✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance rikicin makiyaya da manoma -Sale Bayeri

Aminiya: Yaya kuke kallon kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa don gano abubuwan da suke haddasa rikic- rikicen Fulani makiyaya da manoma a karkashin jagorancin…

Aminiya: Yaya kuke kallon kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa don gano abubuwan da suke haddasa rikic- rikicen Fulani makiyaya da manoma a karkashin jagorancin Mataimakin shugaban kasa?

Bayeri:  Gaskiya abubuwan da suke faruwa kan rikice-rikicen  Fulani makiyaya da manoma a kasar nan suna daure mana kai kwarai da gaske. Saboda haka mu kusan a yanzu babu abin da za a gaya mana mu yarda, domin wadannan abubuwa sun ki ci sun ki cinyewa,  an mayar da mu kamar  yara. Ko kuma kamar kwallo, wannan ya buga nan wannan ya buga can. Ya kamata duk abin da gwamnati za ta yi ta dubi abin da zai yiwu, domin babu amfani aje  a fitar da wani abu wanda makiyaya ba za su yarda  ba, su ma manoma su ki yarda. Ka ga an koma gidan jiya ke nan.

Aminiya:  A baya akwai wadansu abubuwa ne da aka yi wadanda kake ganin cewa  ba a samu nasara ba?

Bayeri:  Shi dai Bafulatani tun ba yau ba ake ta kokarin a killace shi a hurumin gwamnati.  Muna  ta kokarin jan hankalin Fulani makiyaya shekara da shekaru, har sun fara cewa za su amince da wannan abu. Ana kan haka, sai ya kasance ita gwamnati  ba ta fito ta nuna cewa da gaske take yi kan wannan abu ba. Shi kuma Bafulatani yana nan yana tashinsa. Idan nan ya bushe ya tashi ya koma can, inda yake da ruwa da ciyawa yake, haka ya cigaba da rayuwarsa.

Daga baya kuma rana daya sai aka tashi aka ce babu maganar burtaloli, babu kiwo irin na gargajiya saboda rikice rikicen da ake yi tsakanin Fulani makiyaya da manoma, ba a yarda da irin wannan kiwo na gargajiya ba. Aka ce a koma maganar a samar wa da Fulani wuraren kiwo na gwamnati. Muna kokarin wayar da kan Fulani makiyaya kan wannan shiri sai aka zo aka ce Fulani ba su da kasa, don haka wadanda suke ikirarin cewa suna da kasa suka ce ba su yarda a debi kasarsu a bai wa Fulani su rika kiwo ba. Sai kuma  suka zo suka  fara kafa dokar hana kiwo. Jihar Benuwai ta yi, yanzu  jihar Taraba tana shirin yi. Suka ce ba su yarda a samar wa Fulani wuraren kiwo ba, kuma ba su yarda a cigaba da yin  kiwo irin na gargajiya a jihohinsu ba.

Kuma yanzu an zo ana cewa za a nemi wadansu wurare na kiwo mallakar shanu. To yanzu  sun fara fitowa suna cewa turawa sun mallake su, yanzu kuma an sake dauko Fulani su zo su mallake su. Saboda haka ka ga abin ya zama wani mummunan abu a wurinsu. Don haka abin da muke fadi shi ne, ita gwamnatin nan da aka je aka kafa wani kwamiti na gwamnoni karkashin Mataimakin shugaban kasam Meye suke dubawa? domin mu shugabannin Fulani ba mu san abin da suke dubawa ba. Meye ya sa duk abin da za a yi a kanmu ba za a yi shawara da mu ba? Duk abubuwan da aka yi a baya ba a yi shawara da mu ba. Abubuwan da aka yi a baya manoma sun ce ba su yarda ba. Yanzu wannan kwamitin da aka kafa ba mu san abin da yake yi ba.

A duk kasashen Afrika babu inda aka hana kiwo, kuma shi fa Bafulatani ba daga sama ya fado ba, tun da aka fara duniya da Bafulatani aka fara. An fara kiwo kafin a fara noma. Sai da aka fara kiwo shekaru 750 kafin a fara noma. Idan haka ne yaya za a ce manomi ya riga makiyayi zuwa wuri?. Sai dai a ce  makiyayi ba mazauni wuri daya ba ne.

Aminiya: To, meye mafita kan wannan al’amari?

Bayeri:  Abin da muka sha fada a kullum  shi ne  akwai Fulani bararo wadanda ba su zama, a kulllum su a tafiya suke, ko da ruwa ko babu ruwa, su abin da suka saba ke nan. Don haka a barsu su yi ta tafiyarsu, wata rana za su gane cewa wadannan tafiye-tafiye da suke yi babu riba a ciki. Su kuma kamar manyan makiyaya wadanda suke kiwo don kasuwanci, kamar su tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako su Abdullahi Adamu su Tafidan Mafindi su Muhammad Buhari su Obasanjo su Abubakar Abdulsalam, suna da manyan gonaki. Filayen da suka mallaka sun ishe su ko da shanu nawa suke da su. Kuma suna kiwo da noma irin na zamani a wadannan wurare da suka mallaka.

Saboda haka mafita ita ce a bar kiwo na gargajiya ya cigaba, nan gaba Fulani makiyaya na gargajiya za su bari, domin za su ga wadanda suka canza suka zauna wuri daya suna samun riba. Ka ga a karshe za a samu kowane makiyayi ya zauna wuri daya ba tare da wani tashin hankali ba.