Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yadda ’yan wasan kwallon Najeriya mata suke baje kolinsu a duniya

Asisat Oshoala a tsakiya
Asisat Oshoala a tsakiya

Kasancewar an fi kula da ’yan wasan kwallon kafa maza a Najeriya, hakan ya sa ake watsi da ’yan wasa mata wadanda suke kokari sosai a duniyar kwallon kafa yanzu. A yanzu kusan za a iya cewa matan Najeriya sun fi maza fice domin kuwa akwai wadanda suke manyan kungiyoyi kamar Barcelona da Atletico Madrid da kuma wadda ta lashe kyautar wadda ta fi zuwa kwallo a gasar Firimiya ta China, sannan da wadanda suka lashe gasar gwarzayen ’yan kwallon Afirka sau hudu da wadda ta lashe sau uku da sauransu. Sannan uwa-uba shi ne yadda ya kasance yawancinsu ba zaman benci suke yi ba a kungiyoyin da suke wasa kamar yadda da yawa daga cikin ’yan wasa maza suke yi. Wannan dalilin ne ya sa Aminiya ta rairayo wadansu daga cikinsu da kuma yadda suke wakiltar kasar a duniyar kwallo.

 

ADVERTISEMENT
  1. Asisat Oshoala: FC Barcelona

Asisat Oshoal ’yar wasa ce da ke taka leda a kungiyar FC Barcelona ta kasar Spain a matsayin ’yar wasan gaba. A kakar bara ta buga wa kungiyar Dalian Kuanjian F.C. da ke kasar China, inda ta kasance wadda ta fi zura kwallaye a gasar baki daya.

Asisat, mai shekara 24 ta buga wa kungiyoyin Liverpool Ladies, inda a lokacin kocinsu Matt Beard ya kwatanta da daya daga cikin matasan ’yan wasan duniya masu tasowa a kwallon kafa, sannan ta buga kungiyar Arsenal Ladies.

ADVERTISEMENT

Asisat ta lashe kyautar gwarzuwar ’yar wasan Afirka sau uku a shekarun 2014 da 2016 da 2017, sannan bara ta zo ta biyu.

Asisat wadda ake wa lakabi Sedorf ko Superzee tana lambar kasa ta MON.

 

  1. Francisca Ordega: Atletico Madrid

Franciska Ordega wadda ake yi wa lakabi da Franny ’yar wasan gaba ce da ke kungiyar Atletico Madrid a kasar Spain a matsayin aro daga kungiyar Washington Spirit.

Ordega mai shekara 25 a duniya ta buga wa kungiyoyin Rossiyaka ta kasar Rasha da Pitea IF ta kasar Sweden da Washington Spirit da Sydney FC ta kasar Austreliya, inda ta fice wajen zura kwallaye.

 

  1. Tochukwu Oluehi: Medkila IL

Ga duk wanda ya kalli gasar cin Kofin Nahiyar Afirka ta mata da aka kammala kwanakin baya, wanda Najeriya ta lashe bayan ta lallasa  Afirka ta Kudu a bugun karshe da  yadda ta doke Kamaru a bugun kusa da karshe, da ya ji sunan Tochukwu, babu abin da zai tuna sai yadda ta rika kama bugun daga kai sai gola. Tochukwu yanzu haka ita ce golar kungiyar Medkila IL da ke kasar Norway.

 

  1. Rashidat Ajibade: Abaldsnes IL

Rashidat Ajibade ’yar shekara 19 matashiyar ’yar wasan Najeriya ce da ke kungiyar Abaldnes IL ta kasar Norway. Ta fara wasa ne tun daga ’yan wasan kasa da shekara 17 da 20 kafin ta samu shiga cikin manyan ’yan wasa na kasar nan.

Rashidat ’yar wasar gaba ce wadda a kakar shekarar 2017, Rashidat ce tare da Reuben Charity suka fi zura kwallaye.

 

  1. Onome Ebi: FC Minsk

Oneme tana daya daga cikin manya kuma tsofaffin ’yan wasan Najeriya wadanda har yanzu ake damawa da su. Yanzu haka tana kungiyar FC Minsk ta kasar Belarus.

Oneme mai shekara 35 wadda ’yar wasan baya ce, ta buga wa kungiyoyin Pitea IF  da Djurgarden duk a Sweden. Sai kungiyar Atasehir Belediyespor da Dubenciler Lisesispor na Turkiyya. Daga bisani ta sake komawa Sunana SK a Sweden kafin ta tafi Minsk a Belarus.

 

  1. Desire Oparanozie: Guingamp

Desire Oparanozie tana cikin ’yan wasan gaba da Najeriya ke alfahari da su. Yanzu haka tana kungiyar Guingamp da ke kasar Faransa.

’yar wasan mai shekara 25 ta buga wa kungiyoyin Dubenciler Lisesispor ta Turkiyya da Rossiyanka a Rasha da Wolfsburg a Jamus da Atasehir Belediyespor a Turkiyya.

Sauran sun hada da Ngozi Ebere  da ke kungiyar Arna-Bjornar ta Norway da Osinachi Ohale da ke taka leda a kungiyar Badjo DFF da ke Sweden. Sai kuma Josephine Chukwunonye  da ke kungiyar Asarum AIF a Sweden da Halimat Ayinde ta kungiyar Asarum AIF a Sweden da sauransu.