Da Dumi Dumi

Yadda za ki kula da farcenki

Kin taba tunanin yadda aka yi wadansu mata ke da kyawawan farata?

Shin haka farcensu yake tun asali? Babu shakka za a iya samun mutanen da Allah Ya halitta da kyawawan farata, amma yawanci idan kika bincika za ki tarar cewa akwai gyara. Abin nan da ake cewa idan kana da kyau ka kara da wanka. Sirrin samuwar kyawawan farata a wajen mace ya dogara ne da irin matakan da ta dauka wajen kula da su.

Lafiyayyu kuma kyawawan farata su ne wadanda suke sumul-sumul babu wata gargada ko karkacewa a jikinsu. Za ki samu cewa, gaba dayansu sun zama launi guda ba tare da wani rauni ko tabo a kai ba.

Farce yana da amfani kwarai da gaske ta fuskar ginuwar jiki. Sai dai hakan ba zai samu ba sai idan muna ba su kulawa ta musamman.

Ga wadansu hanyoyi da muke ganin matukar za mu kula da bin su daki-daki,  to za mu samu biyan bukata na mallakar kyawawa kuma lafiyayyun farata:

ADVERTISEMENT

•    Ki kula da farcenki ta hanyar zuwa salun a kai-a kai.

•    Ki guji tara farce ya yi tsayi sosai, wato akwai bukatar su zama a yanke a koyaushe.

•    Ki guji cire farce da hakori. Ko da ya zama cewa wani abu ya taba farcenki ya yi irin dagowar nan, kada ki sa hakori ki cizge shi, domin hakan zai sa ya fita ba bisa ka’ida ba ta yadda har zai sa tsarin farcen ya zama wani iri daban. Wato sai ki ga wani bangaren na farcen ya fi wani tsawo. Maimakon haka ki samu reza ko kuma abin yankan farce da ake kira da nail cutter ki  yanke farcen da shi.

•    Kada ki bari farcenki ya zama a jike koyaushe, domin hakan zai sa ya rika kakkaryewa tun kafin ma ki kai ga yankewa. Idan ya zama za ki yi aiki da ruwa, yana da kyau ki samu irin safar hannun nan ki sa, don ta kare miki faratanki daga lalacewa.

•    Kada ki yi amfani da alkamashi wajen yanke farcenki, ko da farcen ya kasance mai rauni ne, balle kuma ga wanda ba ya da wata matsala.

•    Bayan kin kammala da yanke faratanki za ki iya samun man farce ki shafe su da shi, wanda hakan shi zai sanya faratanki su rika walkiya da sheki, ba lallai sai kin sanya jan farce ba.

Idan har ke mai sha’awar tara farce ce to ki tabbatar cewa kina kula da su ta hanyar fitar da duk wata dauda da ke shiga ciki ta samu mazauni.

Idan kika kula barin dauda ta zauna cikin farce ba ya da kyawun gani a ido ma, ballantana ga lafiyar jiki.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya