✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zaizayar kasa ke karya noma da tattalin arziki – Dakta Gital

Aminiya: Ya ya zaka bayyana matsalar kwararowar hamada? Dakta Iliyasu  Aliyu Gital: Gaskiya matsalar kwararowar hamada na da dogon tarihi, saboda masana kimiyya ba su…

Aminiya: Ya ya zaka bayyana matsalar kwararowar hamada?

Dakta Iliyasu  Aliyu Gital: Gaskiya matsalar kwararowar hamada na da dogon tarihi, saboda masana kimiyya ba su bar shi ba saboda illar da yake da shi, saboda haka sanannen abu ne da yake faruwa a duniya , ba kasa daya ya shafa ba, yana daya daga cikin matsalolin dake faruwa a duk fadin duniya, kusan kowace kasa na fama da irin nata matsalar. A kiyasin lokacin muna makaranta kimanin sama da shekaru 20 da suka wuce, an ce daya bisa biyar na duniya na fuskantar matsalar kwararowar hamada, abinda ake nufi anan doron kasar, kasan ruwa shi ke da kaso biyu cikin uku na duniyar baki daya.

A yanzun ma masana na ci gaba da bincike kuma kwararowar hamadar ya karu ya kai yana barazana ga daya bisa uku na doron kasa a fadin duniya, ta na shafansu ne ta hanya daya ko biyu, kodayake akwai dalilai da yawa da suke sa ake samun kwararowar hamadar, wadansu daga ciki yin dan Adam ne, wasu kuwa ikon Allah ne. Abu ne mai faruwa, a cikin na ikon Allah wani yana gyaruwa da kansa wani kuma cikin ikon Allah wanda yin dan Adam ne, idan ba dan Adam yasa nasa gudummawar ba, sai ka samu hamada yana karuwa a yanayin dama zai tsoratar.

Kamar a Najeriya yanzu da ana maganar kwararowar hamada yana cin kasa fadin kilomita daya zuwa daya da rabi, yanzu kuwa ana maganar a kowace shekara yana lalata kasa mai nisan kilomita biyar zuwa 15 a kowace shekara! Ka ga akwai abin damuwa.

Aminiya: Ko wadanne dalilai ne ke kawo karuwar sa? Kuma ta ya ya za a magance su?

Gital: To dalili na farko na da can, wanda har yanzu ba mu rabu da dalilan ba musamman bangaren Najeriya daya daga cikin kasashe masu tasowa wadda sune suka fi fama da matsalar, don a kasashen da suka cigaba matsalar ta ragu sosai, a dalilin kwararowar hamada wannan matsala ita ce wanda ake cewa yawan kiwo, wato (Ober Grazing) abin nufi yanayin ciyawar da dabbobi suke cinye ciyawa da kuma kananan bishiyoyi sun yi yawa, ba abu na damina ko kuma tsiro da zai zauna ya rufe kasa, wannan matsala na yawan yin kiwo fiye da yadda kasar za ta dauka yana daya daga cikin manya manyan dalilai da suke kawo kwararowar hamada, yanzu ka duba misali ko anan Bauchi sai ka samu yawan dabbobin da ada ake zuwa da su Kudu domin su yi kiwo su dawo, yanzu yawancin shekarun kiwonsu anan Arewa suke yi, kuma illar dabbobin nan ba kawai cinye ciyayi ba ne, su kansu yadda suke taka kasar su na bantare kasar ta yadda idan iska ya zo zai hure shi, shi kansa yana jawowa zaizayar kasa, idan ka kwatanta da inda ciyayi ya rufe kasa da kuma wannan din, zaka san illar ba karama ba ce. Wannan yana daya daga cikin wadanda dan adam ke kawo su,  na biyu shine yawan sare bishiyoyi domin yin katako ko dafa abinci, abin bakin ciki ne, yin hakan yafi yawa a kasashe masu tasowa domin a nan ne har yanzu ba a samu abubuwan da za a yi amfanin da bishiya ke yi ba. Na tuna an taba kirana a wajen wani taro na dashen itatuwa da aka yi shekaru 15 da suka wuce, na ce ai ba za a hana mutane dafa abinci ba, matukar za a dafa abinci kuma matukar babu gas ba kanazir ba lantarki, to dole a sare itace ayi girki, idan har za a hana mutane amfani da itace don yin girki, to dole ne akawo hanyoyin da za a yawaita amfani da abubuwan makamashi kamar kwal, da gas da kananzir  ko lantarki da za a yi amfani da shi domin yin girki, in ba haka ba sai dai kullum mutaru mu yi surutu mu watse ba za a daina sare wadannan bishiyoyin ba. Matukar anci gaba da maida makamashi abu mai tsada sai wane da wane, to gaskiya maganar hana sare bishiyoyin nan ba ta taso ba. Na uku kuma shi ne yadda muke nomanmu gaskiya akwai matsala, don ba kwararru masana muhalli dake jawo hankalin manoma, don da a kowace ma’aikatar gona akwai sashen kula da gandun daji da suke hade da maluman gona, amma yanzu an maida su ma’aikatan muhalli na kasa,  da can an san cewa abubuwan da suka shafi gona ya fi shafar dazuzzukan, shi yasa aka bar su a ma’aikatar gona don su rika bada shawara ga manoma, domin in zaka yi nomanka a baka shawara kar ka bar kasar ta yadda zai kara kwararowar hamada, amma yanzu babu su, duk da cewa suna ma’aikatar muhalli amma abinda suke yi daban.

