✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da lebe lokacin hunturu

Lebe yana daya daga cikin gabobin fuskar mutum wanda kuma yake bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen furta magana. A duk lokacin da mutum yake magana…

Lebe yana daya daga cikin gabobin fuskar mutum wanda kuma yake bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen furta magana. A duk lokacin da mutum yake magana za a ga cewa masu saurarensa suna mayar da hankalinsu kan bakinsa wanda a nan lebe yake, tunda haka abin yake to kula da lebe ya zama dole. Sai dai ana bukatar kulawa ta musamman a lokacin sanyi.

Yanayin leben mutum kamar yanayin fatarsa yake don haka akwai leben da ke saurin bushewa akwai kuma wanda kan jima da lema a jikinsa.

Bushewar lebe babbar matsala ce da ke janyo lebe ya rika saba ta hanyar fitar da busasshiyar fata ko ma leben ya tsattsage wanda zai zama illa ga lafiyar mutum  baya ga janyo wa mutum kyama daga duk wanda suka yi ido hudu da shi.

Domin samun lebe mai cike da lafiya da kyau ga wasu hanyoyi da ya kamata a bi:

•    Kada a rika tattaba lebe ko kuma a rika lasar lebe.

•    A rika cin abinci mai gina jiki.

•    A rika shan ruwa sosai.

•    Idan za a kwanta barci a goge jambaki sai dai a shafa basilin wanda zai bar leben a jike.

•    A rika yawan shafa mai a leben (lip balm) wanda aka tanada don lebe.