✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Kungiyar ASUP ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 21

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Najeriya (ASUP) ta sanar da wa’adin kwanaki 21 wanda zai fara daga ranar 2 ga watan Oktoba 2018…

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Najeriya (ASUP) ta sanar da wa’adin kwanaki 21 wanda zai fara daga ranar 2 ga watan Oktoba 2018 don gwamatin tarayya ta biya masu bukatunsu ko kuma su rufe duk makarantun kasar.

Shugaban kungiyar ASUP reshen zone A Kabir Yunusa ne ya fitar da sanarwar a madadin shugaban kungiyar na kasa, an kuma dauki matakin ne bayan wani zama da kwamitin zartarwa suka yi.