✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance sankon kai

Mutane da dama ba su sha’awar sankon kai kuma yakan shafi mace ko namiji. Wannan abu ne da ke matukar bata kyan mutum. Sanko na…

Mutane da dama ba su sha’awar sankon kai kuma yakan shafi mace ko namiji. Wannan abu ne da ke matukar bata kyan mutum. Sanko na da sababi daga jinsin mutum. Idan har akwai sanko a dangin mutum zai iya faruwa da shi ko a haife shi da shi.

Akwai wasu ababuwa da suke janyo sanko kamar yawan gajiya ko yawan amfani da launi a gashi domin rage furfura da sauransu. A yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin magance wadannan matsaloli.

• A samu man ‘castor’ da man kwakwa sai a hada su wuri daya sannan a rika shafawa a fatar kai, a rufe kan da leda na tsawon minti biyar. Yana da kyau a yawaita yin haka don samar da gashi a sanko.

• A yawaita amfani da ruwan ganyen dogon yaro domin yana tsiro da gashi da wuri kuma yana hana furfura. A tafasa ganyen dogon yaron idan ya huce sai ana wanke kai da ruwansa.

• Ganyen shayin na’ana’a da ruwan ‘aloe bera’ na dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma C, suna kuma taimakawa wajen fitar da gashin da ya zube da wuri. A rika hada ganyen shayin na’ana’a da ruwan aloe bera kadan, sai a rika sha na tsawon makobiyu za a ga canji.

• Cin albasa na taimakawa wajen feso da gashi. Yana da kyau a yawaita cin danyar albasa kamar guda biyu a rana. Za a iya yin kwadonta da rama ko da latas domin saukin ci. Sannan a yawaita jajjaga ta ana shafawa a inda sankon yake za ta taimaka.

• Kwaiduwar kwai da ruwan lemun tsami da kuma man zaitun na taimakawa wajen fitar gashi da wuri. A same su sannan a hada su waje daya a shafa a fatar kai. Yana da kyau a rika yin wannan kamar sau biyu a mako.

• A samu ‘baking soda’ da kuma man wanke kai sannan a rika shafawa a sankon, yin hakan na magance kowace matsalar fata da na amosanin kai sannan yana taimakawa wajen haifar da gashin kai.

• Lalle da man kwakwa a hada su a wuri daya sannan a shafa a kan sankon na tsawon minti talatin na taimakawa wajen magance matsalar sanko da rashin gashi a kai.