Categories: Kwalliya

Yadda za ki gyara furfurarki

Fitowar furfura ko farin gashi akan mace yana zama wani abu na jin kunya ko rashin so ga wasu mata. Mata da yawa suna fargabar ace an wayi gari furfrura ta fito musu. Yayin da aka ce furfura ta fito wa wasu matan, sai ka ga sun daina gyaran gashinsu, wai a cewarsu  tunda

gashin ya yi fari, to babu amfanin yi masa gyara na musamman.

ADVERTISEMENT

Yin maganin furfura tamkar magance damuwar sauran sassa  na jiki ne ko kuma mu ce ya danganta da yadda ake kula da gashin ne. Wani abu da mata ba su sani ba shine ita furfura ba abu ne dake fito miki da tsufa ba ya danganta da yadda kike kula da gashinki.

ADVERTISEMENT

Akwai hanyoyin da za a bi wajen gyara furfura:-

A Wanke gashi da man wankin gashi mai kyau, wanda kuma yake da maiqo.

Ki riqa shafa man wankin gashi a jikin fata, sai ki bar shi tsawon mintuna sannan sai ki wanke. Daga nan sai ki xauko kwandishina ki sa a gashin. Ki bar shi tsawon minti xaya zuwa biyu sannan sai ki sa  ruwa ki xauraye.

. A kare gashi daga rana. Waannan ba wai lokacin rani kaxai ba har ma da lokacin sanyi. Ida ana barin gashin a buxe zai bushe ya zama babu kyawun gani. Don haka a duk lokacin da za ki fita ki rufe kanki.

. Za ki zavi man rinin gashi mai kyau wanda ya dace da gashin . Idan kika sa rinin zai taqaita yawan wanke gashinki, domin kada gashin ya koxe.

Idan ma za a wanke gashin ya kamata a wanke shi da ruwan zafi ko ruwan xumi.

. A riqa shafawa gashin mai, mai kyau don yayi laushi da sheqi misali

man kwakwa da sauransu.

. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago