✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘Yan sanda suka kubutar da mutum 3 da aka yi garkuwa da su ranar Sallah

Wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a yankin ruwa na Ijebu da ke jihar Ogun sun sami kubuta bayan da rundunar ‘yan…

Wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a yankin ruwa na Ijebu da ke jihar Ogun sun sami kubuta bayan da rundunar ‘yan sandan jihar ta yi wa tsaunukan yankin kawanya da jirgi mai saukar ungulu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa, an yi garkuwa da mutanen uku wadanda suka hadar da Adamson Bamidele sai Adam Jelili da Sanni Azeez, ya ce an yi garkuwa da su ne a ranar Babbar Sallah da ta gabata, ” jami’an mu karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Bashir Makama, sun yi nasarar kubutar dasu ba tare da an masu ko kwarzane ba, domin an yi wa yankin da aka yi garkuwa da zu kawanya ne bayan da masu garkuwa suka ji tsanani sai suka sake su” in ji shi.

Ya ce, rundunar ta yi nasarar kame mutum guda da ake zargi da hannu a yin garkuwar kuma tuni aka hada wadanda aka kubutar da iyalan su.