✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Zainab ta fada tarkon masu fataucin miyagun kwayoyi

A yayin da Zainab Habib Aliyu ta bar filin jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar  24  ga Disamban bara domin zuwa aikin Umara, ba…

A yayin da Zainab Habib Aliyu ta bar filin jirgin saman Malam Aminu Kano a ranar  24  ga Disamban bara domin zuwa aikin Umara, ba ta taba tsamanin za a kama ta bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a  Saudiyya ba.

Zainab ta tafi Umarar ce tare da mahaifiyarta Hajiya Maryam Habib Aliyu da yayarta Hajara Habib Aliyu a jirgin sama na kasar Habasha, kuma sun bar filin jirgin saman Malam Aminu Kano ba tare da wata matsala ba.

Bisa ga al’adar kamfanin jiragen sama na Habasha, jirgin ya yada zango a babban birnin kasar Habasha wato Addis-Ababa, inda fasinjojin suka kwana sai ranar 25 ga Disamba suka ci gaba da tafiya zuwa kasa Mai tsarki, inda suka isa da asubahin ranar 26 ga Disamba.

Isarsu filin jirgin sama na Sarki Abdul’azeez da ke Jiddah ke da wuya, sai aka saka su cikin manyan safa-safa domin kai su Madina su gudanar da ziyara, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Sun isa Madina da misali karfe 11:30 na safe, don haka kai-tsaye suka wuce masaukin da aka tanada musu.

Sai dai Zainab da mahaifiyarta da ’yar uwarta ba su sauka a masaukin nasu ba, saboda sun riga sun yi tanadin wani masauki na daban da wanda kamfanin jigilar matafiya ya yi musu. Don haka koda suka je masaukin da aka tanada musu sai suka bayyana musu cewa ba za su sauka a nan ba, inda a sakamakon haka aka amince su je masaukin da suka tanada wa kansu.

A cewar mahaifiyar Zainab, wato Hajiya Maryam Habib, isarsu masaukin ke da wuya sai suka yanke shawarar su tafi Masallacin Annabi (SAW) domin su yi Sallar Azahar da ta La’asar, sannan su dawo gida. Haka kuwa aka yi, sai dai a lokacin da suke dakon lokacin Sallar, sai Zainab da Hajara suka sake shawara. Don haka suka samu mahaifiyarsu suka roke ta su koma gida domin akwai gajiya tare su.

Mahaifiyarsu ta amince, don haka suka dawo gida domin su ci abinci, sannan su kwanta. Hajiya Maryam ta bayyana wa Aminiya cewa bayan da suka dawo gida suka ci abinci, sun zauna a falo suna kallon talabijin amma bayan kankanen lokaci sai ta fara jin barci don haka ta tashi ta shiga daki, ta bar su Zainab suna kallo.

“Jim kadan bayan na kwanta, sai Zainab ta shigo ta kwanta kuma bayan dan lokaci ’yar uwarta ma ta biyo bayanta. Zuwa wani lokaci sai kawai na ji ana taba ni don in tashi. Bude idanuna ke da wuya sai kawai na ga wadansu Labarawa da bakaken fata tsaye a kanmu. Na yi salati na sanar da Ubangiji, na tashi na ce musu lafiya? Sai daya daga cikinsu ya ce min kun manta jakarku ce a Jiddah? Na ce masa a’a ba mu manta ba. Sai ya ce ai kuwa akwai wata jaka mai sunan Zainab Habib Aliyu da aka manta a Jiddah. Na ce masa ba tamu ba ce,” inji ta.

“Daga nan sai ya tambaye ni wace ce Zainab? Na ce masa ga ta nan, na nuna ta. Sai ya ce ina jakarta take? Na ce masa ga ta nan. Sai ya ce to, za su binciki jakar. Na ce masa ba damuwa. Bayan da suka gama binkicensu ba su samu komai ba, sai kuma suka ce za su bincike dakin namu, na ce musu bismillah.Bayan da suka gama binkicensu ba tare da sun samu komai ba, sai suka ce za su tafi da Zainab da jakarta domin gudanar da bincike. Sai na ce to, ai sai dai mu tafi tare. Sai daya daga cikin bakaken fatar ya ce mini ba sai mun tafi tare ba, za su je ne su yi mata tambayoyi su dawo da ita, domin jakar da aka samu kwayoyi a ciki sunanta aka rubuta. Sai na hakura amma ba don na so ba,” inji ta.

Maryam Habib ta ce tunda aka tafi da ’yarta, ba su sake jin wani abu game da ita ba, ba wanda ya kira su kuma duk kiran lambar Zainab da suka rika yi ba wanda ya amsa. Haka duk sakon da suka tura mata, ba wanda aka aiko da amsa duk da cewa alamu sun nuna an karanta su.

Ganin haka ya sa ta kira lambar daya daga cikin bakaken fatar da suka zo da su otel din da suka sauka domin jin karin bayani game da ’yarta. Daga nasa bangaren, wannan bawan Allah sai ya yi wa mahaifiyar Zainab alkawarin bincika mata halin da take ciki a hannun wadancan Larabawa da suka bayyana mata cewa su ma’aikatan hukumar yaki da fatuacin miyagun kwayoyi ne na kasar Saudiyya.

