✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da gashi

Gashi yana daga siffofin da ke kara fito da kyan mace, don haka kula da shi ya zama wajibi. Kusan kowace mace tana mafarkin ta…

Gashi yana daga siffofin da ke kara fito da kyan mace, don haka kula da shi ya zama wajibi. Kusan kowace mace tana mafarkin ta ga gashinta yana kara yawa tare da santsi da kuma sheki, sai dai hakan ba ko yaushe yake samuwa ba saboda rashin bin ka’idojin gyara ko kula da gashi. Ya kamata mata su fahimci cewa kula da gashi abu ne da ake yi akowa ne lokaci sai dai ana so a kara mayar da hanali wajen kula da gashi musamman a lokacin sanyi ko hunturu.

Ga wasu hanyoyi da ya kamata mata su bi wajen kula da gashinsu:-

  • A duk lokacin da aka tashi wanke gashi ya kamata a fara shafa mai a gashin tun daga fatar kai har zuwa jikin gashin. Sai a bar shi tsawon awa daya sannan a wanke gashin da sabulun wankin gashi (Shampoo).
  • Amfani da ruwan dumi: A guji wanke gashi da ruwan zafi sosai don yana busar da gashi sosai. Ruwan dumi ko ruwan sanyi ya fi domin shi zai bar maikon man da aka shafa a gashin
  • A sirka sabulun wankin gashi: Yana da kyau a sami kofi a zuba ruwan sabulun wankin gashin tare da zuba ruwa don rage masa karfi. Idan aka zuba sabulun ba tare da sirkawa ba yana sa gashi ya bushe kwarai.
  • Idan an zo wanke gashi a guji cuccuda gashin cikin gaggawa, a maimakon haka a wanke shi a natse a hankali.
  • A wanke gashi da kondishna. Idan za a sabulun kwandisna a shafa shi a karshen gashi amma kada ya tabo fatar kai, idan ya yi kamar minti biyu sai a wanke gashin.
  • A guji wanke gashi a kullum, Idan kina tunanin wanke kai kullum tsafta ne, to zai haifar miki da bushewar gashi wanda zai iya kai wa ga karairayewar gashi.
  • A tsane gashi da tawul mai kyau. Sannan a bar shi a bude iska ta busar da shi.
  • A taje gashi da mataji mai kyau mai girma a daidai lokacin da gashin bai gama bushewa gaba daya ba.
  • A shafa man gashi sosai yadda gashin zai yi maiko.
  • A rika rufe gashin musamman idan za a fita waje don kare shi daga rana da kuma kura.
  • A rika yawaita yin kitso don guje yawan taje shi idan yana tsefe.