✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zaman tankiya ta samo asali tsakanin Ganduje da Sanusi

Nadin sabbin sarakuna hudu a ranar 10 ga watan Mayun bara, da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi kara fito fili da irin…

Nadin sabbin sarakuna hudu a ranar 10 ga watan Mayun bara, da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi kara fito fili da irin tsamin dangantaka tsakanin Masarautar Kanon da kuma Gwamnatin jihar.

A ranar Litinin 6 ga watan Mayun bara, Majalisar Dokokin jihar ta kafa dokar da ta kirkiro da sabbin masarautu hudu a jihar da sukar hadar da Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi. Hakan ya nuna yadda aka kirkiro da sabbin sarakuna hudu masu iko iri guda da Sarki Sanusin.

Tsamin dangantakar tsakanin Ganduje da Sanusi ta jima tana faruwa.

Idan dai za a iya tunawa Sarki Sanusi ya dare karagar mulkin Kano bayan ya rike Gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Ya yi shuhura sosai bayan da ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Shugaban Kasa na wancan lokaci Goodluck Jonathan, game da yadda take ririta arzikin da Najeriya ke samu daga man fetur.

A dai mukamin Gwamnan Babban Bankin ma, cire shi aka yi daga kujerar ta hanyar da ta haifar da cece-kuce, wanda ya samu suka sosai daga ‘yan Najeriya, ciki har da jam’iyyar APC wacce Gwamna Gandujen yake cikinta.

An sanar da nada Sanusi Lamido a matsayin sabon sarkin Kano a ranar 8 ga watan Yunin shekarar 2014 sa’annan an sanar da tsige shi daga karagar a ranar 9 ga watan Maris: Ma’ana ya yi sarautar Kano na tsawon shekara biyar da wata tara da kwana daya ke nan.

Tun shekarar 2017 aka fara takaddama tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi.

An zargi Sanusi Lamido da goyon jam’iyyar PDP a zaben gwamna na 2019
Bayan kammala zabukan shekarar 2019, an bude wani sabon shafi na takun-saka tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, lamarin da ya yi kamarin da ba a taba zaton zai yi ba.

Gwamnan Kano da magoya bayansa sun zargi Sarki Sanusi da goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna.

Sun yi zargin cewa ya fito fili ya yaki Ganduje, kuma ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP yakin neman zabe, sai dai sarkin ya musanta wannan zargi.

Wannan zargi ya janyo gagarumar baraka tsakanin shugabannin biyu, lamarin da ya kai ga gwamnatin na yunkurin tube sarkin.

Haka kuma, an rage yawan fadin masarautar Kano zuwa kananan hukumomi 10 daga 44, sannan aka mayar da mafi yawan hakiman masarautar zuwa wadancan sabbin masarautun.

Masu zabar sarkin Kano sun kalubalanci matakin da kotun ta dauka, lamarin da wasu suke ganin kamar Sarki Sanusi ne kai karar gwamnatin Kano.