Bayan wani dan lokaci, ya kira ta ya shaida mata cewa Zainab na cikin koshin lafiya kuma har yanzu tana hannun jami’an hukumar, domin bayan da suka tafi da ita da dare ba a samu sukunin yi mata tambayoyi ba saboda jami’an da za su gudanar da tambayoyin sun tashi daga aiki don haka sai da safe za a yi mata tambayoyi.

Ta ce bayan da aka sake shafe wasu awanni sai ta sake kiran shi bakar fatar don sanin halin da ’yarta ke ciki. Sai ya shaida mata cewa an tafi da Zainab zuwa Jiddah don fadada bincike amma yana zaton a ranar za a dawo da ita. Haka ya umarce ta da ta kira lambar Zainab domin su yi magana da ita.

Hajiya Maryam ta ce haka kuwa aka yi, inda Zainab ta shaida mata cewa suna hanyarsu ta zuwa Jiddah kuma da sun je za ta kira ta sanar da ita duk abin da ya gudana.

“Sai dai hakan bai samu ba domin tun daga waccan rana ba mu sake jin wani abu game da Zainab ba sai a ranar 27 ga Disamba, lokacin da wata mata ta kira ni ta ce Zainab ce ke son magana da ni amma sai na saya mata katin waya na Riyal 30 kafin na yi magana da ita. Bayan da na sayo katin sai ta ba ni Zainab a waya muka yi magana, inda ta shaida min cewa an kai ta gidan kaso ne. A tsawon lokacin da muka dauka muna ta fadi-tashi don ganin mun kubutar da Zainab, na sanar da mahaifinta wanda shi kuma ya sanar da hukumomin da abin ya shafa kamar Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayioyi ta Najeriya (NDLEA) da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa,” inji ta.

Ta ce “A takaice wannan shi ne yadda aka kama ’yata Zainab bisa  zargin fataucin miyagun kwayoyi a Saudiyya a bara kuma sai da ta shafe wata hudu kafin Allah cikin ikonSa Ya sa ta kubuta daga halin da ta shiga.”

Ta kara da cewa “Mun gode wa Allah kan kubutar da ita daga wannan mummunan hali da ta shiga, kuma mun gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da duk wanda ya taimaka Zainab ta samu ’yanci. Na gode wa Allah da Ya ba ni tsawon rai na ga wannan rana mai muhimmaci a gare ni. Alhamdu lillahi.”

 

Yadda Zainab ta fada tarkon masu fataucin miyagun kwayoyi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano

Binciken da Aminiya ta gudanar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano ya nuna cewa halin da Zainab ta samu kanta a ciki na zargin fataucin miyagun kwayoyi, daya ne daga cikin cuwa-cuwar da ake yi domin fataucin miyagun kwayoyi a filin jirgin saman, tare da hadin bakin ma’aikata da jami’an tsaro, musamman na FAAN da NDLEA da Kwastam.

Wata majiya da ta bukaci a sakayata, ta bayyana wa wakilinmu cewa a yanzu haka masu fataucin miyagun kwayoyin na cin karensu ba babbaka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano saboda daurin gindin da suke samu daga jami’an tsaron. Ta ce a zahirin gaskiya Zainab Habib Aliyu da sauran ma’aikatan kamfanin jigilar kayan matafiya da ake zargi da hannu a cikin saka Zainab a halin da ta shiga, ba su da laifi.

“Su ma saka su aka yi amma masu laifin na gefe kuma in har gwamnati za ta aiwatar da cikakken bincike, to za ka tarar wadannan mutane sun kubuta domin ba su ne masu laifin ba. Su ma ba sa sanin abin da ke cikin jakankunan da ake ba su domin fito. Abin da yake faruwa shi ne, akwai kamfanonin harkar jigilar kayan matafiya, wato ejan-ejan, wasu suna da rajista wasu kuma ba su da ita. To wadanda ba su da rajista suna fakewa ne da masu rajista domin gudanar da aikace-aikacensu don neman abinci kuma yadda suke yi shi ne, duk lokacin da suke da kaya, sai su nemi masu rajista su taimaka musu domin shigar musu da su ba tare da sun biya kudin awo ba. Su kuma masu rajista dama ba a binciken kayansu sakamkon kudin da suke ba jami’an tsaro domin dauke ido daga kayansu. Don haka za ka tarar duk lokacin da suke wucewa da kayansu to ba a binciken duk abin da suka zo da shi,” inji majiyar.

Ta kara da cewa “A kowace jaka suna bai wa jami’an Kwastan Naira 500, su kuma jami’an NDLEA Naira 1,000 wadanda su kuma ba za su binciki kayan ba. Duk lokacin da ake son shigar da kayan marasa rajista to za duba ne a ga wane matafiyi ne kayansa ba su kai yawan kilon da aka kayyade masa ba, sai kawai su rubuta sunansa da lambar fasfonsa a kan kayan da ejan mara rajista ya zo da shi ba tare da sanin matafiyin ba. Shi kuma ejan din zai dauki kayansa a can kasa Mai tsarki ba tare da sanin matafiyin da aka rubuta sunansa ba.

“A irin wannan tsari ne aka rubuta sunan Zainab a kan kayan wani dan fito wai shi Sanda, wanda kuma daga bisani an kama shi. Sai dai tuni aka saki Sanda ya ci gaba da yawonsa. Hasali ma wata majiya ta tabbatar da cewa ko makon jiya sai da Sanda ya tura kaya Saudiyya,” inji majiyar tamu.