Yanzu lokaci ne na damina da kuma sanyi don haka, dole ne mu kula da tafukan kafafunmu. Mata da dama na mantawa wajen kula da kafa a duk lokacin da suke kwalliya. Lallai idan aka yi hakan kamar an yi tuya an manta da albasa ce. Abin kunya ne a ce mace idan ta taka mutum sai ya ji kamar kaya tsabagen kaushi da faso da ke tafin kafarta. Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kula da tafukan kafarmu kamar haka:
- A samu man glycerin da gishirin Epsom (ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man tee tree da kuma man peppermint a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon minti 15 zuwa 20 sannan a dauko dutsen goge kafa a diddirza, za a ga canji.
- Za a iya amfani da baking soda (ana samunsa a inda ake sayar da kayan hada kek) da man tea tree da man lafinta sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su sai a tsoma kafa na minti 20 sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kaushi da faso a tafin kafa.
- Man lafinta da sea salt da ruwan aloe bera da man Rosemary a hada su a ruwa sannan a tsoma kafa na tsawon minti 20 sannan a dirza kafa har sai kafa ta fita tsaf.
- Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da tawul. Sannan a shafa man glycerin da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa. Sannan sai a yanka farce a gyara su.
- Wadda ke fama da matsalar kaushi lallai ne ta dage wajen yin amfani da safar kafa idan da dama a shafa man basilin a tafin kafar kafin a kwanta a kullum. Sannan a sanya fatar kafar yin laushi da kuma rage shi daga tsagewa.
- Dutsen goge kafa na taka rawar gani wajen tabbatar da samun tafin kafa mai sulbi da kuma cire kaushin kafa. Ya kasance kafa ta jiku kafin a yi amfani da dutsen goge kafa domin samun sakamako mai matukar amfani