Search
Subscribe
Yadda za ki kula da ainihin kyanki

Fruit don gyaran jiki

Yadda za ki kula da ainihin kyanki

Kowane mutum yana da ainihin kyawun da Allah Ya halicce shi da shi wanda kuma ya bambanta da na wani. Yana da kyau mutum ya ci gaba da kula da kyansa don ganin wannan kyan ya  zauna sosai tare da shi.

Ga wasu hanyoyi da ya kamata mutum ya bi wajen ganin an samu nasarar haka:

Yin amfani da man da zai yi maganin rana. Wannan shi ne zai taimaka wajen magance duk wata konewar da fatarki ta samu a lokacin zafin rana wanda kuma zai iya sa fatarki yin duhu.

Akwai bukatar ki yawaita shan kayan itatuwa, saboda ki samu fata mai sheki. Kowa yana sane da irin alfanun da ke dauke a cikin kayan itatuwa ga lafiyar mata, don haka ki tabbatar kin sanya wani dan itace a cikin jerin abincin da kike ci a rana. Idan zai yiwu ma ya kasance kina cin ’ya’yan itatuwa a duk lokacin da kike cin abinci.

Ki rika samun isasshen barci. Ki yi kokarin samun barci na tsawon kimanin awa takwas a kullum. Wanan shi zai magance miki kumburin fuska ko kuma idanunki su yi duhu.

Ki yawaita shan ruwa sosai, koda kuwa ba ki jin kishirwa. Ya zama duk bayan minti 30 kina shan ruwa kofi daya. Hakan zai taimaka wa fatarki ta yi sulbi da santsi.

Ki rage yawan caba wa fuskarki kayan kwalliya wato kayan da aka fi sani da “make ober.”

Yawancin lokuta wadannan kayayyakin da ake kwabawa a fuska ko fata ba su haifar da komai sai tsofar da fata.

Ki rika amfani da kayan da suke masu sauki ne akan fata wadanda ba su cutar da fata.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin