✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaduwar naman jaki a Birnin Tarayya Abuja

Hukumar Babban Birnin Tarayya ta nuna damuwarta a kan yaduwar naman jaki a wasu kasuwanni, wanda ya kasance abin damuwa musamman ga mazauna birnin ganin…

Hukumar Babban Birnin Tarayya ta nuna damuwarta a kan yaduwar naman jaki a wasu kasuwanni, wanda ya kasance abin damuwa musamman ga mazauna birnin ganin babu ta yadda mutum zai iya tantance irin wannan nama.

Hukumar ta ce ana shigo da naman jakin ne daga wasu jihohi da ke mawabtaka da birnin, kuma tuni Daraktan Kula da Muhalli, Alhaji Baba Shehu Lawan  ya umarci sashin ya kula  kuma ya sa ido da kuma kwace duk wani danyen nama da aka shigo da shi cikin birnin domin sayarwa.

A sanarwar da Shugaban SashinLabarai da Wayar da kan Jama’a na Hukumar, Muktar Ibrahim ya fitar ta ce “Wadansu batagarin masu sana’ar sayar da nama, na kawo barazana ga rayuwar al’umma inda suke shigo da irin wannan nama a boye zuwa cikin kasuwanninmu.” Ya ce yawaitar samun wannan matsala ta kawo nama marar tsabta ko naman jaki da ake shigowa da shi, ba abin da za a amince da shi ba ne, domin ba mu da yakinin ingancin lafiyar wannan nama, kuma hukumar sa-ido da tabbatar da ingancin abinci ta birnin tarayya, ba ta da hurumi a wasu jihohi. Don haka sai ya ce an hana shigo da duk wani danyen nama daga jihohi makwabta.

Daraktan ya ce “Ba ma bukatar faduwar tattalin arzikin kowa, amma babu ja da baya a kan wannan hukunci, kuma tuni hukumar mulki ta Birnin Tarayya ta amince da haka. Abin da muke bukata shi ne inganta tsarin samar da nama mai tsabta, domin mun kasance fittacen birnin a duniya kuma cibiyar kasashen Afrika, Birnin Abuja na jawo baki daga ciki da wajen kasar nan, don haka ya zama dole mu tabbatar da samun ingantattacen abinci da ya dace da kowa.”

Sai dai abin takaici shi ne yadda ake kawo gurbatatcen nama cikin kasuwanni, walau na jaki ko na kowace irin dabba ce, ana sayar wa jama’a, sam bai dace ba, kuma muna yaba wa hukumomin gudanarwa na Birnin Tarayya domin daukar mataki a kan wannan mumunan abu. Domin hakanne jam’ian kula da lafiya za su rika zuwa kasuwannin suna duba irin yanayin naman, kuma a lalata shi nan take, kuma a hukunta wanda ya kawo da mai sayarwa, don ya zama darasi ga wadansu. Kazalika wannan aikin sa-idon zai ci gaba, gaskiya ne yanayin da wajen yanka dabbobinmu suke a kasar nan, ko da dabbar mai lafiya ce, amma wajen sassara ta kan sa nama ya hadu da wata cuta, don haka ana daukar matakai na tsabtace wajen yanka da gyaran nama a kowane lokaci.

Daga nan Daraktan ya ce duk wani nama da ake shigowa da shi daga wajen Abuja an haramta hakan, a kokarin da ake yi na magance wannan matsala, domin watakila hakan kan iya zama shi ne makasudin kawo karshen lamarin. Dabbobin da ake yankawa a kwatar da ke cikin birnin  an san ba za su wadatar da al’ummar birnin ba, wanda hakan yakan sa tsadar naman, kuma yana wahalar da jama’a su yi tafiya mai nisa kafin su sayi nama, wannan dakatarwa ba ta dindindin ba ce.

Haka kuma dabi’ar nan ta duba dabba kafin a yanka, tana nan, haka dokar da take kula da ayyukan masu sayar da nama ta nan daram, duk wadannan suna nan amma rashin aiwatar da su ya kawo koma-baya, saboda haka ba za mu jira ba, har sai wata annoba ta tashi, kafin mu kaddamar da dokar da take da amfani ga rayuwar al’umma, domin haka dukkan jihohin kasar nan su san wannan doka, kuma su ba da kyakkyawar kula a kan naman da ake sayarwa a kasuwanni.

Don haka akwai bukatar fadakar da al’umma a kan su rika kula da naman jaki da kuma irin illar da yake da ita, kuma a fadakar a kan yadda za su gane irin naman da matakan da za su dauka.

Ya zama dole a hada hannu a yi aiki tare don dakile wannan lamari.