ya ce ganin ba zai iya jure ganin dukan da ake yi wa dansa ba,  kuma ba zai iya tserar da shi ba, ya sanya ya bar ofishin ’yan sandan yana hawaye.

Dan uwan marigayin, Malam Ahmad Nasir, ya bayyana wa Aminiya cewa a gabansa ya ga wani dan sanda yana dukan dan uwan nasa da itace. “Lokacin da na je ofishin ’yan sandan, mahaifinmu ya tafi gida. A nan na shiga ciki bayan na gaishe da ’yan sanda sai na nemi su kyale shi ganin irin dukan da suke yi masa, domin a gabana Saje Shehu Saleh ya dauki itace yana dukansa. Da na ga abin ya yi yawa har nake gaya masa cewa idan fa ya mutu shi za a kama amma haka suka ci gaba da dukansa har sai da suka galabaitar da shi. Hakan ya sa aka kwashe shi zuwa Asibitin Madobi, inda likitocin asibitin suka ce abin ya fi karfinsu. Don haka suka yi umarnin a mayar da shi zuwa Asibitin Kwararu na Murtala,” inji shi.

Ahmad ya ce sai da aka kai ruwa rana tare da bayar da Naira dubu takwas kafin DPO na Madobi ya bayar da iznin daukar marigayin zuwa asibiti. “Daga nan ne na tafi Kano wurin kanwata da mijinta, inda suka nemo wani Sajan ’yan sanda da ke aiki a Bompai, muka taho tare zuwa Madobi don rokon DPO; inda ya ce wai wani Sabi’u ne maganar ke hannunsa, don haka shi zai yanke abin da za a yi. Daga nan muka je wurin Sabi’u wanda ya ce in ba su wuri, zai yi magana da abokin aikinsa. Bayan na fito sai ga Sabi’u ya biyo ni ya ce wai na dauko dan sanda na zo da shi kuma shi ba zai yi maganar kudi a gabansa ba. Don haka sai in ba su Naira dubu 20, wai za su kai wa DPO a matsayin toshiyar baki. A lokacin ba ni da kudi, ga shi kuma zan kai marigayin asibiti amma ba su gaya min cewa sun riga sun kai shi asibiti ba. Sai suka dage lallai sai na ba su wannan kudin sun kai wa DPO. A nan na gaya musu cewa Naira dubu 10 gare ni, wanda kuma haka dai ba yadda zan yi na dauki Naira dubu takwas na ba dan sanda Sabi’u ya tafi ofishin DPO. Ban dai san me ya faru tsakaninsa da DPO ba. A nan ne ya gaya min cewa ai marigayin yana Asibitin Akilu na Madobi. Don haka muka je can muka same shi rai kwakwai-mutu kwakwa,” inji shi.

Ya ce lokacin da ya ga halin da dan uwansa yake ciki, da farko ya ki daukarsa zuwa asibitin Murtala. “Da farko na yi niyyar ba zan kai shi asibiti ba, ganin cewa ’yan sandan da kansu suka kawo shi suka yar da shi a asibitin, amma sai Saje Bashir ya nuna min cewa ya riga ya sa hannu ya karbi yaron daga ’yan sandan Madobi sannan a gefe daya ya nuna min muhimmancin ceton ran yaron, inda ya yi alkawarin sanar da Kwamishinan ’Yan sanda yadda abubuwa suka kasance. Hakan ya sa muka dauko shi zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda aka ce za a yi masa hoto. Sai dai bayan mun gama biyan kudin, ba a kai ga yin hoton ba yaron ya ce ga garinku nan,” inji shi.

Malam Ahmad ya kara da cewa lokacin da suka nemi asibitin su ba su takardar dalilin rasuwar dan uwan nasu, sun ce ’yan sanda ne kadai za su iya karbar wannan rahoto idan sun nema.

A cewar Malam Ahmad, duk da cewa bayan rasuwar dan uwansu Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya aike da wakilansa don yi musu ta’aziyya tare da alkawarin daukar matakin da ya dace kan al’amarin amma zuwa yanzu sun yanke tsammanin samun adalci, ganin yadda al’amarin yake tafiyar hawainiya.

“Lokacin da aka gayyace mu don mu ba da bahasin abin da ya faru sai Sabi’u yake tambayata wai ko na san yaron yana da shaidanun aljanu? In da na ce ba mu taba sanin haka ba a iya tsawon rayuwarsa. To tun daga wannan lokaci na yanke kaunar samun adalci a kan maganar. Haka kuma a wata ranar Litinin, a wani shiri da ake yi a gidan rediyon Pyramid FM, na ji Kakakin Rundunar ’Yan sandan Kano yana cewa wai an sallami yaron daga asibiti kafin ya rasu daga bisani.

“Haka a lokacin da ake maganar na fahimci yadda DPO din Gwale, Mannir wanda ya zama kamar shi ne alkali, yake gaya wa Sabi’u tambayoyin da zai yi mini. Lokacin da na nuna rashin amincewata sai ya ce ai aikinsu ne, ni kuma tunda ba dan sanda ba ne sai na yi shiru da bakin,” inji shi.

Dagacin Madobi, Alhaji Umar Muhammad ya bayyana cewa tun kafin faruwar lamarin, al’ummar garin sun yi ta kokawa game da yadda ’yan sandan da ke Madobi suke cin mutuncinsu tare da karbar kudi a hannunsu a kan kananan laifuffukan da suke zargi. Ya ce, DPO din ba ya da kyakkyawar mu’amala da mutanen yankin.

Ya yi kira ga hukumomi da suke fadi a ji su tsaya wajen ganin an yi adalci a cikin lamarin, don ya zama darasi ga na baya.

Barista Abba Hikima Fagge, daya daga cikin lauyoyi masu kare marasa galihu wadanda suka dauki niyyar ganin an bi hakkin marigayin, ya ce babu inda aka ba dan sanda dama ya doki farar hula ko da kuwa ana zarginsa da aikata wani laifi. “Akwai sashe na 34 a Kundin Tsarin Mulkin Kasa, wanda ya hana dukan mutum don kawai ana zarginsa da wani laifi. Saboda sunansa wanda ake zargi bai zama mai laifi ba har sai ainihin shari’a ta tabbatar masa laifi. Mafi yawan lokuta ana gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu amma daga bisani bincike ya wanke su. To, ka ga idan ka taba lafiyarsa kuma aka wanke shi, ka zalunce shi. Haka kuma akwai dokar da ta hana azabtar da mutum, wacce kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ta, kuma Najeriya ta sanya hannu a kanta cewa jami’anta masu sanya kayan sarki ba za su taba lafiyar kowa ba. Don haka kisan da aka yi wa Abba abu ne marar dadi wanda kuma ya zama tilas mu sa ido don ganin an gurfanar da wadanda ke da hannu a cikin aikata sh,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni rundunar tasu ta kama jami’anta biyar da ke bakin aiki a lokacin da lamarin ya auku. “A yanzu haka jami’anmu da ake zargi su biyar suna tsare, kuma an fara fadada bincike a kansu. Da zarar an gama bincike idan an same su da laifi za a gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.