✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da gashin kai lokacin sanyi

Assalamu alaikum matan gidan nan, tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a…

Assalamu alaikum matan gidan nan, tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a lokacin sanyi. Gashin kawunanmu na bukatar kulawa sosai saboda gashin mace na cikin abin da ke kara mata kyau. Akwai abubuwa da dama da suka kamata ki yi amfani da su kamar su; man zaitun da zuma da man ‘castor’ da ruwan lemun tsami da man kwakwa. Wadannan nau’o’in mai suna da inganci sosai musamman wajen kare gashi daga tsinkewa da kuma sa shi karfi da santsi da sheki.

Man Kasto (castor oil)

Man Kastor (castor oil) na taimakawa wajen gyara gashin kai a hunturu. A debo man kastor kamar cokali uku, sai ki shafa a fatar kai sannan a taje a hankali. A turara tawul har sai ya yi zafi, sannan a daura tawul din a kai na tsawon minti 15, bayan haka, sai a yi wanka. Yana hana gashi tsinkewa a lokacin hunturu.

Man Zaitun da  zuma

A  hada cokali uku na man Zaitun da cokali daya na zuma a kwaba sai a gauraya su sosai, sannan a shafa hadin a kan fatar kai. Bayan mintuna kadan, sai a wanke da ruwa da sabulun wanke gashi.

Kwai ‘Binegar’ da man kwakwa

A kada kwai guda, sai a sa man kwakwa cokali biyu da ‘binegar,’. a hada waje daya, sai a kwaba su. A sa hadin a fatar kai sannan a taje gashin. A bar hadin ya jima tsawon minti 15, sai a wanke da ruwan dumi.

Lemun tsami da man kwakwa

A  hada cokali biyu na man kwakwa da cokali daya na ruwan lemun tsami. Sai a gauraya hadin ya gaurayu  sosai. Sannan a shafa a kan fatar kai. Wannan hadi na warkar da amosanin kai da kuma hana gashi tsinkewa.

Man Zaitun

Man Zaitun na da matukar inganci musamman ga gashi mai gautsi . Fatar kai na saurin bushewa saboda hunturu. In ana da irin wannan matsalar, sai a dora man zaitun a tukunya idan ya yi dumi, sai a shafa a fatar kai, a ci gaba da shafa man a fatar kai har sai man ya shiga fatar sosai. Sannan a bar shi kamar tsawon minti15. Bayan haka sai a wanke.