Duk da cewa an san a muhalli sune suke da hakki, amma da muna hade da yafi inganci, muna ba juna shawara, ka ga yadda muke nomanmu sai ka ga mutum kamar ya share kofar gidansa ne in zai yi noma ya share ko’ina bai bar inda in iska yazo zai ragamma kasar ba, ko kuma in ruwan sama mai yawa ya zo sai ka ga ya kwashe kasar ya tafi da ita, kwashe kasar saman nan ya zamana ba abin da zai yi kuma in saiwa na wajen ba zai tsira ba, idan har abu bai girma a gona ko a fili ba, yana daya daga cikin abubuwan da suke taimakawa kwararowar hamada, don wajen zai zama kamar sahara ne. Na hudu akwai maganar manyan garuruwa koda yake ba shi da muhimmanci mai yawa, amma ba za a maida shi baya ba, ace bai kai ba, misali inka dauki garin Abuja yau da jeji ne, amma yau an sare bishiyoyi anyi gine gine, iskar da bai isa ya wuce da gudu a Abuja ba, amma yanzu zai wuce da gudu, haka matsalar birane yake sai ka ga an kada bishiyoyi masu yawa anyi gine-gine, amma kuma ba za a dasa wadansu itatuwa da za su kare muhallin ba, wannan ma illa ce babba dake kawo kwararowar hamada, sai kuma na yanzu wanda shi ya yi kusan fin komai daukan illar kwararowar hamada wanda mu ke ce sauyin yanayi (climate change), Babbar Matsalar da take faruwa a yau ita ce canjin yanayi sai ya zamana kuma yana kara kwararowar Hamada, kuma yana kara canjin yanayi, irin noman da muke yi na kara dumamar yanayi, irin abubuwan da ake yi na yanzu motoci ne, iskar gas ne, iskar menene duk yana kara canjin yanayi su kuma za ka ga duk sun ta’allaka ga noman ne saboda haka in ba ka gyara yanayin noman ba, canjin yanayin nan zai ci gaba, gashi da wadancan abububwa su suka kawo sauyin yanayi, shi kansa canjin yanayin yana kawo illa wajen kwararowar hamada.

Misali yanzu ruwan sama da da ake samu ada can muna kananan yara shekaru 50, 60 da suka wuce, sai ka samu daga ance maka watan 7 watan 8, har zuwa watan 9 fita waje ma kaje ka nemi abinci, yakan zama matsala saboda yanayin yawan ruwan sama, amma yanzu ba a samun ruwan haka saboda fari ya yi yawa, duka wannan saboda dumamar yanayi ne, kuma illolinsa na tattare da abinda dan Adam yake yi da muhallinsa, to in ba an shawo kan dumamar yanayin nan ba, akwai matsala, ka ga saboda damuwa da shi ya sa kasashen duniya keyin taro kowace shekara domin dumamar yanayin a matasayin daya daga cikin dalilan dake kawo kwararowar hamada don a yanzu dai kusan shi yafi kowanne illa wajen kawo kwararowar hamada, irin su tona ma’adinai, a kwanan nan muka je kasar Morocco na ga wani inda ake tona ma’adinin yin taki, kamfani musamman aka dauko don in kun yi tono kun tafi, su kuma aikinsu shi ne su maida gurbin kasa a wajen su yi dashe-dashe don su mai da gurbin wajen kamar yadda yake ada.  

Aminiya: Ko ka gamsu da irin rawar da gwamnatoci ke takawa a Najeriya domin shawo kan wannan matsala?

Gital: To gaskiya gwamnatoci dai na san cewa a kwanan baya akwai matakan da aka dauka da kuma wadanda ake dauka, amma bisa gaskiya ba su isa ba, don yanzu akwai wani babban mataki da aka dauka, wanda aka sa a gaban da ake ce masa babban katafaren katangar dashe-dashe (Great Green Wall) wanda ake yi daga Afirka ta tsakiya har azo a wuce Afirka ta yamma, aje a shiga teku, ayi abinda ake cewa tunda hamadan na zuwa da gudu in yazo inda aka samu aka rage yawan gudun iska, ko aka rage karfin iskar, amma babbar matsalar da ake samu a yanzu ita ce kasashe da yawa wadanda ga shi an zauna an yi wannan da su sai ka samu abinda ake cewa za a ayi din ba ayi ba, yanzu anan Najeriya dai Jihohin Yobe, Borno, Katsina da Zamfara su ne manya manyan jihohin da wannan katafaren katangan dashe-dashe ya fi shafa, amma nan cikin kuma an yi ta kokari a rika yin dashe dashe a wassu manyan filaye, koda yake yawanci sun fi so a dasa abin da zai zamo na abinci ne, ka ga shi ma zai kara wa mutane kaimi, tunda wannann abin inka noma ba zai kara wa mutane abu ba ne, domin kai ma din akwai abin da zaka diba ko ka ci ko ka sayar, to duk da anyi wannan kokari amma akwai wanda ba a sa su a kasa da za su taimaka ba. 

Kaga na daya tukuna bishiya ba zai tsiro ba sai da ruwan sama, kuma ga maganan kamban ruwan sama (drought) wanda in ba an tanadi ruwa ba to ba zai yiwu ba, haka kuma yawan sa wuta a daji shi ma yana kara kwararowar hamada, an je an yi dashe-dashe a daji amma ba a yi katanga na tsare gobara ba, ka ga da sauran aiki, koda kana ban ruwan in baka tsare shi ba idan har an samu wutar daji to akwai matsala, wadannan sune matakan da ake dauka, amma gaskiya wani lokaci za a tattauna ne kawai ba tare da aiwatar da shi ba. bangaren noma, anyi kokari sosai  don su kansu manoman sun ga tsarin bishiyoyin bai cin hana kwararowar hamada.