✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zogale ke rage kashe kudaden sayen magunguna

Kimanin kusan nisan kilomita uku daga garin Chuka a kasar Kenya akwai dubban bishiyoyi da aka shuka saboda sauyin yanayi. Jama’ar yankin sun ce, akalla…

Kimanin kusan nisan kilomita uku daga garin Chuka a kasar Kenya akwai dubban bishiyoyi da aka shuka saboda sauyin yanayi. Jama’ar yankin sun ce, akalla akwai bishiyoyi  dubu 4 wadanda aka shuka da nufin sanyaya yankin, wadannan bishiyoyin duk na zogale ne, an shuka su ne saboda muhimmancinsu.

Akwai wani manomi mai suna Mista Wahome Githui mai shekara 63 wanda ya himmatu wajen shuka irin wadannan bishiyoyin fiye da sauran abubuwan da yake shukawa.

A shekarar 2006 Wahome ya fara nazari a kan muhimmanci zogale. A bincikensa kan zogale ya gano cewa, zogale na da muhimmanci sosai da ya hada da: itacensa da magance cututtuka na al’ajabi da man zogale da kuma amfanin da tushen bishiyar take da shi.

Mista Wahome, ya fahimci cewa bishiyar zogalen na da saurin girma kuma tana iya girma a duk yanayin da aka samu na sauyin yanayi sannan zai iya jure duk yanayin annobar da kasar za ta samu.

Mayuwaci ne a samu wata cuta ko kwari da zai iya yi wa zogale illa.

Irin wannan zogalen na da matukar wahalar samu, har sai da Mista Wahome ya tafi cibiyar binciken bishiyoyi a kasar Kenya, wanda take da hedkwatar a garin Maguga a Lardin Kiambu ta kasar.

A duk irin wannan bishiyar zogale ana sayar da ita a kan kudin Kenya Shilling 40 wanda ya yi daidai da Naira 143.19, an shuka bishiyoyin ne da barin tazarar kafa hudu,” inji Mista Wahome.

Jami’an hukumar tsirrai na kasar Kenya, sun bayyana wa Mista Wahome cewa, barin tazara tsakanin bishiyoyin zai ba da damar wadata bishiyoyin da ruwa lokacin ban ruwa kuma wannan ba zai haifar da wata matsala ba lokacin sanya takin gargajiya.

Mista Wahome ya ce, ya kashe kimanin kudin Kenya Shilling dubu 300 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 107 da dubu 391 a kan sayo irin bishiyoyin zogalen da kudin dakonsu da kuma lura da su tun suna kanana.

Noman zogale na kaiwa tsawon shekara biyu kafin girbewa. “Na kasance wanda ya samu horo a fannin hada magunguna amma daga bisani na zama mai jinya,” inji Mista Wahome.

Mista Wahome, ya yanke shawarar fara noman zogale ne saboda mutanen da suke kasashen da ke tasowa irin su Kenya suna da karancin abinci mai gina jiki ko mai kara kuzari, wadannan bishiyoyin zogalen za su dace da al’ummar yankin. Zogale na da muhimmanci wajen samar da isassshen abin da jiki ke bukata, musamman kananan yara da iyaye masu shayarwa.

Bishiyar zogalen tana da saukin noma har zuwa girmanta, saboda tana tattare  da sinadaran kiwon lafiya ta kowa ne fanni tun daga ganyen da iri da jijiya da fulawar da yake fitarwa. Tana da amfani a jikin mutum da dabba.

Wadansu abokan huldar kasuwancin zogalen suna shanya ganyen zogalen a inuwa don amfaninsa wajen gina jikin dan Adam.

Idan an cire ganyen sai a wanke kafin a yi amfani da shi, sannan idan ana da bukatar shanyawa ne, sai a ajiye tire mai fadi a shanya a inuwa zuwa sa’o’i 24, sai kuma a shirya shi yadda kada ya harhade.

Yana shirya zogalen ne a kan kwantena mai nauyin giram 250 zuwa giram 500, ana sayar da giram 250 a kan kudin Kenya Shilling 650 wanda ya yi daidai da Naira dubu 232 da 681 yayin da giram 500 ake sayar da shi a kan Shilling 1,300 wanda ya yi daidai da Naira dubu 465 da 361.

 

Daga jaridar Daily Nation ta kasar Kenya.