✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yagana Ali: Mace mai farautar ’yan Boko Haram

Malama Yagana Ali, ta kwashe sama da shekara 5 tana aikin sintiri a garin Munguno, ta ce ta shiga aikin ne bayan ’yan Boko Haram…

Malama Yagana Ali, ta kwashe sama da shekara 5 tana aikin sintiri a garin Munguno, ta ce ta shiga aikin ne bayan ’yan Boko Haram sun kashe  mijinta da ’ya’yanta biyu da mahaifinta:

 

Me ya ba ki sha’awakika shiga wannan aiki na Bijilanti?

“A gaskiya kishi da bakin cikin abin da ya same ni ne ya sanya ni shiga wannan aikin, saboda ’yan Boko Haram ne suka kashe mini miji  da ’ya’yana biyu da kuma babana wanda ya rike ni har na girma. To ni kuma na kasance ba ni da kowa ke nan sai dai kawai fama da bakin ciki. Ana cikin haka kuma sai aka sace mini ’yar jaririyar yarinyata wanda ba ta wuce wata  8 da haihuwa ba a wancan lokaci. Sai abu dai ya taru ya yi mini yawa na shiga cikin damuwa, to wannan ya sa na shiga wannan aiki na sintiri.

Aikin da kike yi, ya tsaya ne a cikin garin Munguno, ko har da wajen Munguno?

Bai tsaya a garin Munguno ba muna shiga har cikin daji muna farautar ’yan Boko Haram da makamanmu na gargajiya kuma muna cin nasara a kansu, haka muna gudanar da aikinmu a sansanonin gudun hijira na garin Munguno da cikin garin Monguno muna aikin agaza wa mutane da sauran ayyukan agajin gaggawa, don ka san  tun daga lokacin da Boko Haram suka farmaki garuruwan yankin Arewacin Borno akasarin jami’an tsaro musanmma ’yan sanda suka bar garuruwa sai ya kasance mu ne muke aikin ’yan sandan na samar da tsaro.

Kin ce kuna shiga daji har ku samu nasara a kan Boko Haram,  kuma da bindigar toka. Akwai wani abu ne da kike sha da ke cire miki tsoro a matsayinki na mace?

Ba na shan komai ba na kuma da wani dafa’i kawai dai na dogara ga Allah ne, kuma sai Ya sa mini karfin hali da juriya ta yadda nake ganin zan iya duk wani abu da namiji zai yi har shiga dajin tare da yin arangama da wadannan mutane. Kada ka manta na fada maka cewa bakin cikin abin da ya faru da ni ne ya kai ni ga rungumar wannan aiki.

To ko akwai  lada da ake biyanku?

Babu wani abin da ake biyanmu kuma babu wani mai biyanmu haka muke aikin sai dai kawai wanda ya ga dama a cikin mutanen gari ya mika mana abin da ya yi niyya saboda Allah.  Sannan muna gadin kasuwanni ko shaguna duk mako-mako sukan biyamu Naira 500 zuwa dubu daya, to da haka ne muke samun na ci-maka, amma baya ga wadannan babu  wanda yake ba mu wani abu ko da gwamnati ce.  A baya gwamnatin jiha ta yi mana alkawarin  za a rika biyanmu amma har yanzu maganannar da nake yi da kai babu ko sisin kwabon da gwamnati ke ba mu, karfin hali ne kawai muke yi don wata rana mukan yini da yunwa ko mu kwana da yunwa. Da yake mun san taimakon al’umma ne wata rana Allah zai taimake mu.

Yaya yanayin aikin sintirinku yake a nan garin Mongono da sansanonin gudun hijira na garin?

To ka ga dai mu ’yan Bijilanti a garin nan ba mu wuce 3000 da doriya ba kuma ni kadai ce mace a cikinsu. Kuma dukanmu muna aikin sakai ne, baya ga shiga daji muna aikin taimakon jama’a a cikin sansanonin gudun hijira masu girma da fadi har sama da 5 masu dauke da dubban daruruwan mutane da suka fito daga kananan hukumomin Abadam da Marte da Kukawa da Guzamala da Kala-Balge da Gamboru Ngala to duk wasu ayyukan da suka shafi kula da walwalar jama’a da sasanta tsakaninsu da kare rayuka da dukiyoyinsu da sauransu mu muke yi. A gaskiya ba karamin aiki ba ne akwai kalubale tattare da wannan aiki, ga shi kuma ba biyanmu ake yi ba. To in ka duba sai ka ga ba karamin aiki ba ne, domin kusan zan iya cewa ayyukan ’yan sanda muke yi mun kuma kwashe tsawon lokaci muna yi kafin su dawo kwanan nan. Sannan in ba ka manta ba na fada maka cewa muna gadin kasuwanni da shaguna da ake biyanmu duk mako da kudi kalilan, ko a cikin garin ma haka muke yi idan kuma lokacin shiga dajinmu ya yi za mu shiga. Haka dai muke fama, amma akwai kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen duniya da suke da ofishi a nan tare da wadansu jami’an tsaro duk muna hada kai da su wajen agaza wa al’ummomin da suke nan Monguno.

To wadanne matsaloli kuke fuskanta?

Eh to a gaskiya muna da matsalar rashin kayan aiki wato rashin makamai da motocin zirga-zirga, sai rashin alawus ko da ba mu samu albashi ba. To wadannan ne matsalolin da muke fuskanta kuma suke kawo tarnaki ga ayyukanmu.

Mene ne kiranki ga gwamnati?

Ina rokon gwamnati ta yi wa Allah ta agaza mana da bindigogi, da motocin da za su taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu kuma ta taimaka wajen ba mu alawus kamar yadda ta yi mana alkawari don zai taimaka wajen gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum, saboda akwai masu iyali.  Gwamnati ta rika ba mu wani dan abin kyautatawa tunda dai wannan aiki muna yi don jama’a ne kuma jama’a su ne gwamnati, kuma gwamnati tana bukatar ganin a samu zaman lafiya.

Ko kina da kira ga ’yan uwanki mata?

To kirana ga mata shi ne su tashi su rungumi ilimi da sana’a domin idan suna da daya daga cikinsu ba za su wulakanta ba, balle a ce su hada duka biyu.