✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a ceto matsa daga shaye-shaye

Tasirin shan kwaya a tsakanin matasan kasar nan ya dade da zamowa sanadin lalacewar tarbiyya da haifar da bara-gurbi a cikin al’umma. Wannan wani mummunan…

Tasirin shan kwaya a tsakanin matasan kasar nan ya dade da zamowa sanadin lalacewar tarbiyya da haifar da bara-gurbi a cikin al’umma. Wannan wani mummunan al’amari ne da sai an tashi tsaye, an hada hannu wajen gyara tarbiyya da dawowa da martabar al’umma. Ba zai yiwu a nade kafa, a zauna ana ganin munanan dabi’un shaye-shaye na yi wa jama’a mummunar illa ba.

Me ake nufi da shaye-shaye? Shaye-shaye shi ne mutum ya yi gaban kansa wurin shan kwayoyi, ko kuma duk wani nau’in abu mai bugarwa, iya yawan da yake so, a lokacin da ya ga dama, ko kuma cikakken dogaro a kan kwaya da aiki da ita sabanin dacewa, ba tare da izini daga likita ba. Da yawa daga matasan Nijeriya sun fada yin shaye-shaye, wadansu da saninsu, da yawa kuma bisa jahilci.

Abubuwa da dama ne kan haifar da shaye-shaye, wadanda suka hada da abokan banza da rashin tarbiyya daga gida da cushewar al’amuran rayuwa da jahilci da rashin aikin yi da sauransu. Misali shi ne, kwayoyi da magunguna masu hadari irin su, Hodar Iblis da tabar wiwi da kwayoyin Ephedrine da Morphine da sauransu su ne suka fi illa. Sannan ga abin da matasa suka dauki shansa yayi ko wayewa, shi ne shan kwalaben maganin tari mai dauke da sinadarin Codeine, irin su Benylin, Tutolin, Parkalyn, Emzolyn da Cofmid da sauransu, wadanda suke matukar tasiri wajen lalata kwakwalwar mai shansu. Shi ya sa idan mutum ya sha take tunaninsa zai jirkice, saboda ba sa bin ka’idar shan maganin, shanye shi suke take. Sai su rika ganin sun fi kowa a duniya, ko kuma su rika jin rayuwarsu ba ta da amfani kowa ya fi su galihu a duniya, wadansu kuma na yin shaye-shayen ne, domin su aikata wani abin da ba zai yiwu su aikata suna cikin hankalinsu ba.

Matsalolin da shaye-shaye ke haifarwa sun hada da tayar da zaune-tsaye da wargaza zamantakewa da rashin tabbas din rayuwa. Sannan wasu na samun sanadin shaye-shaye daga irin yadda suka samu tarbiyya tun daga gidajensu, sakamakon matsalolin yau da al’umma ke fama da su irin yawan mutuwar aure da tsananin talauci da munanan al’adu da rashin sanya idon iyaye a kan ’ya’yansu. Uwa uba idan mahaifi ko mai kula da yaran mashayi ne, shi ke nan yaro ya koya tun daga gida.

Wadansu iyayen kuma a kokarinsu na neman abin duniya da zafin nema, sai su nuna halin ko-in-kula, sai su bar tarbiyyar ’ya’yansu a hannun wadansu mutane daban, kamar ’yar aikin gida ko a kai yaro wurin ubangida, ko ma dai a bar yaro ya yi rayuwarsa shi kadai. Wadansu lokutan wannan dabi’ar na dakusar da tunanin yaro, ta jirkita ta matuka, sai a wayi gari yaro ya koyi shaye-shaye don ba ya kusa da iyayensa ko wani mai tsawatar masa, ballantana ya samu kula da soyayyar da zai fahimci shi ma yana da muhimmanci a kashin kansa.

Wadansu matasan kuma daga makarantu suke fara shaye-shaye, inda suke farawa da shan gahawa (Coffee) ko kwayar Taramol don su hana kansu barci, wai don su samu damar yin karatu sosai, alhalin ci gaba da aikata hakan na tsawon wani lokaci kan sa mutum kan wayi gari ya zamo mai shaye-shaye. Hukumomi irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) da sauransu, sun haramta mu’amala da magunguna da dama saboda illarsu ga al’umma saboda illarsu. Sakamakon da ake samu kan yawan mashaya a cikin al’umma su ne, rikice-rikice marasa tushe a tsakanin matasa da yawaitar masu tabin hankali da yaduwar sace-sace da fashi da makami da rashin ladabi da zaman banza da fyade da sauransu. Duk mai zurfin tunani zai ce wai mene ne sanadin wannan lalacewar ce? Iyaye su ne suke da babbar rawar da za su taka wurin gyaran tarbiyyar matasa wadanda su ne manyan gobe.

Za a rage kaifin wannan masifar ta shaye-shaye ta hanyoyi kamar haka, tun a gida iyaye su rika  nuna wa ’ya’yansu illolin shaye-shaye ga lafiyarsu da al’umma baki daya, saboda tarbiyya tana farawa ce daga gida. Sannan a sanya darasi mai zaman kansa game da shaye-shaye a cikin manhajar karantarwa na dukan makarantunmu, tun daga matakin farko har zuwa jami’a, sannan a rika shirya tarurruka da wasannin kwaikwayo domin bayyana illolin shaye-shaye.

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kara fito da sababbin dabaru na zamani wurin yaki da shaye-shaye a cikin al’umma. Dukan matakan gwamnati su tashi tsaye wurin maganin wannan al’amari, ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa da wayar da kan al’umma da ilimantar da su, domin tserar da al’umma daga rushewa da dawo da martabar matasanmu, domin su taimaka wurin hadin kan kasar nan da kuma bunkasarta.

Ibraheem El-Tafseer, Potiskum 08054362811