✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda ’yan sanda suka tsare mu da ’yata da aka sace bayan bayyanarta’

Mahaifiyar budurwar da aka sace a garin Dakwa, Abuja, Malama Binta Lawal ta zargi ’yan sanda da ci gaba da tsare ’yarta mai shekara 17…

Mahaifiyar budurwar da aka sace a garin Dakwa, Abuja, Malama Binta Lawal ta zargi ’yan sanda da ci gaba da tsare ’yarta mai shekara 17 mai suna Lauratu Lawal bisa umarnin wanda suke zargi da sace yarinyar mai suna Jibrin Abubakar.

Da take bayani kan yadda yarinyar ta bayyana, Malama Binta ta ce ’yarsu wadda suka rabu da gani tun a ranar 1 ga Janairu bayan Jibrin, ya ce ta raka shi waje, sun samu labarin ganinta a garin Asaba a Jihar Delta.

Ta ce wadansu Hausawa da ke wurin suka ganta tana gararamba a kan titi inda suka kai ta wani gida, bayan hayyacinta ya dawo aka tambaye ta ko akwai lambar da ta rike. “A nan ne ta ba su lambar wani dan uwana da ke Kaduna, kuma nan take ya sanar da mu. An hada ta da wani direba ya taho da ita zuwa garin Zuba inda ya sauke ta a mota bayan magaribar ranar Talatar makon jiya, ya wuce Kano.

“Mun yi ta waya da shi lokacin da suke tahowa, sai dai da suka iso Allah bai ba mu damar haduwa da shi ba, sai muka wuce zuwa ofishin ’yan sanda na SARS tare da mijina inda maganar take don sanar da su lamarin. To ana cikin haka sai ga ta, ta taka har zuwa gida Dakwa daga Zuba, aka sanar da mu ta waya, ’yan sandan SARS sun je gida sun dauko ta zuwa wajensu.

“Ba mu iya komawa gida ba lokacin saboda dare ya yi nisa, sai muka kwana a ofishin da nufin komawa da safe, sai dai da gari ya waye sai suka ki bari mu dawo, suka ce za su ci gaba da tsare mu tare bayan sun yi zargin cewa sharri muka yi wa Jibrin, ba shi ne ya dauke ta ba,” inji ta.

Malama Binta ta ce bayan kwana uku suna tsare tare da ’yar, ’yan sanda sun sako ta a ranar Asabar tare da mahaifin yarinyar.

“Sai dai sun ce ba za su saki Lauratu ba har sai Jibrin ya janye maganar,” inji ta.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito bacewar yarinyar a baya inda mahaifiyarta ta yi zargin cewa Jibrin wanda surukinta ne ya zo unguwarsu da ke garin Dakwa ya kira yarinyar ta waya, kuma tun daga lokacin ba ta sake dawowa ba.

Ta ce a dalilin haka sun shigar da kara a ofishin ’yan sanda da ke garin, inda aka kama wanda ake zargin kafin daga bisani babban ofishin ’yan sanda na Zuba ya karbi binciken kuma ya mika wanda ake zargin ga Sashin Binciken Manyan Laifuffuka (CID) na Rundunar  da ke  Abuja.

Sai dai ana cikin haka ne, sai sashin dauki da leken asiri da ke hedkwatar ’yan sandan Najeriya (IRS) ya karbi binciken bayan wanda ake zargin ya shigar da nasa korafi ta wajensu, kamar yadda wata majiyar ’yan sanda ta bayyana.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya  Frank Mba, ya ce bai da masaniya a kai, amma ya ce zai binciki lamarin ya sake waiwayar wakilinmu, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi wani bayani ba.