Categories: Kwalliya

Yadda za mu kula da tafin kafarmu

Yanzu lokaci ne na damina da kuma sanyi don haka, dole ne mu kula da tafukan kafafunmu. Mata da dama na mantawa wajen kula da kafa a duk lokacin da suke kwalliya. Lallai idan aka yi hakan kamar an yi tuya an manta da albasa ce. Abin kunya ne a ce mace idan ta taka mutum sai ya ji kamar kaya tsabagen kaushi da faso da ke tafin kafarta. Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kula da tafukan kafarmu kamar haka:

  • A samu man glycerin da gishirin Epsom (ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man tee tree da kuma man peppermint a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon minti 15 zuwa 20 sannan a dauko dutsen goge kafa a diddirza, za a ga canji.
  • Za a iya amfani da baking soda (ana samunsa a inda ake sayar da kayan hada kek) da man tea tree da man lafinta sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su sai a tsoma kafa na minti 20 sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kaushi da faso a tafin kafa.
  • Man lafinta da sea salt da ruwan aloe bera da man Rosemary a hada su a ruwa sannan a tsoma kafa na tsawon minti 20 sannan a dirza kafa har sai kafa ta fita tsaf.
  • Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da tawul. Sannan a shafa man glycerin da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa. Sannan sai a yanka farce a gyara su.
  • Wadda ke fama da matsalar kaushi lallai ne ta dage wajen yin amfani da safar kafa idan da dama a shafa man basilin a tafin kafar kafin a kwanta a kullum. Sannan a sanya fatar kafar yin laushi da kuma rage shi daga tsagewa.
  • Dutsen goge kafa na taka rawar gani wajen tabbatar da samun tafin kafa mai sulbi da kuma cire kaushin kafa. Ya kasance kafa ta jiku kafin a yi amfani da dutsen goge kafa domin samun sakamako mai matukar amfani
ADVERTISEMENT
. .

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

11 hours ago