Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Yadda za a rabu da gishirin fuska - Aminiya
Aminiya

Yadda za a rabu da gishirin fuska

Shin mene ne gishirin fuska? Gishirin fuska dai ana kiransa da suna white heads a Turance. Abubuwan da ke kawo shi su ne, yawan gumi a fuska ko maikon fuska. Idan muka yi gumi, fuskarmu takan fitar da maiko. Idan ba mu damu mun wanke fuskarmu a lokacin da ta yi gumi ba to hakan yakan taru ne sai ya zama gishirin fuska. Yakan fari a kan fuska. Idan muka yi kokarin cire gishirin fuskar da hannu, hakan kan janyo kurajen fuska. Saboda haka na kawo mana hanyoyi da dama da za mu bi don rabuwa da gishirin fuska.

Idan muna son rabuwa da irin wadannan kurajen fuska da gishirin fuska, amfani da hadin gargajiya irin namu na saurin warkar da cututtukan fata. Za mu iya amfani da daya daga cikin wadanda na lissafo don magance gishirin fuska.