✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan sanda suka kama ‘yan ta’adda 46 a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta yi nasarar damke masu fashi da kisa da satar mutane domin karbar kudin fansa 46 tare da hallaka…

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta yi nasarar damke masu fashi da kisa da satar mutane domin karbar kudin fansa 46 tare da hallaka wasu 10 a jihar Zamfara.

Babban sufetan ‘yan sandan Muhammad Adamu, ya ce a yayin aikin raba jihar da makwabtanta da ‘yan taddar da suka fara a makon jiya, mai lakabin Operation Puff Adder, sun kuma yi nasarar kubutar da wasu mutane biyu da aka sace.

Shugaban ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ya yi da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi ranar Alhamis, a Abuja.

Sai dai kuma yayin da babban sufetan ‘yan sandan ke bayyana wannan nasara da ya ce sun yi a jihar ta Zamfara, wasu mazauna kauyukan Maikuru da Masha-awo na yankin Birnin-magaji na jihar sun ce ‘yan bindiga sun afka wa kauyukan biyu inda suka kashe akalla mutane 32 tare da yin ta’adi mai yawa a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

Wani dan garin na Maikuru ya shaida wa BBC cewa da rana kirikiri barayin suka yo gayya suka kawo musu hari, inda suka karkashe jama’a, suka kona babura, washegari kuma ana shirin jana’iza suka dawo suka hana daukar gawawwaki.

Mutumin ya ce, ‘yan ta’addar ba su bari ba a yi suturar gawawwakin har sai da Uban kasar ya kware hularsa ya roke su arziki sannan suka bari.

Bayanai dai sun nuna a yanzu haka kusan babu kowa a garin saboda barayin sun sake komawa inda suka rika kwashe kayan amfanin gona da dabbobin jama’a, daga bisani suka cinna wuta a gidaje.

Daman dai an ce ‘yan ta’addar sun mamaye wannan yanki kusan gaba daya, kamar garuruwan Mai-jan-ido da Hayin-bajimi da Samawa da makamantansu.

Mazaunin yankin ya sheda wa BBC cewa, babu wata hukuma ko dan sanda ko sarkin gargaji ko kotu da ke aiki a wurin.

Ya kara da cewa ko ta kotu aka kai dan wannan yanki, ba zai je ba kuma babu wani abu da za a iya yi masa.

Mutumin ya ce a duk wannan hali da suka shiga babu wani jam’in tsaro da ya je wurin, sannan kuma a yanzu ma ‘yan ta’addar sun lashi takobin cewa bana babu wanda zai yi noma a yankin.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara kan wannan hali da al’ummar yankin na karamar hukumar Birnin-magaji suke ciki, amma kakakin rundunar ya ce zai yi bincike tukuna, kafin ya yi magana.